"Ba a Taba Maganar Sauya Sheka tsakanin Kwankwaso da APC ba": Kwankwasiyya
- Kungiyar Kwankwasiyya a Najeriya ta bayyana cewa babu wani lokaci da jagoranta, Rabi'u Musa Kwankwaso zai yi wa jam'iyya mai mulki aiki, ko da an nemi hakan
- Yana wannan batu ne bayan gwamnatin Kano ta bakin Sanusi Bature Dawakin Tofa ta bayyyana cewa Kwankwaso ya san da batun sauya-shekar Abba Kabir
- Kakakin Kwankwasiyya, Habibu Mohammed, ya shaida wa Legit cewa yana mamakin dalilin da ya sa gwamna Abba Kabir Yusuf bai fito da zancen a baya ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Kakakin ƙungiyar Kwankwasiyya, Habibu Mohammed, ya bayyana cewa jagoranta ba zai yi aiki tare da jam’iyyar APC ba duk da Bola Tinubu ya nemi ba Sanata Rabiu Musa Kwankwaso mukami a baya.
Mai magana da yawun kungiyar ya bayyana haka ne a matsayin martani ga gwamnatin Kano da ta ce Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya san komai game da sauya shekar gwamna Abba Kabir Yusuf.

Source: Twitter
Habibu Mohammed ya ce haka ne yayin wata hira da gidan talabijin na Arise News, inda ya ƙaryata zargin da ake yi cewa jagoran Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso, na aiki a ɓoye da Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Ya ce babu wani lokaci da aka yi maganar sauya sheka tsakanin Kwankwaso da APC, sai dai Shugaban kasa ya taba yi masa tayin mukami.
Kwankwasiyya ta soki hadimin gwamnan Kano
A zantawarsa da Daily Post, Habib Mohammed ya bayyana cewa zarge-zargen da kakakin gwamnatin Kano, Sanusi Bature, ya yi ba su da tushe kuma siyasa ce kawai. A kalamansa:
“Mutumin da ya yi aiki ƙarƙashinka na tsawon shekara 43 ba tare da ka taɓa ganin wata matsala a tare da shi ba, ko ka taɓa ganin ya rikice wajen yanke hukunci ba, to ‘yan Najeriya za su gane wanda yake rikicewa a zahiri.”
Ya ƙara da cewa Kwankwaso mutum ne da aka sani da yanke shawara da kansa, yana mai tunatar da yadda ya fice daga PDP zuwa NNPP kafin zaɓen 2023.
Obi mutumin kirki ne - Kwankwasiyya
Kungiyar Kwankwasiyya ta bayyana cewa akwai mamaki da har gwamnan Kano zai yi shiru a lokacin da Kwankwaso ke yi wa Tinubu aiki idan har da gaske ne zarginsa.

Source: Twitter
Game da alakarsa da Peter Obi, daya daga cikin manyan Kwankwasiyya a Kano, Injiniya Ibrahim Karaye ya shaida wa Legit cewa wannan zumunci ne aka kulla domin ci gaban Najeriya.
A kalamansa:
"Shi wannan zumunci da aka kulla, zumunci ne mai kyau. Domin tun sanda aka faro wannan jamhuriyyar tun daga 1999, wadannan mutane na wancan yankin ba su taba yin shugabancin Najeriya ba. Ku san babu wani yanki bai yi ba, daga su, sai wadannan mutanen da suke yan Arewa maso Gabas."
"Ko mutum yana so, ko ba ya so, Najeriya kasa ce ta Musulmi da Kirista. Ba zai yiwu ka ce kai kadai za ka yi ta mulki saboda su wadancan ba mutane ba ne."
'Dan majalisar APC ya yi wa Kwankwaso gori
A baya kun samu labarin cewa 'dan majalisar tarayya daga jihar Kano, Hon. Aliyu Sani Madakin Gini ya ce son kai da burin mukami ne suka hana Rabiu Kwankwaso shiga jam'iyyar APC ba komai ba.
Babban 'dan siyasar ya bayyana cewa shi ne ya hada ganawar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da shugaban kasa Bola AhmedTinubu, inda aka yi masa alkawarin mukamin minista kafin ya ki shiga APC.
'Dan siyasar, wanda ya fara takun saka da darikar Kwankwasiyya ya ce Kwankwaso ya koma NDC ne bayan ya fahimci ba zai samu burinsa na samun shugaban kasa ko mataimaki a ADC ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


