Ndume, Natasha da Sanatocin da Aka Buga da Su a Majalisa a Mulkin Akpabio

Ndume, Natasha da Sanatocin da Aka Buga da Su a Majalisa a Mulkin Akpabio

Tun kafa majalisa ta 10 a Najeriya a 2023 aka fara kai ruwa rana da wasu Sanatoci da suka soki majalisar ko gwamnatin tarayya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Tun bayan kafa majalisar dattawa ta 10 da Sanata Godswill Akpabio ke jagoranta aka fara samun sabani da wasu sanatoci.

Sabani ya kai ga dakatar da wasu Sanatoci, wasu kuma an kai ga rage musu matsayi saboda wasu maganganu da suka yi a kan gwamnati mai ci.

Ndume
Sanatocin da aka buga da su a majalisa. Hoto: Nigerian Senate|Kola Sulaimon
Asali: Facebook

A wannan rahoton, mun tattaro muku jerin wasu Sanatoci da suka samu matsala a majalisar da yadda aka kai ruwa rana da su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Sanata Abdul Ningi

Sanata Abdul Ningi daga jihar Bauchi na cikin Sanatocin da aka buga da su a majalisar dattawa ta 10.

Kara karanta wannan

Sanata Natasha: Shugaban Majalisa, Akpabio ya dira kan ƴan Najeriya

Rahoton Channels TV ya nuna cwa an samu sabani da Sanata Ningi a majalisa wanda hakan ya kai ga dakatar da shi na tsawon watanni uku.

Ningi
Sanata Abdul Ningi. Hoto: Nigerian Senate
Asali: Facebook

Dalilin dakatar da Sanata Ningi

A ranar 12 ga Maris, Majalisa ta dakatar da Sanata Ningi na tsawon watanni uku bayan ya yi iƙirarin cewa an ƙara N3.7tn a kasafin kuɗin 2024 ba tare da an san inda aka nufa da kuɗin ba.

A lokacin da ake tuhumarsa, Ningi ya yi zargin cewa ana gudanar da kasafin kuɗi iri biyu a Najeriya, kuma an fifita wasu yankuna fiye da wasu.

Ce-ce-ku-ce kan zargin da Ningi ya yi

Bayan fitar da wadannan bayanai, wasu daga cikin ‘yan majalisa da fadar shugaban ƙasa sun soki kalaman Sanata Ningi, suna masu cewa basu da tushe.

Daga baya Ningi ya janye wani ɓangare na maganarsa, yana mai cewa ba wai ana da kasafin kuɗi iri biyu ba, amma akwai Naira 3.7 tiriliyan da ba a bayyana inda za a kashe su ba.

Kara karanta wannan

Rabuwar kai a Majalisa, Sanatoci 13 ba su sa hannu a dakatar da Natasha ba

Majalisa ta dawo da Sanata Ningi

Dawo da Abdul Ningi ya zo ne makonni biyu kafin wa’adin dakatarwarsa ya ƙare a ranar 12 ga Yuni, 2024.

Mataimakin shugaban marasa rinjaye a majalisa, Sanata Abba Moro ne ya jagoranci buƙatar janye dakatarwar, yana mai cewa Ningi ya yi nadama kuma ya ɗauki alhakin abin da ya faru.

Bayan haka, Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya sanar da cewa an amince da dawo da Ningi, yana mai bayyana shi a matsayin ƙwararren ɗan majalisa mai muhimmanci.

2. Sanata Ali Ndume

Duk da cewa yana jam'iyya mai mulki ta APC, Sanata Ali Ndume ya fuskanci kalubale a majalisar dattawa sakamakon wasu maganganu.

Majalisa ta cire Ali Ndume daga matsayin mai tsawatarwa a kan wasu maganganu da ya yi game da salon mulkin Bola Tinubu.

Ndume
Sanata Ali Ndume. Hoto: Kola Sulaimon
Asali: Twitter

Majalisa ta sauke Ndume daga mukaminsa

Majalisar Dattawa ta sanar da cire Sanata Ali Ndume daga mukaminsa na mai tsawatarwa a ranar Laraba, 6 ga Maris, 2024, yayin zaman majalisa.

Kara karanta wannan

Ajali ya yi kira: Hatsabibin ɗan bindiga, Shekau ya mutu yayin arangama da ƴan ta'adda

Sauke Ndume ya biyo bayan amincewar ‘yan majalisar APC bayan Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio, ya sanya batun a ƙuri’a.

Bayan daukar matakin, Sanata Tahir Mungono mai wakiltar Borno ta Arewa ne ya karɓi mukamin da aka sauke Ndume daga shi.

Hakan ya faru ne bayan wasu kalaman da Ndume ya yi, inda ya soki yadda gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke tafiyar da al’amura.

