Kungiyar Kiristoci Ta Kai Karar Tikitin Musulim Musulim ga Trump

Kungiyar Kiristoci Ta Kai Karar Tikitin Musulim Musulim ga Trump

  • Kungiyar Kiristoci ta CYAN ta fusata da yadda jam'iyya mai mulki ta APC ta dage a kan ci gaba da neman zaben 2027 da tikitin Muslim-Muslim
  • Ta ruga zuwa Amurka, inda ta kai kara ga shugaban kasar Donald Trump game da abin da ta kira barazana ga Kiristocin Najeriya baki daya
  • Kungiyar ta bukaci Amurka ta ci gaba da sanya Najeriya cikin jerin ƙasashen da ake samun barazana ga rayuwar Kiristoci wata CPC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Wata ƙungiyar haɗaka ta ƙungiyoyin matasan Kiristoci da masu rajin kare haƙƙin ɗan Adam mai suna CYAN ta rubuta takardar ƙorafi zuwa ga Shugaban Amurka, Donald Trump.

Kungiyar ta kuma kai wasikar korafin ga Majalisar Dokokin Amurka kan batun tikitin Musulm-Musulim da jam'iyyar APC ke shirin amfani da shi a zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Rikici ya danno cikin kungiyar goyon bayan Obi da Kwankwaso gabanin 2027

Kiristoci sun kai karar tikitin takarar APC ga Trump
Shugaban Najeriya Bola Tinubu da Shugaban Amurka Donald Trump Hoto: Bayo Onanuga/Donald J Trump
Source: Twitter

Jaridar Nigerian Tribune ta kawo labarin cewa takardar da aka kuma aika wa Sakataren Harkokin Wajen Amurka da mambobin Majalisar Dattawa da ta Wakilai, ta ce ƙungiyar na neman Amurka ta ci gaba da sanya ido kan abin da ta kira tabarbarewar tsaron Kiristoci a Najeriya.

Kiristoci sun kai karar Najeriya ga Trump

Jaridar Daily Post ta wallafa cewa CYAN ta yabawa matakin da Amurka ta ɗauka na mayar da Najeriya cikin jerin kasashen da ake da damuwa a kansu game da rayuwar Kiristoci.

A cikin takardar, ƙungiyar ta ce:

"Muna yaba wa matakin sake sanya Najeriya cikin jerin CPC, domin hakan ya taimaka wajen karyata labaran da ke ƙoƙarin bayyana kashe-kashen Kiristoci a matsayin hare-haren 'yan bindiga kawai, maimakon abin da al'ummomin yankunan suka sani cewa kashe-kashen addini ne da aka shirya."

Sai dai ta ce har yanzu kashe-kashen ba su tsaya ba, tana mai ikirarin cewa an kashe Kiristoci akalla 30 a ƙauyen Naridon da ke jihar Kaduna cikin makon nan.

Kara karanta wannan

Amurka ta yi kuskure da ta yi magana kan harin 'yan bindiga a Kaduna

Kiristoci sun ce ana masu barazana

CYAN ta ce ci gaba da amfani da tikitin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Mataimakinsa Kashim Shettima a zaɓen 2027 zai ƙara jefa Kiristoci cikin haɗari, musamman a Arewacin Najeriya.

Ana neman Trump ya sa ido a kan Najeriya
Shugaban kasar Amurka Donald Trump Hoto: Donald J Trump
Source: Twitter

Ta ce:

"A ra'ayinmu, ci gaba da riƙe tikitin Musulm-Musulm a zaɓen 2027 shi ne babbar barazanar siyasa ga lafiyar Kiristoci a Najeriya, musamman a yankin Arewa."

Ƙungiyar ta kuma yi zargin cewa tikitin Tinubu da Shettima na 2023 ya karya al'adar da aka saba bi ta raba manyan mukaman ƙasar tsakanin mabiya addinai biyu.

'Kungiyar ta yi zargin cewa gwamnatin Najeriya ta ɗauki kamfanonin hulɗa da jama'a a Washington domin inganta martabarta bayan sake sanya ƙasar cikin jerin CPC.

Amurka ta yi magana kan harin Kaduna

A baya, mun kawo labarin cewa Amurka ta yi Allah-wadai da harin da ya kashe aƙalla mutum 30, ciki har da yara, magidanta da mata a jihar Kaduna da ke Arewacin Najeriya.

Kara karanta wannan

Komai ya fito fili, INEC ta saki bayanan karatun Tinubu da Shettima

Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ce za ta ci gaba da matsa wa gwamnatin Najeriya kan matsalar tsaro a yankin Arewa ta Tsakiya na Najeriya bayan matsayarta kan zargin kisan Kiristoci.

Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya umarci hukumomin tsaro su ƙara ƙaimi wajen gano waɗanda suka kai harin, sannan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nemi a kamo 'yan ta'addan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng