Dalilan da Suka Ja Matan da ke Majalisar Dattawa Suka Juyawa Natasha baya

Dalilan da Suka Ja Matan da ke Majalisar Dattawa Suka Juyawa Natasha baya

A yayin da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ke fuskantar kalubale a majalisar dattawa, wasu manyan mata ‘yan siyasa a ƙasar nan sun yi burus da faɗin bahaushe na 'ciwon ƴa mace, na ƴa mace ne.'

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT AbujaWasu daga cikin mata ƴan siyasa, daga ciki har da takwarorinta mata ‘yan majalisa a kasar nan sun ƙi goyon bayanta, yayin da wasu suka yi gum a kan batun.

Oluremi
Wasu mata 'yan siyasa sun soki Sanata Natasha Hoto: Senator Oluremi Tinubu/Natasha H Akpoti/Sen Ireti Kingibe Crew
Asali: Facebook

Legit ta tattaro wasu daga cikin matan da ba sa tare da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, musamman bayan da ta zargi shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, da cin zarafi.

1. Sanata Remi Tinubu ta goyi bayan majalisa

Uwargidan shugaban kasa, Oluremi Tinubu, ta bayyana ra'ayinta kan rikicin da ya taso a majalisar dattawa tsakanin Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan da Godswill Akpabio.

Kara karanta wannan

Akpabio: Majalisa ta lissafo manyan zunuban da suka sanya aka dakatar da Natasha

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Premium Times ta wallafa cewa a tattaunar ta da manema labarai, Oluremi Tinubu ta jaddada muhimmancin girmama majalisar dattawa, saboda a cewarta, wuri ne mai daraja.

Ta ce:

"Majalisar dattawa wuri ne na dattako, dole ne a mutunta ta, na yi aiki a can na tsawon shekaru 12, mata su dage ka da a raina su."

Sanata Remi Tinubu ta kuma bayyana goyon bayanta ga matakan da majalisar dattawa ta dauka a kan batun zargin cin zarafi da Sanata Natasha ta yi.

2. Yadda Ireti Kingibe ta kwayewa Natasha baya

Jaridar Punch ta wallafa cewa Sanata Ireti Kingibe ta ce canjin wuraren zama a majalisa ya shafi sauran 'yan majalisan mata, ba Natasha kawai ba, saboda haka bai kamata ta rika yin babatu ba.

Ta jaddada cewa bin dokokin majalisar ya fi muhimmanci fiye da mayar da hankali kan batutuwan da ba su da muhimmanci, duk da haka ta tabbatar da cewa.

Kara karanta wannan

Daga ƙarshe, Sanatocin PDP sun ziyarci Natasha, sun yi mata babban alkawari

Sanata
Sanata Kingibe ta soki Natasha Hoto: Sen Ireti Kingibe Crew
Asali: Facebook

Sanatar Abujan ta bayyana cewa babu wani abu mai kama da matsa wa mata 'yan majalisa, duk da cewa ta tabbatar da cewa Natasha ta taba shaida mata cewa Akpabio ya gayyace ta zuwa otal.

3. Tsohuwar Sanata ta caccaki Natasha

Sanata Ita-Giwa ta mayar da martani kan zargin cin zarafi da Akpoti-Uduaghan ta yi wa Godswill Akpabio, tana cewa irin wadannan koke-koke alamun rauni ne.

Ta ce:

"Idan har ka tsaya takara ka kuma lashe zabe har ka shiga majalisar dattawa, ka riga ka wuce matakin da za a ci zarafinka ta fuskar neman lalata.
Mata a majalisar dattawa da maza duk daya muke."

4. Natasha: Ma'aikatan majalisa mata sun jinjinawa Akpabio

Mata masu taimaka wa 'yan majalisa sun bayyana godiyarsu ga jagorancin Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio duk da dambarwar da ke gudana tsakaninsa da Natasha.

Duk da cece-kuce a kan zarge-zargen da Sanatar Kogi ta Tsakiya da aka dakatar da yi masa, waɗannan mata sun bayyana Akpabio a matsayin mai goyon bayan mata da adalci a tsakaninsu.

Kara karanta wannan

Rabuwar kai a Majalisa, Sanatoci 13 ba su sa hannu a dakatar da Natasha ba

Sanata
Mata masu aiki aiki a majalisa sun karrama Akpabio Hoto: Solomom Ogor
Asali: Facebook

Sun ce:

"Mun yarda kuma muna godiya ga goyon bayan da Shugaban Majalisar Dattawa ke bayarwa ga mata a siyasa da shugabanci. Kuma muna goyon bayan ƙoƙarinsa na inganta adalci da daidaito."

Akwai masu ganin cewa, wannan lamari ne da ya shafi mata, kuma ya kamata su dauki dumi tare da nuna damuwa kan abin da ya shafi Natasha.

Akwai kuma ganin bai kamata Natasha ta dauko wannan lamari ta kawo gaban majalisa ba, inda suke ganin ya kamata a daidaita ba tare da duniya ta sani ba.

Ba sabon abu bane samun bayanai masu tada hankali a majalisar Najeriya ba, akwai masu ganin dama an saba abin kunya a majalisar.

Sanatan Katsina ya caccaki Natasha

A wani labarin, kun ji cewa Sanata mai wakiltar Kudancin Katsina, Dandutse Mohammed Muntari, ya ce bai ji dadin shawarar da aka bayar na rage dakatarwar Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ba.

Wannan shawara ta taso ne daga wata tattaunawa da aka yi a majalisar, inda aka bayyana cewa za a iya rage wa ko soke dakatarwar idan Sanata Natasha ta rubuta takardar neman afuwa ga majalisar.

Kara karanta wannan

Sanatan Katsina ya fusata, ya soki sharadin yi wa Natasha afuwa

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Salisu Ibrahim ya fadada labarin nan ta hanyar kara bayani kan matsayar matan majalisa kan batun Akpabio da Natasha.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng