Ramadan: Direba Ya Murkushe Sufetan Ɗan Sanda da Ke Bakin Aiki a Masallacin Abuja

Ramadan: Direba Ya Murkushe Sufetan Ɗan Sanda da Ke Bakin Aiki a Masallacin Abuja

  • Wani direba da ya saba dokar hanya ya buge wani sufetan dan sanda a kusa da Masallacin Kasa, Abuja, a daren jiya Alhamis
  • Direban mai suna David Auta, yana tuka mota kirar 'Toyota Hummer' daga Cibiyar Kiristoci ta Kasa zuwa Wuse Zone 4, inda ya saci hanya
  • Hakan ya haddasa wa sufeta James Haruna raunuka da karyewar kafar hagu, kuma an garzaya da shi zuwa Asibitin kasa da ke Abuja
  • ‘Yan sanda sun cafke direban tare da kwace motarsa, an ji cewa ana ci gaba da bincike kuma ana shirin gurfanar da shi a kotu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Wani sufetan dan ‘yan sanda ya samu munanan raunuka bayan wani direba ya buge shi a kusa da Masallacin Abuja.

Direban da ake zargin ya saba dokar hanya ya biyo ta inda bai dace ba tare da buge jami'in dan sandan da ke bakin aiki.

Kara karanta wannan

Ajali ya yi kira: Hatsabibin ɗan bindiga, Shekau ya mutu yayin arangama da ƴan ta'adda

Yan sanda sun cafke direba da ya buge jami'ansu a Abuja
An kama motar direban da ya buge jami'in dan sanda a masallacin Abuja. Hoto: Nigeria Police Force.
Asali: Facebook

'Dan sanda ya mutu bayan farmakin matasa

Wata majiyar tsaro ta shaida wa Zagazola Makama cewa lamarin ya faru da misalin karfe 9:00 na daren ranar Alhamis 6 ga watan Maris, 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na zuwa ne bayan wani sufetan dan sanda ya mutu a jihar Plateau bayan dukan tsiya da wasu matasa suka yi masa a Jos.

Rundunar yan sanda ta tabbatar da mutuwar jami'in mai suna Ikale Mohammed da aka kai wa farmaki a birnin Jos.

Rahotanni sun ce an farmaki dan sandan ne a ranar 1 ga Maris yayin da yake kokarin kama wanda ake zargi da safarar miyagun kwayoyi.

Wanda ake zargin ya tsere, amma daga baya ya dawo da ‘yan acaba suka kai wa ‘yan sanda hari inda Muhammed ya samu munanan raunuka.

Direba ya buge jami'in dan sanda a Abuja
Yan sanda sun cafke direban da ya buge jami'insu a masallacin Abuja. Hoto: Nigeria Police Force.
Asali: Twitter

Yadda direba ya buge jami'in dan sanda

An ce direban mai suna David Auta yana tuka motar bas kirar 'Toyota Hummer' mai lamba: FKJ 527 CW.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun bude wuta kan masu taron siyasa a Najeriya, an harbi mutane 14

Majiyoyi sun ce direban ya kaucewa dokar hanya inda ya bi hannu daya wanda ya yi sanadin buge jami'in dan sanda.

Majiyar ta ce:

“Direban ya kauce wa alamar hanya, ya saci hanya, ya buge sufatan dan sanda mai suna James Haruna wanda ke bakin aiki a kofar masallacin."

An tabbatar da hakan ya haddasa masa raunuka da karyewar kafar hagu, sannan an garzaya da shi zuwa Asibitin Abuja, inda yake karbar magani a halin yanzu.

Rahotanni sun ce ‘yan sanda sun cafke direban tare da kwace motarsa nan take yayin da ake ci gaba da bincike da shirin gurfanar da shi bisa tuhumar tukin ganganci.

Ana zargin tsohon jami'in tsaro da safarar makamai

Kun ji cewa Rundunar ƴan sandan a Abuja ta samu nasara a ƙoƙarin da take yi wajen yaƙi da masu aikata laifuffuka.

Rundunar ta cafke wani tsohon jami'in hukumar shige da ficen Najeriya (NIS), mai safarar makamai ga ƴan bindiga.

Kara karanta wannan

'Yadda na yi watsi da sunan da iyayena suka rada mani': Obasanjo ya yi fallasa

Rahotanni sun ce an cafke shi ne ɗauke da manyan makamai lokacin da yake ƙoƙarin kai su ga ƴan bindiga a jejin Abuja zuwa Kaduna.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng