Sulhu ko Kato bayan Kato: Jam'iyyar APC Ta Kaddamar da Fara Zaben Fitar da Gwani

Sulhu ko Kato bayan Kato: Jam'iyyar APC Ta Kaddamar da Fara Zaben Fitar da Gwani

  • Jam’iyyar APC za ta fara zaben fitar da gwani na ‘yan takarar majalisar wakilai a mazabu 360 na fadin Najeriya daga gobe
  • Manyan ‘yan siyasa da shugabannin majalisa da suka hada da Abbas Tajudeen da Benjamin Kalu na neman tikitin komawa majalisa
  • APC ta ce duk da matsin lokaci da koke-koke, za ta gudanar da zabukan cikin lumana tare da bin jadawalin da aka tsara a farko

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Jam’iyya mai mulki a kasa, APC, za ta fara gudanar da zaben fitar da gwani domin zakulo ‘yan takararta na majalisar wakilai gabanin zabukan shekarar 2027.

Rahotanni sun nuna cewa masu neman tikitin majalisar wakilai za su fara fafatawa a mazabu 360 da ke fadin kasar nan daga ranar gobe.

Jam'iyyar APC ta kaddamar da fara zaben fitar da gwani da 'yan majalisar wakilai
Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Prof. Nentawe Goshwe Yilwatda yana jawabi a ofishinsa a Abuja. Hoto: @OfficialAPCNg
Source: Twitter

A hedikwatar jam’iyyar da ke Abuja, jami’an APC sun kasance cikin tarurruka domin tattara rahotannin tantance ‘yan takara da kuma sauraron koke-koke daga masu neman tikiti, in ji rahoton The Nation.

Kara karanta wannan

2027: Masu neman takara sun cika sakatariyar APC da gidan shugaban jam'iyya

Wani mamba na kwamitin gudanarwa na kasa (NWC) ya bayyana cewa tsarin na fuskantar kalubale saboda karancin lokaci da yawan ayyukan da ake gudanarwa.

Daga cikin manyan jiga-jigan APC da ke neman komawa majalisar wakilai akwai:

  • Shugaban majalisar wakilai, Abbas Tajudeen
  • Mataimakin kakakin majalisa, Benjamin Kalu
  • Shugaban masu rinjaye, Farfesa Julius Ihonvbere
  • Kakakin majalisa, Akin Rotimi
  • Ado Doguwa
  • James Abiodun Faleke
  • Tsohuwar minista, Nkeiruka Onyejeocha
  • Chijioke Edoga
  • Leke Abejide wanda ya sauya sheka daga ADC zuwa APC
  • Bimbo Daramola daga Ekiti
  • Kafilat Ogbara daga Legas
  • Oluwole Oke daga Osun
  • Donald Ojogo daga Ondo

Shugabannin majalisun jihohi sun shiga takara

Rahotanni sun nuna cewa wasu manyan ‘yan majalisun jihohi ma suna neman shiga majalisar wakilai ta tarayya.

Daga cikinsu akwai shugaban majalisar Legas, Mudashiru Obasa da shugaban majalisar Rivers, Martins Amaewhule.

Sakataren yada labarai na APC na kasa, Felix Morka, ya jaddada cewa ba za a sauya ranar da aka sanya domin gudanar da zaben fidda gwanin ba.

Ya bayyana cewa APC za ta bi tsarin zaben kai tsaye idan ba a samu maslaha tsakanin ‘yan takara ba, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Atiku ya 'bankado' shirin gwamnoni game da tazarcen Tinubu a zaben 2027

An samu koke-koke daga wasu ‘yan takara

Majiyoyi sun bayyana cewa kwamitin sauraron koke-koke na APC ya gudanar da zama a Treasures Suites da ke Abuja domin duba korafe-korafen da suka taso bayan tantancewar.

Jam'iyyar APC ta ce ba za ta sauya tsarin jadawalin zaben fitar da gwaninta ba.
Tutar APC a wani gangamin jam'iyyar da aka gudanar. Hoto: @OfficialAPCNg
Source: Twitter

Sai dai wani jami’in jam’iyyar ya ce duk da matsin lamba daga wasu bangarori, ba a hana ko dan takara daya shiga zaben fitar da gwani ba.

A cewarsa:

“An yi kokarin hana wasu takara amma kwamitin tantancewa ya tsaya tsayin daka a kan haka, aka kyale kowa ya yi takara bisa tsarin doka.”

Majiyoyi daga APC sun ce gwamnoni na ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen tsara irin tsarin zaben fitar da gwani da zai fi dacewa da jihohinsu.

An ce kwamitocin gudanar da zaben fitar da gwani sun riga sun isa jihohi domin hada kai da gwamnoni wajen tabbatar da gudanar da zabukan cikin lumana.

Tinubu ya aika sako ga 'yan APC

A wani labari, mun ruwaito cewa, shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi jawabi ga mambobin APC yayin da ake shirin fara zaben fitar da gwani.

Kara karanta wannan

Sabani ya bulla APC bayan kifar da mutum 150 yayin tantance masu son takara

Mai girma Bola Tinubu ya bukaci mambobin APC da masu neman takara da su nuna halin dattako yayin da ake shirin fara zaben fitar da gwanin.

Shugaban kasar ya bukaci su ba 'yan adawa kunya ta hanyar kin tayar da rikici a zabubbukan fitar da gwanin na jam'iyyar APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com