APC ta bukaci Ndume ya sauya sheka

Bayan sauke shi daga mukaminsa, jam’iyyar APC ta rubuta wa ‘yan majalisar dattawa takarda, inda ta bukaci Ndume ya fice daga jam’iyyar idan ba ya gamsu da yadda ake tafiyar da al’amura.

Shugaban APC na ƙasa, Dr Abdullahi Umar Ganduje, da Sakatare na ƙasa, Ajibola Bashiru, suka sanya wa wasikar hannu.

Sai dai daga baya APC ta yafe wa Sanata Ali Ndume, amma duk da haka bai dawo matsayinsa na mai tsawatarwa ba.

Kalaman da Ndume ya yi a kan Tinubu

Kara karanta wannan

Sanatan Katsina ya fusata, ya soki sharadin yi wa Natasha afuwa

Ndume ya bayyana cewa Shugaba Tinubu bai san halin da al’umma ke ciki ba, yana mai cewa wasu sun ‘killace’ shi daga ganin gaskiya.

A cikin hirar da ya yi da manema labarai a Majalisar Dattawa, Daily Trust ta wallafa cewa Ndume ya ce:

"Shugaban ƙasa ba ya san halin da mutane ke ciki. An rufe masa hanya kuma an hana shi jin abin da ke faruwa a waje.
Akwai matsalar karancin abinci, kuma gwamnati ba ta ɗaukar matakin da ya dace. Rashin abinci matsala ce babba fiye da kowace matsala."

3. Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan

Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan na daya daga cikin Sanatoci mata da suka rika kai ruwa rana da Sanata Akpabio.

A baya bayan nan, lamarin ya kai ga zargin shugaban majalisar da neman lalata da ita bayan sun samu sabani yayin wani zama wanda daga karshe aka dakatar da ita.

Kara karanta wannan

Ramadan: Direba ya murkushe sufetan ɗan sanda da ke bakin aiki a masallacin Abuja

Sanata Natasha
Sanata Natasha daga jihar Kogi. Hoto: Natasha Akpoti-Uduaghan
Asali: Twitter

Dalilin dakatar da Sanata Natasha

Majalisar Dattawa ta dakatar da Sanata Natasha na tsawon watanni shida bayan da ta gabatar da ƙorafi cewa Shugaban Majalisar, Sanata Godswill Akpabio, ya nemi lalata da ita.

Sanata Natasha ta fara yin wannan zargi ne a wata hira da ta yi da manema labarai, lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce a fadin kasar nan.

Kwamitin ladabtarwa na majalisa ya ce an yi watsi da ƙorafin nata saboda rashin bin tsari, sannan ya bada shawarar dakatar da ita bisa dalilin kawo wa majalisa abin kunya.

A bisa hakika, majalisa ta ce da dauki matakin dakatar da ita ne saboda rikici da aka yi da ita kan wajen zama ba saboda zargin da ta yi ba.

Martani kungiyoyin kare hakkin mata

Bayan sanar da dakatarwarta, wata mai fafutukar kare hakkin mata, Hadiza Ado, ta bayyana cewa hakan wani mataki ne da zai dakile yancin mata a siyasar Najeriya.

Kara karanta wannan

Natasha ta ja daga, ta nufi kotu kan dakatarwar watanni 6 da majalisa ta yi mata

BBC ta wallafa cewa Hadiza Ado ta ce:

"Rana ce ta bakin ciki ga mata a Najeriya. Daga cikin sanatoci 109, guda hudu ne kawai mata, yanzu kuma daya daga cikinsu an dakatar da ita,"
Akpabio
Shugaban majalisa, Sanata Akpabio. Hoto: Nigerian Senate
Asali: Facebook

4. Sanata Kawu Sumaila

Majalisar Dattawan Najeriya ta yi kakkausar gargaɗi ga Sanata Kawu Sumaila bayan ya yada wata hira da ke dauke da zarge-zargen da ba su da inganci a shafinsa na sada zumunta.

Kano times ta wallafa cewa hirar ta kunshi kalaman Sanata Abdul Ningi, inda ake zargin akwai rashin daidaito a kasafin kudin kasa da fifita yankuna.

Sanata Sumaila
Sanata Kawu Sumaila. Hoto: Hassan Dan Kano
Asali: Twitter

SERAP ta yi magana kan Sanata Natasha

A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar SERAP ta gargadi Sanata Akpabio kan dakatar da Sanata Natash Akpoti Uduaghan a da aka yi.

Kungiyar ta bukaci majalisar dattawa da janye dakatarwar da ta yi wa Sanata Natashi tana mai cewa ba bisa kai'da aka dakatar da ita ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng