Sanata Natasha: Shugaban Majalisa, Akpabio Ya Dira kan Ƴan Najeriya
- Shugaban majalisar dattawa, ya ce masu yin sharhi kan al’amuransu ba su da cikakken ilimi game da abubuwan da suke magana a kai
- Godswill Akpabio yana fadin hakan ne lokacin da ake dambarwa kan dakatar da Sanata Natasha Akpoti Uduaghan da ta zarge shi da cin zarafi
- Ya ce hukuncin dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan yana kan ka'ida, domin sai da aka bi dukkanin matakan da aka shimfida a doka
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Shugaban Majalisar Dattijawa, Godswill Akpabio, ya yi suka ga wadanda ke yin sharhi kan al’amuran majalisa kan dambarwar Sanata Natasha Akpoti Uduaghan.
Shugaban majalisar ya kwatanta muhawarar 'yan kasar nan kan batun da magoya bayan kungiyoyin kwallon kafa, wanda ba su san abin da su ke magana a kai ba.

Asali: Facebook
The Cable ta ruwaito cewa Akpabio ya yi wannan magana ne lokacin da ya karbi wata tawaga ta shugabannin matasa daga yankin Neja Delta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya nuna damuwarsa game da abin da ya kira "muhawarar jama'a ba tare da sani ba" kan al’amuran da ke gudana a cikin majalisa.
Akpabio ya yi bayani kan dakatar da Natasha
Jaridar Nigerian Tribune ta ruwaito cewa Akpabio ya ce hukuncin majalisa na dakatar da Natasha ya yi daidai da dokokin majalisar da tsarin ladabtarwasu.
Ya ce:
"Ya kamata ku tafi ku bincika gaskiyar lamarin kafin ku fara yin sharhi a talabijin."
"Idan ba ku karanta baibul ko kuma ba ku da alaka da Kiristanci, ba za ku iya yin ikirarin sanin abin da ya ke cewa ba. Haka ma, idan ba limamai ba ne, ba za ku iya fatawa da ayoyin Al-Kur'ani ba."
"A amma kuna ganin wasu mutane da ba su da cikakken ilimi suna zaune suna yin sharhi kamar yadda ake yi a wasan kwallon kafa, suna cewa, 'Ronaldo ya kamata ya buga kwallon nan daga hagu."
Natasha: Akpabio ya soki ‘yan Najeriya
Shugaban majalisar dattawa ya ce majalisar na da nasu tsarin warware matsaloli, yana mai cewa batun dakatarwar Natasha Akpoti-Uduaghan yana bisa tsari.

Asali: Twitter
Ya ce:
"Idan mutane ba su da cikakken ilimi game da hanyoyin da ake bi amma suka fara muhawara kan sharuddan da ba su fahimta ba, wani lokaci, wannan abu yana damuna."
"Don haka muna ba da shawara ga jama'a da su daina yin sharhi kan abubuwan da ba su sani ba, suna kuskure wajen fassara dokokin majalisa."
'Yan siyasa mata sun guji Sanata Natasha
A wani labarin, kun ji cewa Uwargidan shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu, Ireti Kingibe, Sanata Ita Giwa da matan da ke taimakawa 'yan majalisa sun juya wa Natasha Akoti baya.
A yayin da ta zargi shugaban majalisa, Godswill Akpabio da nemanta a lokuta da dama, matan sun yi tir da irin wannan kalamai a matsayinta na Sanata, suka ce bai dace ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng