2027: Zabukan Sanatoci 4 da Za Su Fi Ɗaukar Hankali a Arewacin Najeriya
Yayin da ake ci gaba da tunkarar zaben 2027, gwagwarmayar neman kujerun majalisar dattawa da dama ta fara bayyana tsananin rikicin siyasa, rugujewar kawance, rikicin magaji da kuma fafatawar neman iko.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Daga Adamawa zuwa Gombe da kuma Kogi, takarar da ke bayyana yanzu ba wai kawai game da wakilci a majalisar tarayya ba ce illa siyasar neman iko.

Source: Facebook
Zaben sanatoci da zai iya yin zafi
Daily Trust ta ce a hankali siyasar na rikidewa zuwa ruguntsumin siyasa, tsarin neman iko a kujerar da kuma tsarin siyasar jihohi gabanin wani muhimmin zangon zabe.
A lokuta da dama, tsofaffin abokan siyasa sun zama manyan abokan hamayya, yayin da sabani, bukatun kashin kai da sauyin biyayya tsakanin jam’iyyu ke kara ruruta rikici tun kafin fara yakin neman zabe a hukumance.
Legit Hausa ta duba wasu zabukan sanatoci musamman a Arewacin Najeriya da za su fi daukar hankali.
1. Gombe: Gwamna Inuwa vs Sanata Dankwambo
A Gombe, siyasa ta fara zafi gabanin zaben shekarar 2027 yayin da Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya shirya tsayawa takarar kujerar majalisar dattawa, kamar yadda hadiminsa, Ismaila Uba Misilli ya rubuta a Facebook.
Gwamnan zai kara da tsohon gwamna Sanata Ibrahim Hassan Dankwambo da ke wakiltar mazabar Gombe ta Arewa, wanda kuma ake cewa yana neman wa’adi na gaba.
Fafatawar da ke tafe kan kujerar sanatan na rikidewa zuwa wata babbar karawar siyasa tsakanin manyan jiga-jigan siyasar jihar guda biyu, Dankwambo na jam’iyyar PDP mai adawa da kuma Inuwa Yahaya na APC mai mulki.
Takun-sakarsu ta siyasa ta fara ne tun sama da shekara 10 da suka gabata, kuma ta kasance daya daga cikin manyan fafatawar siyasa da suka fi daukar hankali a jihar Gombe.

Source: Facebook
2. Adamawa: Ahmadu Fintiri vs Aisha Binani
Siyasar Adamawa na kara sauyawa zuwa wata sabuwar fafatawa mai zafi tsakanin Gwamna Ahmadu Fintiri da Sanata Aisha Binani.

Kara karanta wannan
Shugaban majalisar dattawa ya yi wa 'yan Arewa barazana kan zaben 2027? Gaskiya ta fito
Duk da cewa ba a mazaba daya suke ba, ana ganin gwabzawa da suka sha yi a zabukan gwamna zai yi tasiri matuka kan zaben 2027 da ke tafe.
Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri zai fafata ne da fitaccen ɗan kasuwa wanda ya koma harkar siyasa, Abdulrahaman Kwacham.
Finiti da Binani sun jagoranci daya daga cikin zabukan gwamna mafi cike da ce-ce-ku-ce a Najeriya a shekarar 2023.
Zaben ya rikide zuwa babban rikici bayan Kwamishinan Zabe na Adamawa ya bayyana Binani a matsayin wadda ta lashe zaben alhali ana ci gaba da tattara sakamako, matakin da daga baya Hukumar INEC ta soke.
Daga bisani hukumar zaben ta bayyana Fintiri a matsayin halastaccen wanda ya lashe zaben bayan kammala dukkan matakan tattara sakamako.
A yanzu, Fintiri ya kammala wa'adinsa, yana neman takarar sanatan Adamawa ta Arewa yayin da ake hasashen Binani da ta koma NDC za ta yi takarar gwamna.

Source: Twitter
3. Kogi: Yahaya Bello vs Natasha Akpoti
Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya bayyana a hukumance aniyarsa ta tsayawa takarar kujerar majalisar dattawa ta Kogi ta Tsakiya a babban zaben shekarar 2027.

Kara karanta wannan
An dora Hayatu Deen a gaban Atiku, Obi da Amaechi a takarar zama shugaban kasa a 2027
Hakan ya sanya shi cikin shirin fafatawa da sanata mai ci yanzu, Natasha Akpoti-Uduaghan da ke wakiltar yankin.
Yayin da yake jawabi a taro, tsohon gwamnan ya ce ya amsa kiraye-kirayen magoya bayansa na neman kujerar majalisar dattawa, tare da nuna shirinsa na wakiltar Kogi ta Tsakiya a majalisar tarayya.
Rikicin siyasa tsakanin Yahaya Bello da Natasha Akpoti-Uduaghan na daya daga cikin manyan takun-sakar siyasa mafi zafi a Kogi da ma Najeriya baki daya, cewar Punch.
A tsawon shekaru takwas da Yahaya Bello ya yi yana gwamna, ya yi kokarin dakile karuwar tasirin Natasha wanda ya jawo hankalin jama’a kan gwamnatin jihar.

Source: Facebook
4. Gombe: Anthony Yaro vs Jerry Damara
Masu sharhi na ganin zaben sanata a yankin Gombe ta Kudu zai yi matukar zabi bayan dan siyasa mai mazabar ya rasa tikitin takara a APC.
Gwamna Inuwa Yahaya ya ce an yi zama tare da amincewa a Hon. Jerry Damara a matsayin wanda zai yi takara a kujerar sanatan Gombe ta Kudu.
Sanata Yaro ya dawo jam'iyyar APC ne a watan Afrilun 2026 kafin rasa tikitin takarar komawa majalisar dattawa da ya ci karkashin PDP.
Har ila yau, bayan rasa tikitin a APC, Sanata Yaro ya yi gaggawar fice wa daga jam'iyyar inda ya koma PDP domin kalubalantar abin da gwamnan da jam'iyyarsa ke so.

Source: Facebook
Gwamnonin da ke neman tazarce a Arewa
An ji cewa a Arewacin Najeriya akwai wasu gwamnoni da suke neman wa'adi na biyu yayin da ake tunkarar zaben 2027.
Akalla gwamnonin sun kai 10 daga yankin Arewa maso Gabas, Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya a Najeriya.
Wannan rahoton ya jero muku gwamnoni 10 da ke shirin sake neman kujerunsu a karo na biyu da kalubalen da za su fuskanta.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

