Babachir Ya Fadi Wanda Ya Yi Kulle Kulle Aka Kore Shi a Gwamnatin Buhari

Babachir Ya Fadi Wanda Ya Yi Kulle Kulle Aka Kore Shi a Gwamnatin Buhari

  • Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal, ya ce ya fice daga ADC ne saboda rashin adalci a zaɓukan fitar da gwani
  • Babachir ya zargi shugabannin jam’iyyar da fifita Atiku Abubakar, yana mai cewa an ware wasu sahihan ‘yan takara
  • Ya kuma yi iƙirarin cewa tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa ne ya taka rawa wajen sauke shi daga mukaminsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal ya yi martani kan ce-ce-ku-cen da suka biyo bayan ficewarsa daga jam’iyyar ADC.

Babachir ya ce ya bar jam’iyyar ne saboda abin da ya kira watsi da dimokuraɗiyya cikin gida, inda ya zargi shugabanni da karkatar da zaɓukan fitar da gwani.

Babachir ya caccaki tsarin jam'iyyar ADC
Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal. Hoto: Babachir David Lawal.
Source: Facebook

Legit Hausa ta samu wannan bayani ne a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook a yau Lahadi 7 ga watan Yunin 2026.

Kara karanta wannan

Birtaniya za ta sa ido kan zaben Najeriya domin tabbatar da adalci

Babachir ya caccaki jam'iyyar ADC

A cikin rubutunsa, Babachir ya yi zargin cewa an shirya zaɓukan ne domin bai wa Atiku Abubakar da magoya bayansa fifiko.

Ya ce an ware wasu sahihan ‘yan takara daga fafatawa, tare da cewa an riga an tsara sakamakon wasu zaɓukan tun kafin gudanar da su.

Tsohon sakataren gwamnatin ya bayyana cewa ba zai iya ci gaba da zama a jam’iyyar da ta zama hanyar tabbatar da takarar Atiku Abubakar ba.

Sai dai kalaman da ya yi sun jawo suka daga magoya bayan Atiku, duk da cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasar bai shiga musayar yawu ba.

Dalilin rasa mukamin Babachir a mulkin Buhari

Babachir ya kuma yi ƙoƙarin fayyace batun da ya kai ga cire shi daga mukami, yana mai cewa ba gaskiya ba ne cewa an same shi da laifin cin hanci.

Ya ce wasu mutane sun shirya makarkashiya domin a kore shi daga ofis saboda kusancinsa da tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

Kaico: Matashi ya aika mahaifinsa lahira bayan yi masa dukan kawo wuka

Har ila yau, ya bayyana cewa tun shekarar 1971 Buhari ya kasance mai gidansa, kuma hakan ya sa wasu suka fara tunanin yana samun wata gata ta musamman.

A cewarsa, wasu sun yi adawa da naɗinsa a matsayin SGF saboda asalinsa daga ƙaramar ƙabilar Kilba da kuma kasancewarsa Kirista.

Ya ce bayan Buhari ya ƙi amincewa da matsin lambar da aka yi masa, wasu sanatoci da masu ruwa da tsaki suka fara neman hanyoyin sauke shi.

Lawal ya yi iƙirarin cewa wani babban jigo daga baya ya nemi afuwarsa a gaban abokansu bayan ya fahimci yadda aka tafiyar da lamarin.

Babachir ya fadi yadda Osinbajo ya raba shi da kujerarsa
Marigayi Muhammadu Buhari, Babachir Lawal da Yemi Osinbajo. Hoto: Muhammadu Buhari, Babachir David Lawal.
Source: Facebook

Zargin Babachir kan rasa kujerarsa

Ba tare da ambaton suna ba, ya yi zargin cewa tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa ya ci gaba da matsa wa Buhari lamba kan batun.

Ya ce shugaban ƙasar ya fara watsi da rahoton farko na majalisar dattawa bayan shawarar babban lauyan gwamnati cewa bai cika ka’ida ba.

Sai dai daga baya an ba da damar gudanar da bincike na daban wanda, a cewarsa, ya ba da shawarar a cire shi daga mukami.

Lawal ya ce daga bisani an miƙa batun ga EFCC domin gudanar da cikakken bincike da gurfanarwa a kotu.

Kara karanta wannan

Zamfara: Ana jita jitar ba malami takara a ADC, Mahadi ya magantu kan janyewa

Babachir ya caccaki Tinubu, Atiku, Obi

Mun ba ku labarin cewa tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal ya caccaki APC, PDP, ADC da NDC, yana cewa dukkan manyan jam’iyyun ba su ba da manufa.

Ya ce zai iya zaɓar matashin ɗan takara a 2027, amma ya bayyana rashin gamsuwa da dukkan manyan ‘yan takarar da ake da su yanzu a Najeriya.

Babachir wanda Muhammadu Buhari ya kora daga ofis ya ce ya yi murabus daga ADC saboda zargin rashin gaskiya a zaben fitar da gwani da aka yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.