‘Zaben Peter Obi da Kwankwaso kamar ba Tinubu Damar Nasara ne a 2027’

‘Zaben Peter Obi da Kwankwaso kamar ba Tinubu Damar Nasara ne a 2027’

  • Jigon ADC mai adawa a Najeriya ya bayyana damuwa game da zaben dan takarar NDC, Peter Obi da Rabiu Kwankwaso a 2027
  • 'Dan siyasar ya ce goyon bayan Peter Obi a zaben shugaban kasa na 2027 na iya taimaka wa Bola Tinubu kai tsaye ko a kaikaice
  • Tsohon kakakin LP ya bukaci jam’iyyun adawa su hade kan dan takara guda domin kauce wa rarrabuwar kuri’u a zaben 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Tsohon kakakin jam’iyyar LP kuma jigo a jam’iyyar ADC, Kenneth Okonkwo, ya yi magana game da zaben shekarar 2027.

Keneth Okonkwo ya bayyana cewa goyon bayan Peter Obi a zaben shugaban kasa na 2027 na iya karawa Shugaba Bola Tinubu damar samun wa’adi na biyu.

Jigon ADC ya caccaki takarar Obi da Kwankwaso
Sanata Rabiu Kwankwaso, Peter Obi da Bola Tinubu. Hoto: Mr Peter Obi, Bayo Onanuga.
Source: Twitter

Yayin wata hira da yan jaridu wanda Tribune ta bibiya, Okonkwo ya yi magana kan siyasar adawa da shirye-shiryen tunkarar zaben shugaban kasa mai zuwa.

Kara karanta wannan

Bayan sukar kalamansa a 2023, Peter Obi ya shawarci matasa kan siyasar addini, kabilanci

Matsalar da 'yan adawa za su samu

A cewarsa, jam’iyyun adawa dole ne su hada kai bayan dan takara guda idan suna son kayar da shugaban kasa mai ci a zaben 2027.

Ya gargadi cewa fitowar ‘yan takarar adawa da yawa za ta raba kuri’u kuma hakan zai yi aiki ne domin amfanin Tinubu.

Ya ce:

“Dalilin da ya sa na fadi haka shi ne ko dai kana yi wa Tinubu aiki kai tsaye, wato kana cikin APC, ko kuma kana yi masa aiki a kaikaice.
“Idan ka raba kuri’un hadakar adawa da sauran ‘yan adawa, kana kara sanya Tinubu cikin matsayi mafi kyau na samun nasara.”
An shawarci mutane su guji zaben Obi da Kwankwaso
Dan takarar shugaban kasa a NDC, Peter Obi da mataimakinsa, Rabiu Kwankwaso. Hoto: Mr. Peter Obi.
Source: Facebook

Yadda Obi ke gudun kalubale a siyasarsa

Okonkwo ya kuma yi magana kan rahotannin da ke cewa Peter Obi ya janye daga tattaunawar hadakar siyasa da ake yi a karkashin jam’iyyar ADC.

Ya yi zargin cewa tsohon gwamnan Anambran bai nuna sha’awar shiga zaben fiar da gwani mai cike da gasa ba, cewar rahoton Punch.

Kara karanta wannan

'Atiku da Peter Obi su sake bude wa Tinubu kofa, APC na iya lashe zaben 2027'

A cewarsa:

“Ba za ka guji fafatawa a zaben fitar da gwani ba kana son zama dan siyasa. Kana son zama shugaban kasa a kasa mai kalubale amma kana guje wa kalubale.”

Ya kuma yi zargin cewa Sanata Victor Umeh mai wakiltar Anambra ta Kudu ya taba bayyana cewa mafi kyawun damar yankin Kudu maso Gabas na samar da shugaban kasa ita ce ta hanyar hadin gwiwa da ‘yan siyasar Arewa.

A karshe, Okonkwo ya bukaci magoya bayan adawa su yi la’akari da illar rabuwar kawuna kafin zaben 2027.

Peter Obi ya magantu kan siyasar kabilanci, addini

A wani labarin, mun ba ku rahoton cewa dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya shawarci matasan Najeriya yayin da ake tunkarar zaben 2027.

Obi ya buƙaci matasan Najeriya su guji rarrabuwar kawuna ta hanyar ƙabilanci da addini, su rungumi haɗin kai.

Tsohon gwamnan ya ce bayan zaɓen 2023 a Lagos, tattaunawa ta karkata zuwa ƙabilanci wanda bai dace ba ko kadan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.