Halin da Wutar Lantarki ke ciki bayan Narka Kuɗi Sama da Naira Tiriliyan 10 a Najeriya
- Rahotanni sun nuna cewa an kashe sama da Naira tiriliyan 10 a bangaren wutar lantarki cikin shekaru 13 a Najeriya
- Ministan Wutar Lantarki, Joseph Tegbe, ya ce gwamnati ta fara gyara matsalolin da suka dade suna hana bangaren ci gaba
- Gwamnati ta ce cikin shekaru biyu zuwa uku za a samu ingantacciyar wutar lantarki da kwanciyar hankali a tsarin lantarki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Bayanai kan halin da wutar lantarki ke ciki sun nuna cewa sama da Naira tiriliyan 10 sun makale ko kuma an kashe su a bangaren ta hanyoyin tallafi da sauran shirye-shiryen gwamnati.
Sai dai Ministan Wutar Lantarki, Joseph Tegbe, ya ce Gwamnatin Tarayya ta fara sabon tsarin gyaran bangaren domin magance matsalolin da suka shafe fiye da shekaru 40 suna hana bangaren lantarki ci gaba.

Source: Instagram
Gwamnati ta fadi sababbin matakan gyara
Rahoton Vanguard ya rahoto ministan na cewa, sabon tsarin ya kunshi cikakken binciken fasaha kan layukan wutar lantarki na kasa da daidaita dokokin wutar lantarki tsakanin gwamnatin tarayya da jihohi
Tegbe ya ce:
"Cikin shekaru biyu zuwa uku masu zuwa, 'yan Najeriya za su ga canji a bangren wuta, raguwar asarar lantarki, kyakkyawan tsarin kasuwa, karin amincewar masu zuba jari, fadada samun wutar lantarki da karfin aiki."
Tiriliyoyin kudade da aka kashe tun 2013
Binciken ya nuna cewa tun bayan da aka sayar da kamfanonin wutar lantarki ga masu zaman kansu a watan Nuwamban 2013, gwamnatoci daban-daban sun kashe makudan kudade domin farfado da bangaren.
Daga cikin manyan shirye-shiryen akwai tallafin N213bn na CBN domin daidaita kasuwar wutar lantarki da N701bn na biyan kamfanonin samar da wuta (GenCos).
Sai kuma sama da Naira biliyan 200 na shirin samar da mitoci, N700bn na Shirin Presidential Metering Initiative (PMI) da kuma Yuro biliyan 2.3 na Shirin Siemens Presidential Power Initiative.
Haka kuma akwai sama da dala biliyan 2.4 daga Bankin Duniya da Bankin Raya Afirka, da kuma sabon shirin rage bashin bangaren wutar lantarki na tiriliyan N4.

Source: Getty Images
Har yanzu samar da wuta bai inganta ba
Duk da wadannan dimbin kudade, samar da wutar lantarki bai samu gagarumin ci gaba a Najeriya ba, cewar rahoton Daily Post.
Rahoton Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya (NERC) ya nuna cewa a rubu'in farko na shekarar 2026, matsakaicin karfin samar da wuta daga tashoshin lantarki 28 ya kai megawatt 4,457.96.
Wannan adadi ya yi kasa da burin gwamnatin tarayya na megawatt 6,000, kuma ya yi nisa da bukatar kasar da aka kiyasta ta haura megawatt 30,000.
Za a kara kudin wutar lantarki a Najeriya?
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta ce ba ta da shirin ƙara kuɗin wutar lantarki a yanzu, tana mai jaddada aniyarta ta inganta samar da wuta ga 'yan Najeriya.
Ministan Wutar Lantarki, Joseph Tegbe, ne ya bayyana hakan yayin wani taron tattaunawa da masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Legas.
Tegbe ya ce gyaran da ake yi wa fannin wutar lantarki ba yana nufin yin watsi da nasarorin da aka samu a baya ba.
Asali: Legit.ng

