ADC na Son Raba Gawuna da Kwankwaso, An Yi Masa Tayin Takarar Gwamnan Kano
- Jam’iyyar ADC na ƙoƙarin jawo tsohon ɗan takarar gwamnan Kano, Nasiru Gawuna, daga NDC inda ya haɗe tare da Rabi'u Musa kwankwaso
- Rahotanni sun nuna cewa an fara tattaunawa da manyan abokan siyasar Gawuna domin shawo kansa bayan an yi masa alkawaru uku
- Daga cikin alkawuran da ake zargin jam’iyyar ta yi har da bai wa wasu daga cikin magoya bayansa takara a majalisun Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Jam’iyyar adawa ta ADC ta ƙara kaimi wajen ƙoƙarin shawo kan tsohon ɗan takarar gwamnan jihar Kano, Nasiru Yusuf Gawuna domin ya dawo cikinta.
Rahotanni sun bayyana cewa ADC na yi Gawuna waɗansu manyan alkawura, daga ciki har da alkawarin ba shi takarar gwamna a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar a babban zaɓen shekarar 2027.

Kara karanta wannan
Isra'ila ta yi ikirarin hallaka kwamandan Hezbollah ana kokarin tsagaita wuta a Lebanon

Source: Twitter
Rahotanni daga majiyoyin da ke da masaniya kan lamarin sun bayyana wa Daily Nigerian cewa wasu jiga-jigan jam’iyyar suna tattaunawa da na kusa da Gawuna domin ganin ya amince da tayin tikitin gwamna na ADC.
ADC na neman Gawuna
Ana ganin wannan yunƙuri na daga cikin dabarun da jam’iyyar ke bi domin ƙarfafa tasirinta a wasu muhimman jihohin ƙasar nan gabanin zaɓen 2027.
Majiyoyin sun ce ADC ta yi wasu muhimman alkawuran siyasa domin jawo hankalin Gawuna da magoya bayansa zuwa jam’iyyar.
A cewar majiyoyin, jam’iyyar ta nuna shirinta na bai wa wasu daga cikin amintattun magoya bayan tsohon mataimakin gwamnan guraben tsayawa takara.

Source: Twitter
Ana sa ran za a ba su takara ne a kujerun majalisar dokokin jihar Kano da kuma na majalisar wakilai ta tarayya.
An kuma ce shugabannin jam’iyyar sun yi alƙawarin samar da isasshen tallafin kuɗi domin gudanar da yaƙin neman zaɓe idan har Gawuna ya amince ya shiga takarar gwamna a ƙarƙashin ADC.

Kara karanta wannan
Hashim: Dan takarar shugaban ƙasa ya faɗi yadda zai raguzo da farashin Dala idan ya ci zabe
ADC na yunƙurin faɗaɗa tasirinta a Kano
Wannan ci gaban na zuwa ne yayin da ADC ke ƙoƙarin ƙara faɗaɗa tasirinta a fagen siyasar Najeriya tare da jawo fitattun ‘yan siyasa daga manyan jam’iyyu zuwa cikinta.
Har yanzu dai babu wata sanarwa a hukumance daga Gawuna ko na kusa da shi da ke tabbatar da ko ya amince da tayin da ake zargin jam’iyyar ta yi masa.
Sai dai masu sa ido kan harkokin siyasa na ganin cewa duk wani mataki da Gawuna zai ɗauka nan gaba zai iya yin tasiri sosai a siyasar jihar Kano, musamman yayin da ake shirye-shiryen tunkarar zaɓen 2027.
Gawuna ya bi Kwankwaso zuwa NDC
A baya, mun wallafa cewa tsohon mataimakin gwamnan Kano, Nasiru Gawuna, ya sanar da sauya sheka daga jam'iyyar hadakar yan adawa ta ADC.
Nasiru Yusuf Gawuna ya sauya sheka ne kwanaki kadan bayan Sanata Rabiu Musa Kwakwaso ya fice daga hadakar 'yan adawa saboda wasu dalilai.
Ya danganta ficewarsa da rikice-rikicen cikin gida da shari’o’i da suka dabaibaye jam’iyyar yayin da ya fice domin neman mafita tare da Rabi'u Musa Kwankwaso.
Asali: Legit.ng