Natasha Ta Ja Daga, Ta Nufi Kotu kan Dakatarwar Watanni 6 da Majalisa Ta Yi Mata

Natasha Ta Ja Daga, Ta Nufi Kotu kan Dakatarwar Watanni 6 da Majalisa Ta Yi Mata

  • Sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, ta bayyana cewa ba za ta lamunci dakatarwar da majalisa ta yi mata ba
  • Lauyanta, Victor Giwa, ya zargi Majalisar Dattawa da yin kunnen uwar shegu da umarnin kotu na hana ta daukar matakin ladabtar da sanatar
  • Ya bayyana cewa kowanne dan Najeriya na da damar neman hakkinsa a gaban kotu, saboda haka ba za su nade hannayensu su yi shiru ba

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT AbujaSanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, za ta kalubalanci hukuncin dakatar da ita na watanni shida da Majalisar dattawan kasar nan ta yi.

An dauki matakin dakatar da ita ne bayan musayar yawu da ta yi da Shugaban majalisa, Sanata Godswill Akpabio, kan yadda aka shirya zama a zauren.

Kara karanta wannan

Yadda majalisar dattawa ta yi biris da rokon Sanata kan dakatar da Natasha

Natasha
Sanata Natasha za ta nufi kotu kan dakatar da ita Hoto: Natasha H Akpoti
Asali: Facebook

A wata tattaunawa da ta kebanga ga jaridar Punch, lauyan Sanata Natasha, Victor Giwa, ya soki korar da majalisa yi wa wacce yake wakilta, yana mai cewa matakin tauye hakki ne da saba doka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lauyan Sanata Natasha ya caccaki majalisa

Victor Giwa ya bayyana cewa Kwamitin ladabtarwa na majalisar dattawa ya saba wa umarnin kotu a matakin da ya dauka.

A cewarsa:

“Dakatarwar ta ci karo da doka, wanda ke nufin ba za ta iya aiki ba. Kotu ta bayar da umarni cewa kwamitin kada ya dauki wani mataki, amma sun saba doka.”
Natasha
Ana zargin majalisa da tauye hakkin Natasha Hoto: Natasha H Akpoti
Asali: Facebook

Ya kara da cewa idan da Natasha ba ta dauki matakin neman hakkinta a kotu ba, da dakatarwar da aka yi mata ta halatta.

Ana zargin majalisa da tauye hakkin Natasha

Lauyan Natasha ya jaddada cewa Matakin Majalisa ba ya saba da doka, kuma za su dauki matakin doka kan wadanda suka ci zarafin umarnin kotu.

Kara karanta wannan

Ta faru ta kare: Majalisar dattawa ta dakatar da sanatar Kogi na tsawon watanni 6

Ya ce:

“Za mu koma kotu. Shari’ar za ta ci gaba a cikin makonni biyu, kuma za mu shaidawa kotu cewa duk da an sanar da su, har da Shugaban Majalisa, sun yi watsi da umarnin kotu ta hanyar dakatar da Sanata Natasha.”

Da aka tambaye shi ko akwai shirin kai maganar ga kungiyoyin duniya, Giwa ya ce:

“A yanzu muna shirin shari’a ne a Najeriya. Amma duniya ta na kallo, kuma majalisa dole ta bi ka’idojin kasa da kasa, wadanda suka hana daukar mataki kan lamari da ke kotu.”

Giwa: "Majalisa ta karya kundin tsarin mulki"

Victor Giwa ya ce kundin tsarin mulkin Najeriya ya fi karfi a kan dokokin majalisa, saboda kowane dan kasa na da damar neman hakkinsa a kotu idan an tauye masa ‘yanci.

Ya kara da cewa:

“Sashe na 6, sakin layi na 6 na kundin tsarin mulki yana bai wa kowane dan kasa damar neman hakkinsa idan aka tauye masa ‘yancinsa. Natasha ta bi wannan hanya ne domin kare hakkin ta.”

Kara karanta wannan

Ana batun cin zarafin Sanata, Remi Tinubu ta bukaci karin wakilcin mata a majalisa

Majalisa ta dakatar da Sanata Natasha

A baya, kun ji cewa Majalisa ta dakatar da Sanata Natasha Akpoti bisa zargin cewa ta karya dokokin majalisa bayan ta yi ikirarin cewa Shugaban Majalisa, Godswill Akpabio, ya ci zarafinta.

Daga cikin matakan ladabtar da Sanatar, an dakatar da albashi da alawus dinta, za a rufe ofishinta, an janye jami’an tsaron dake ba ta kariya, sannan an haramta mata shiga majalisa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng