Bayan 'Yan Kwanaki hannun ’Yan Bindiga, Yayar Tsohon Minista, ’Ya’yanta Sun Kubuta

Bayan 'Yan Kwanaki hannun ’Yan Bindiga, Yayar Tsohon Minista, ’Ya’yanta Sun Kubuta

  • 'Yar uwar tsohon ministan wutar lantarki, Busayo Adegoke John-Paul, da 'ya'yanta tagwaye sun samu 'yanci
  • Wata majiya daga rundunar 'yan sanda ta tabbatar da cewa an kubutar da su cikin dare, bayan kokarin jami'an tsaro
  • Rahotanni sun ce maharan dauke da makamai sun bi motarsu daga gida kafin su tare su a Elewura-Challenge suka sace su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ibadan, Oyo - Majiyoyi daga rundunar yan sanda sun tabbatar da cewa an kubutar da yayar tsohon ministan makamashi da yan bindiga suka sace.

An ce Busayo Adegoke John-Paul, 'yar uwar Adebayo Adelabu, da 'ya'yanta tagwaye da aka sace a cikin makon nan sun samu 'yanci.

An ce yayar tsohon ministan makamashi a Najeriya
Yayar tsohon minista da yaranta kafin a sace su a hagu da yayanta, Adebayo Adelabu. Hoto: Bayo Adelabu.
Source: Facebook

Wata majiya a rundunar 'yan sanda ta tabbatar wa manema labarai a Ibadan cewa an yi nasarar ceto su a daren ranar Asabar 6 ga watan Yunin 2026, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Kwana ya kare: Tsohon shugaban UNILORIN ya rasu bayan ya dawo daga sallar Isha'i

Yadda aka sace yan uwan tsohon minista, Adelabu

Rahotanni sun bayyana cewa an sace John-Paul tare da 'ya'yanta maza tagwaye masu shekaru 12 a yankin Elewura-Challenge da ke Ibadan ta Kudu maso Yamma.

An ce wasu maharan dauke da makamai sun bi motar da ke dauke da su tun daga gidansu kafin su tare su da misalin karfe 7:30 na safe.

Rahoton ya kuma tuna cewa wani jigo na jam'iyyar APC a Oyo, Wale Oriade, ya taba fadawa hannun masu garkuwa da mutane a Ibadan a watan Disamban 2025.

Shaidu sun bayyana cewa maharan sun zo ne cikin wata motar Micra mai launin shudi, inda suka yi awon gaba da shi cikin tsari da ya tada hankalin al'umma.

Yan sanda sun yi nasarar ceto yayar tsohon minista
Taswirar jihar Oyo da ke Kudu maso Yammacin Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

'Yan sanda sun hallaka yan bindiga

An kashe wasu mutane biyu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne bayan musayar wuta da jami’an ‘yan sanda, yayin da aka kwato bindigogi biyu daga hannunsu, cewar The Nation.

Kara karanta wannan

Tafiyar Atiku ta shiga matsala a Gombe, 'yan ADC sun koma APC da PDP

Majiyoyin ‘yan sanda sun bayyana cewa ci gaba da bibiyar bayanan sirri da matsin lambar dabarun tsaro ya tilasta wa masu garkuwar shiga artabu da jami’ai, lamarin da ya kai ga ceto wadanda aka sace cikin nasara.

Wata majiya ta ce:

“An ceto mutanen da aka sace a raye yayin arangamar. An kashe wasu mutane biyu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a musayar wuta da jami’an ‘yan sanda, yayin da aka kwato bindigogi biyu daga hannunsu.”

A halin yanzu, jami’an tsaro na ci gaba da sintiri da bincike a yankunan da ke kusa domin cafke sauran mambobin kungiyar masu garkuwa da mutanen, inda ake kyautata zaton wasu daga cikinsu sun tsere da raunukan harbin bindiga.

Makinde ya yi wa tsohon minista alkawari

A baya, an ji yadda Gwamnan Oyo, Seyi Makinde, ya nuna damuwa game da sace yayar tsohon minista a gwamnatin Bola Tinubu.

Makinde ya tabbatar wa tsohon ministan makamashi, Adebayo Adelabu, cewa gwamnati na kokarin ceto matar da 'ya'yanta biyu da aka sace.

Gwamnan ya kai ziyarar jaje ga Adelabu da iyalansa domin nuna goyon baya tare da yi masa bayanin matakan da gwamnati ke dauka kan lamarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.