Sanata Natasha Ta Kai Karar Akpabio ga Kungiyar 'Yan Majalisun Duniya
- Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta kai karar Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ga Kungiyar Majalisun Duniya (IPU)
- Ta bayyana cewa tana neman ɗaukinsu wajen sa baki kan dakatarwar da Majalisar Dattawan Najeriya ta yi mata ba bisa ƙa'ida ba
- Natasha ta yi zargin an dakatar da ita na tsawon watanni shida ne saboda ta zargi Akpabio da nemanta da lalata a lokuta da dama
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
New York, USA — Natasha Akpoti-Uduaghan, Sanata mai wakiltar yankin Kogi ta Tsakiya, ta kai karar Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ga kungiyar 'yan majalisu ta duniya (IPU).
A lokacin da ta ke jawabi a taron IPU da aka gudanar a hedkwatar Majalisar Dinkin Duniya da ke birnin New York a ranar Talata, ta zargi majalisar dattawan Najeriya da saba doka.

Asali: Facebook
Jaridar The Cable ta wallafa cewa Sanatar ta yi zargin an dakatar da ita ne saboda jifan Godswill Akpabio da zargin neman lalata da ita a wurare daban-daban.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Natasha ta yi takaicin dakatar da ita a Majalisa
Jaridar Leadership ta wallafa cewa zargin da Natasha ta yi wa Akpabio ya biyo bayan wata hatsaniya da ta barke tsakaninsu kan tsarin zaman ‘yan majalisa a zauren majalisar dattawa.
A sakamakon hakan, majalisar dattawa ta dakatar da ita na tsawon watanni shida daga ranar 6 ga watan Maris bisa zargin tayar da rikici kan batun raba kujeru.

Asali: Facebook
Sai dai Natasha ta na zargin cewa an dakatar da ita ne saboda zargin da ta yi wa shugaban majalisar, bayan sun shafe lokaci su na samun sabani a majalisar dattawa.
Natasha ta nemi duniya ta taimaka mata
A yayin zaman taron IPU, Sanatar ta ce ta na neman adalci da kuma shiga tsakani daga kungiyoyin kasa da kasa masu kare dimokuradiyya kan dakatar da ita ba bisa ka'ida ba.
Ta ce:
"Ina zuwa gare ku da zuciya cike da damuwa daga Najeriya. Amma da farko, zan so in ba da hakuri ga mai girma Kafilat Ogbara. Ba don na ci fuskar kasata na zo nan ba, sai don neman taimako ga mata a Najeriya."
"Ranar 6 ga watan Maris 2025, an dakatar da ni daga zama sanata ba bisa ka'ida ba saboda na gabatar da ƙorafi kan cin zarafin da shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya yi min.
Yadda Natasha ta so majalisa ta dube ta
Sanatar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan ta ce a lokacin da ta mika kokenta na zargin Akpabio da cin zarafi, ta yi zaton za a gudanar da bincike cikin adalci.
Ta kara da cewa:
"Na yi tunanin idan na gabatar da ƙorafin, zai janye kansa daga batun sannan mu biyun mu mika kanmu ga kwamitin ladabtarwa da bincike don yin adalci da bayyananniyar bincike.
"Amma abin takaici, an yi mani shiru. An dakatar da ni na tsawon watanni shida tare da wadansu sharudda da suka hada da janye jami’an tsaro na, karbe dukkan motocin gwamnati da aka bani a matsayin sanata, da kuma hana ni albashi.
"Ina nema wa mata adalci," Natasha
Sanata Natasha ta ce dakatarwar da aka yi mata ba ita kadai zai shafa ba, illa alama ce ta yadda ake ware mata daga jagorancin siyasa a Najeriya.
Sanatar ta kara da bayyana cewa:
"Wannan babbar alama ce ta cin zarafi a siyasa, hana mata yin magana game da rashin adalci, cin hanci da rashawa da kuma nuna wariyar jinsi."
Sanata ya yi bayani kan zargin kare Natasha
A wani labarin, kun ji cewa tsohon shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya musanta cewa ya goyi bayan Natasha Akpoti-Uduaghan kan zargin cin zarafin da ta yi wa Godswill Akpabio.
Ya ce maganganun da ya yi a zauren majalisar dattawa a ranar 6 ga watan Maris, 2025, ba su da wata alaƙa da zarge-zargen da ake yi wa Akpabio, kawai ya ja hankali ne kan ladabtar da Natasha.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng