Sanatan Katsina Ya Fusata, Ya Soki Sharadin Yi Wa Natasha Afuwa
- Sanata mai wakiltar Kudancin Katsina, Dandutse Mohammed Muntari, ya nuna rashin jin daɗinsa kan shawarar yi wa Natasha Akpoti-Uduaghan afuwa
- A jiya ne aka dakatar da Sanata Natasha daga majalisa bisa zargin rashin da’a a zauren majalisa, bayan amincewar sanatoci ta hanyar kada kuri’ar murya
- An bayyana cewa za a iya yi wa Sanatar afuwa ta hanyar rage wa ko janye dakatarwar da aka yi mata matukar ta cika sharadi da aka gindaya mata
- Sanata Muntari Dandutse ya ce, duk da an roke ta, Natasha ta ci gaba da kai ƙorafi kotu da bayyana zargin da ta ke yi wa Shugaban majalisar dattawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja — Sanata mai wakiltar Kudancin Katsina, Dandutse Mohammed Muntari, ya bayyana rashin jin daɗinsa kan shawarar da aka bayar na dage dakatarwar Natasha Akpoti-Uduaghan .
An bayyana cewa za a iya dage dakatarwar da aka yi wa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan idan har ta rubuta takardar neman afuwa ga majalisar.

Asali: Facebook
Jaridar The Nation ta wallafa cewa jiya ne aka dakatar da Natasha daga majalisa na tsawon watanni shida bisa zargin rashin da’a a zauren majalisa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilin dakatar da Sanata Natasha Akpoti
Jaridar Punch ta ruwaito cewa an dakatar da Natasha bayan ‘yan majalisa sun amince da rahoton kwamitin ladabtarwa, sannan suka kada kuri’ar kan hakan.
Amma an kafa sharadin cewa za a iya soke dakatarwar da aka yi mata, matukar ta gaggauta neman yafiyar majalisar a rubuce.

Asali: Facebook
Da yake mayar da martani kan wannan shawara, Sanata Dandutse ya ce Sanata Natasha ta bata sunan fitattun 'yan majalisar dattawa duk da roƙon da abokan aikinta suka yi mata.
Natasha ta fusata Sanata Dandutse
Dandutse ya bayyana cewa, wannan batu yana da matuƙar muhimmanci kuma yana bukatar mu dubi lamarin da nutuswar da ta dace.
Ya ci gaba da cewa:
“Idan muka dubi irin yadda jama’a ke muhawara a kan wannan batu mai muhimmanci, da kuma irin tunani na son zuciya da wasu ke da shi kan lamarin, abin takaici ne yadda Sanata Natasha, duk da roƙon da fitattun Sanatoci daga jiharta suka yi mata, ta ci gaba da garzayawa kotu da kuma bayyana matsayinta a idon duniya."
“Ina ganin idan ba za mu tabbatar da dokokinmu da ke cikin kundin tsarin mulki ba, ina roƙon wannan majalisa da ta cire shawarar da ke cewa za a iya dage dakatarwar ko rage wa’adin hukuncin Sanata Natasha idan ta ba da hakuri."
Natasha: Mata sun fusata da matakin majalisa
Wasu mata a Kano sun bayyana rashin jin dadin yadda majalisa ta hade kai wajen hukunta ƴar.majalisar Kogi,Natasha Akpoti Uduaghan.
Wata Halima ta ce:
"Bai kamata kawai a dakatar da ita babu bincike ba. Sai a duba kokenta, a yi bincike kafin a ɗauki mataki."
Hafsa ta ce:
"Ko ƙarya ta ke yi, sai a duba ai, amma duk sun haɗe mata kai."
Wasu matan da suka nemi a sakaye sunayensu, sun ce irin wannan hali da aka nuna a majalisar ƙara daƙile muryoyin mata ne.
Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta tafi kotu
A baya, kun ji cewa Sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, ta bayyana aniyarta ta kalubalantar hukuncin dakatar da ita na tsawon watanni shida.
An dauki wannan mataki ne bayan musayar yawu da ta yi da Shugaban Majalisa, Sanata Godswill Akpabio, kan yadda aka tsara zaman majalisar, lamarin da ya kai ga dakatar da ita.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng