Kotu Ta Taka wa Majalisar Tarayya Birki kan Shirin Sayan Motocin Alfarma na N110bn

Kotu Ta Taka wa Majalisar Tarayya Birki kan Shirin Sayan Motocin Alfarma na N110bn

  • Babbar Kotun Tarayya da ke Lagos ta soke shirin kashe N110 biliyan na Majalisar Tarayya kan motocin SUV da alawus
  • Kotun ta ce kashe N40 biliyan da N70 biliyan ga ‘yan majalisa ya saba ka’ida, yana nuna cin moriyar kai da rashin bin gaskiya
  • SERAP ta yabawa hukuncin kotu, yayin da aka umarci Godswill Akpabio da Tajudeen Abbas su tabbatar duk kudaden gwamnati kashe su bisa doka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Babbar Kotun Tarayya da ke zaune a Lagos ta yi hukunci kan shirin kashe makudan kudi na biliyoyin Naira saboda motocin alfarma.

Majiyoyi suka ce Majalisar Tarayya na shirin kashe makudan kudin wanda kotun ta bayyana a matsayin haramun da saba dokoki

Kotu ta haramta kashe N110bn wurin sayan motocin yan majalisa
Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio da Rt. Hon. Tajudeen Abbas. Hoto: The Nigeria Senate.
Source: Twitter

Kotu ta dakile majalisa kan shirin sayan motoci

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta raba tallafin N6.6bn ga yan Najeriya domin rage talauci

Kotun ta kuma bayyana cewa kashe N40 biliyan wajen sayen motocin ‘yan majalisa 465 da kuma N70 biliyan a matsayin saba doka, cewar Punch.

Hukuncin ya kuma umarci Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, da Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, su tabbatar cewa duk kashe kudaden gwamnati a gaba na Majalisa zai bi doka, gaskiya da rikon amana.

An yanke hukuncin ne ranar Laraba, 6 ga Mayu, 2026, a cikin shari’a mai lamba FHC/L/CS/1606/2023 wadda ƙungiyar SERAP ta shigar a kan Majalisar Tarayya.

Kwafin hukuncin da aka tabbatar ya bayyana a ranar Lahadi, inda SERAP ta ce ta shigar da karar ne tun watan Agusta 2023 saboda shirin kashe kudin a lokacin da ake fama da matsin tattalin arziki a ƙasar.

Kotu ta haramta shirin majalisa na sayan motocin alfarma har N110bn
Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio yana jagorantar zama majalisa. Hoto: The Nigerian Senate.
Source: Facebook

Abin da alkalin kotun ya ce

Alkalin kotu, Mai Shari’a Yellim Bogoro, ta ce irin wannan kashe kudi ba tare da bin ka’ida ba yana nuna rashin gaskiya da amfani da ofis don son kai.

Ta ce:

“Girman kudin da aka kashe da rashin bin ka’ida ya nuna cewa aikin ya saba doka kuma ba shi da adalci.”

Kara karanta wannan

Bayan yaudara na shekaru, Tinubu ya ƙaddamar da gyaran hanyar Gombe zuwa Maiduguri

Ta kuma kara da cewa masu amfana da kudin su ne wadanda suke amincewa da shi, abin da ke nuna cin moriyar kai da rikicin amfani.

Kotun ta ce a halin da Najeriya ke ciki na matsin tattalin arziki, irin wannan kashe kudi ba ya fifita bukatun kasa, cewar Daily Post.

Ta kuma ce kariyar “ikon majalisa” ba za ta zama kariya ga karya doka ba, domin kotu na da ikon sa ido kan bin doka da kundin tsarin mulki.

Kungiyar SERAP ta ce hukuncin babban nasara ne ga gaskiya, rikon amana da ingantaccen amfani da kudin jama’a a Najeriya.

Lauyan kare hakkin dan adam, Femi Falana (SAN), ya ce dole ne a yaba da hukuncin, yana mai cewa rayuwar ‘yan kasa a halin matsin tattalin arziki ba za a yi watsi da ita ba saboda jin daɗin ‘yan siyasa.

Akpabio ya karyata cewa zai ba sanatoci tikiti

Kun ji cewa Majalisar Dattawa ta yi magana game da alkwarin da aka ce shugabanta, Godswill Akpabio ya yi wasu sanatocin.

Rahotanni a baya sun bayyana cewa majalisa za ta duba wasu daga cikin sanatocin da suka fadi zaben fitar da gwani.

Akpabio ya ce ya nuna tausayi ne kawai ga wadanda suka sha kaye, ya ce APC na kokarin warware matsalolin da suka taso.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.