‘Yadda Pantami Ya Wulakanta Sarkin Gombe, Ali Modu Sheriff’: Tsohon Hadiminsa

‘Yadda Pantami Ya Wulakanta Sarkin Gombe, Ali Modu Sheriff’: Tsohon Hadiminsa

  • Tsohon hadimin Isa Ali Pantami, Affan Buba Abuya, ya bayyana abubuwan da ya ce sun faru yayin da yake aiki tare da tsohon ministan
  • Abuya ya yi zargin cewa Pantami kan ƙi karɓar baƙi da dama a ofishinsa, ciki har da Sarkin Gombe, Sarkin Dukku da Ali Modu Sheriff
  • Ya ce sau da dama shi ne ke sanar da manyan baƙin cewa Pantami ba zai same su ba, lamarin da ya ce yana jawo masa matsin lamba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Pantami, Gombe - Tsohon hadimin Farfesa Isa Ali Pantami ya yi tone-tone game da yadda ya yi aiki da tsohon ministan.

Matashin mai suna Affan Buba Abuya ya yi aiki tare da Isa Ali Pantami lokacin da ya ke rike da mukamin minista daga 2019 zuwa 2023.

Kara karanta wannan

'Mahaddacin Kur'ani ne': An fadi riko da addini na babban soja da aka kashe

Tsohon hadimin Pantami ya bulluko da wasu halayensa
Farfesa Isa Ali Pantami da Affan Buba Abuya. Hoto: Professor Isa Ali Pantami da Affan Buba Abuya.
Source: Facebook

Hakan na cikin wani faifan bidiyo da Abuya ya wallafa a shafinsa na Facebook a yau Lahadi 2 ga watan Agustan shekarar 2026.

Tsohon hadimin Pantami ya yi tone-tone

A cikin bidiyon, Abuya ya ce lokacin da Pantami ya ke minista bai ba da dama mutane su gana da shi a ofis komai girman mutum.

Abuya ya tuna yadda Pantami ya ki amincewa ya gana da Sarkin Gombe da kuma na Dukku a lokuta daban-daban.

"Akwai ranar da aka yi rasuwa, Mai Martaba Sarkin Dukku ya zo shi ta'aziyya ya zo amma wallahi haka malam ya tafi, ya ce ba zai samu ganinsa ba, yana da tafiya a jirgi a gabansa.
"Minti daya kam ya kamata ya ba shi, mutumin da ya shigo har kusa da ofishinka, Mai Martaba yana raye ya sani.
"Kowa ya san yadda Sarkin Gombe yake son yaga dan Gombe da yake aiki ko kasuwanci yana ci gaba, mutum ne mai son mutane da alaka mai kyau da su.

Kara karanta wannan

An yi wa dan APC mai tallata Tinubu jina jina, za a farauci wadanda suka daka shi

"Da farko yana zuwa wurin malam yana yaba masa da kara karfin guiwa amma daga baya ya sa muka hana Sarkin Gombe ganinsa, yana hanya zai zo ofishinsa amma malam ya hana ya ce mu ce ya tafi fadar shugaban kasa."
Tsohon yaron Pantami ya yi tone-tone game da halayensa
Farfesa Isa Ali Pantami da Affan Buba Abuya. Hoto: Affan Buba Abuya.
Source: Twitter

Yadda Pantami ya ki ganawa da Sherrif

Affan ya ce kuma sun gane saboda abin da suka yi masa lokacin da ya je Gombe salla a masallacin fadar Sarki.

Matashin ya kuma tabbatar da cewa tsohon gwamnan Borno, Ali Modu Sherrif ya taba zuwa har cikin harabar ofishinsa amma Isa Ali Pantami ya ce ba zai ganshi ba.

"Akwai ranar da Ali Modu Sheriff ya zo ofishinmu kowa na tsoron ya je ya cewa malam yazo shi, nine na je ni saboda ni ne za a zage ni amma zan fada.
"Malam ya ce waye ya shigo da shi, ya rika zage-zage, har hakuri na ke ba shi cewa a rika ba manyan mutane ko minti daya ne, amma haka na fito na ce masa yana ganawa da mataimakin shugaban kasa."

Pantami: Rarara ya ce a jira fitowar wakarsa

Mun ba ku labarin cewa fitaccen mawaki Dauda Kahutu Rarara ya yi martani game da wakarda ya fitar wacce ta jawo maganganu a tsakanin alumma.

Kara karanta wannan

Juyin mulki: An gano yadda malaman addini suka karbi miliyoyi amma da wani nufi

Rarara ya bayyana cewa wakar siyasa ce ta yabon dan takararsa da gwamnan Gombe, yana jaddada cewa bai yi nufin cin mutunci ba.

Mawakin ya ce shi almajirin malamai ne kuma yana girmama su, amma ya soki malaman da ke amfani da zagi maimakon wa'azi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.