APC Ta Kara Karfi a Gombe, Sanatan PDP Ya Koma Jam'iyya Mai Mulki

APC Ta Kara Karfi a Gombe, Sanatan PDP Ya Koma Jam'iyya Mai Mulki

  • Jam'iyyar APC mai mulki a jihar Gombe ta kara karfi bayan wani sanata a jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya ya sauya sheka zuwa cikinta
  • Sanata mai wakiltar Gombe ta Kudu, Anthony Siyako Yaro, ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki bayan ya raba gari da tsohuwar jam'iyyarsa ta PDP
  • Sauya shekar sanatan ta sanya jam'iyyar APC ta kara karfafa karfin da take da shi a jihar Gombe yayin da ake tunkarar babban zaben shekarar 2027 da ke tafe

​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Gombe - Sanata mai wakiltar mazaɓar Gombe ta Kudu a majalisar dattawa, Anthony Siyako Yaro, ya fice daga jam'iyyar PDP.

Sanata Anthony Siyako Yaro ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki bayan ya fice daga PDP wadda ya lashe zabe karkashinta a shekarar 2023.

Kara karanta wannan

2027: An fara zargin Obi zai yaudari 'yan Arewa saboda ya muzguna masu a baya

Gwamna Inuwa Yahaya ya tarbi dan majalisar da ya koma APC
Anthony Siyako Yaro tare da Gwamna Inuwa Yahaya bayan komawarsa APC Hoto: Ismaila Uba Misilli
Source: Facebook

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa, babban mai kula da sashen yada labarai na gwamnan Gombe, Ismaila Uba Misilli, ya fitar a shafinsa na Facebook a ranar Juma'a, 24 ga watan Afirilun 2026.

APC na kara karfi a jihar Gombe

Ismaila Uba Misilli ya bayyana cewa Sanata Anthony Siyako Yaro shi ne na baya-bayan nan a jerin manyan masu sauya sheka da Gwamna Inuwa Yahaya, ya tsara yadda za su dawo jam'iyyar APC.

A baya ma wasu ’yan majalisar wakilai guda uku daga jam’iyyar PDP sun sauya sheka zuwa APC a jihar Gombe.

'Yan majalisar wakilan sun haɗa da, Babban mai tsawatarwa na marasa rinjaye na majalisar Wakilai, Hon. Ali Isa JC; ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Dukku/Nafada, Hon. Abdullahi El-Rasheed da kuma takwaransa na mazaɓar Yamaltu Deba, Hon. Inuwa Garba.

'Yan adawa na sauya sheka zuwa APC

A cewar Ismaila Uba Misilli, wannan sauya sheka ta baya-bayan nan zuwa jam’iyyar ta ƙarfafa ikon APC a jihar Gombe.

Kara karanta wannan

Sabon salo: APC ta faɗi tsari 2 da za ta yi amfani da su wajen zaɓen ƴan takara

Hakazalika ya bayyana cewa sauya sheka ya kara ƙarfafa rinjayen APC na siyasa a jihar Gombe gabanin babban zaɓen 2027.

Dan majalisar PDP a Gombe ya koma APC
Anthony Siyako Yaro da Gwamna Inuwa Yahaya Hoto: Ismaila Uba Misilli
Source: Facebook

'Dan majalisar PDP ya samu tarba

Ya ƙara da cewa babban mai tsawatarwa na majalisar wakilai, Hon. Usman Bello Kumo, da mataimakin sakataren kuɗi na APC na kasa, Hon. Hamma Adama Ali Kumo, sun haɗu da Gwamna Inuwa Yahaya domin karɓar Sanata Yaro zuwa cikin jam’iyyar.

Sauya-shekar dan majalisar dai ya raunana karfin da jam'iyyar PDP take da shi a jihar Gombe yayin da ake tunkarar zaben 2027.

Rashin PDP ya kara rinjayen APC a majalisa

A wani labarin kuma, kun ji cewa dan majalisar dokokin jihar Gombe wanda yake karkashin inuwar jam'iyyar PDP, ya sauya sheka zuwa APC mai mulki.

'Dan majalisar wanda ke wakiltar mazabar Billiri Gabas, Yakubu Daniel, ya sanar da ficewarsa daga PDP zuwa APC, lamarin da ya bar majalisar ba tare da ‘yan adawa ba.

Yakubu Daniel ya bayyana cewa ya yanke shawarar komawa APC ne saboda yadda gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, yake tafiyar da mulki cikin gaskiya da rikon amana.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng