Akpabio Ya Kalubalanci Hurumin Kotu kan Koken Sanata Natasha

Akpabio Ya Kalubalanci Hurumin Kotu kan Koken Sanata Natasha

  • A ranar Litinin, 10 ga watan Maris, 2025 ne kotu ta ci gaba da sauraron karar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta shigar kan dakatar da ita
  • Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya kalubalanci hurumin babbar kotun tarayya kan tsoma baki a harkokin da suka jibanci majalisa
  • Bayan sauraron bangarorin da ke shari’a da juna, kotun ta dage sauraron karar har zuwa watan Maris 2025 domin ba kowa damar kara shiri

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware wajen kawo rahotanni kan al’amuran da suka shafi mata, yara, da siyasa.

FCT Abuja Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya kalubalanci ikon Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja na sauraron karar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta shigar.

‘Yar majalisar mai wakiltar Kogi ta Tsakiya ta shigar da kara a gaban kotu tana kalubalantar matakin ladabtar da ita da Majalisar Dattawa ta dauka.

Kara karanta wannan

Daga ƙarshe, Sanatocin PDP sun ziyarci Natasha, sun yi mata babban alkawari

Natasha
Akpabio ya kalubalanci kotu a kan Natasha Hoto: Natasha H Akpoti/Godswill Obot Akpabio
Asali: Twitter

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa Godswill Akpabio, ta bakin tawagar lauyoyinsa karkashin jagorancin Kehinde Ogunwumiju, SAN, ya na kalubalantar ikon kotu na tsoma baki a harkokin majalisa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A ci gaba da shari’ar a ranar Litinin, Ogunwumiju, SAN, ya bayyana cewa har yanzu Sanata Akpoti-Uduaghan ba ta isar da takardun shari’ar yadda ya kamata ba.

Akpabio ya soki Sanata Natasha a kotu

Sahara Reporters ta ruwaito cewa lauyoyin Akpabio sun ce sai an isar da takardun shari'a gare su kafin su samu damar kalubalantar sahihancin karar.

Baya ga Sanata Akpabio da aka ambata a matsayin wanda ake kara na uku a shari’ar, an kuma hada da Sakataren Majalisar Tarayya da Majalisar Dattawa.

Sauran wadanda Sanata Natasha ke kara sun hada da Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Hakkoki, Ladabtarwa, da Korafe-korafe.

Lauyan Natasha karyata bangaren Akpabio

A gefe guda, lauyan mai shigar da kara, Michael Numa, SAN, ya dage kan cewa an aika da takardun shari’a ga dukkan bangarorin da abin ya shafa.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta tsoma baki kan zargin shugaban Majalisa da neman matar aure

Ya shaidawa kotu haka ne ta hanyar jan hankalinta zuwa takardun shaida da ke cikin kundin kotu, wanda ke nuna cewa an aika wa wadanda ake kara da takardun.

Bayan duban takardun shaida na isar da sakonni, Mai shari’a Obiora Egwuatu ya tabbatar da cewa an aika wa dukkan wadanda ake kara da takardun.

Natasha: Lauyoyin Akpabio sun nemi a dage shari’a

A wannan matakin, lauyoyin Sanata Akpabio sun bukaci kotu ta dage ranar ci gaba da sauraron shari'ar domin ba su damar shiryawa yadda ya dace.

Natasha
Kotu ta dagea karar da Natasha ta shigar gabanta Hoto: Natasha H Akpoti
Asali: Original

Daga bisani, Mai shari’a Egwuatu ya dage sauraron karar zuwa ranar 25 ga Maris, tare da umartar bangarorin su kammala gabatar da takardun da suka dace kafin wannan rana.

Akpabio ya soki 'yan Najeriya kan Natasha

A wani labarin, mun wallafa cewa shugaban majalisa, Godswill Akpabio ya ce 'yan Najeriya suna tofa albarkacin bakinsu kan dambarwar Natasha Akpoti-Uduaghan ba tare da cikakken sani ba.

Kara karanta wannan

Ta faru ta kare: Majalisar dattawa ta dakatar da sanatar Kogi na tsawon watanni 6

Sanata Akpabio ya ce ya kamata jama’a su fahimci yadda majalisa ke aiki, domin sai da kwamitin ladabtarwa na majalisar ya bi duk ka’idojin da suka dace kafin dakatar da sanatar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng