Gwamnatin Tinubu ta fara aiwatar da muhimmin aiki a Kano, zai amfani miliyoyin mutane
- Hukumar FERMA ta fara gyaran titin Kano Eastern Bypass mai tsawon kilomita 13 domin rage cunkoson ababen hawa a cikin birnin Kano
- Ana gudanar da aikin ta hanyar amfani da ma’aikatan hukumar kai tsaye tare da tura kusan ma’aikata 70 zuwa titin
- Ana sa ran kammala aikin cikin makonni biyu bayan fara shi a ranar 23 ga Yulin shekarar 2026
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida
Jihar Kano - Hukumar Kula da Gyaran Hanyoyin Tarayya (FERMA) ta fara gyaran titin Kano Eastern Bypass mai tsawon kilomita 13 da ya lalace, a wani yunkuri na rage cunkoson ababen hawa a cikin birnin Kano.
Injiniyan da ke kula da aikin, Sarfil Umar, ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a lokacin duba yadda aikin ke gudana ranar Asabar, 1 ga watan Agustan 2026 a Kano.

Source: Original
Umar ya ce ana gudanar da aikin ne ta hanyar amfani da ma’aikatan hukumar kai tsaye, inda aka tura kusan ma’aikatan FERMA 70 tare da wasu ma’aikatan da aka dauka aiki zuwa sassan titin.
Ya ce titin hanya ce mai muhimmanci ta gwamnatin tarayya da ke hada hanyar Maiduguri da jihohin Katsina da Kaduna ta hanyar Kano Eastern Bypass.
Muhimmancin titin Kano Eastern Bypass
Umar ya ce gyaran titin zai taimaka wajen saukaka zirga-zirgar ababen hawa tare da kara tsawon rayuwar hanyar.
“Baya ga saukaka zirga-zirgar ababen hawa, ana sa ran aikin zai kara tsawon rayuwar titin ta hanyar hana lalacewar kwalta sakamakon ruwan sama, da rage bukatar gudanar da gyare-gyare masu tsada a gaba."
“Haka kuma, aikin zai rage kudin tafiyar da ababen hawa ga dubban matafiya da masu safarar kaya da ke amfani da hanyar a kullum."
“Titin na da matukar muhimmanci wajen zirga-zirga a Kano, domin yana hada motocin da ke tafiya mai nisa daga Arewa maso Gabas zuwa Arewa maso Yamma, tare da bai wa masu ababen hawa damar kauce wa cunkoson da ake samu a cikin birnin.” In ji shi
Ya bayyana cewa manyan motoci masu dauke da amfanin gona, dabbobi, man fetur da kayayyakin masana’antu suna yawan amfani da titin wajen safarar kaya tsakanin Kano da jihohin da ke makwabtaka da ita.
Saboda haka, ya ce yanayin titin na da matukar muhimmanci ga harkokin kasuwanci da safarar kaya a yankin.
Lokacin kammala aikin
Umar ya ce an fara aikin gyaran ne a ranar 23 ga Yuli, kuma ana sa ran kammala shi cikin makonni biyu.
A cewarsa, aikin ya hada da toshe ramukan da ke kan titi, cire laka daga magudanan ruwa, kwashe shara da sauran abubuwan da suka toshe hanyoyin ruwa, da kuma gyara ginshikan fitilun titin da suka lalace a kan hanyar mai bangarori biyu.
Ya ce an ga bukatar gudanar da aikin ne sakamakon daminar da ake ciki, yana mai bayyana cewa toshewar magudanan ruwa na sa ruwa ya dade a kan tituna, wanda yana daga cikin manyan abubuwan da ke haddasa lalacewar hanyoyin tarayya.
Barazanar ruwa ga tituna
Umar ya ce kula da magudanan ruwa na daga cikin muhimman hanyoyin kare tituna, domin tsayuwar ruwa na raunana tubalin titin, da kara yawan ramuka, tare da rage tsawon rayuwar kwalta.
Ya bukaci mazauna yankin da masu amfani da titin su daina zuba shara a magudanan ruwa. Umar ya gargadi cewa toshewar hanyoyin ruwa na kara hadarin ambaliya tare da jefa jarin da gwamnati ta zuba wajen gina hanyoyi cikin hadari.

Source: Twitter
Gwamnatin Kano za ta gina titi
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya ce ya kaddamar da fara gina titin karkara mai nisan kilomita 7.2 daga Mil Goma zuwa 'Yankatsari.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce gwamnatin Kano za ta kashe Naira biliyan 2.6 wajen aiwatar da aikin gina titin.
Asali: Legit.ng


