Rabuwar Kai a Majalisa, Sanatoci 13 ba Su Sa Hannu a Dakatar da Natasha ba

Rabuwar Kai a Majalisa, Sanatoci 13 ba Su Sa Hannu a Dakatar da Natasha ba

  • Dakatar da Sanatar Kogi na neman raba kawunan ƴan Majalisar Dattawa musamman yadda aka ɗauki matakin cikin gaggawa
  • Wata majiya daga Majalisar ta ce akwai wasu manyan sanatoci 13 da suka jima a Majalisa da ba su hannu a kan wannan mataki ba
  • Majalisar dattawa ta dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan na tsawon watanni shida tare da janye mata jami'an tsaro

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Alamu sun nuna cewa akwai rarrabuwar kai tsakanin sanatoci kan dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan (PDP, Kogi ta Tsakiya) na tsawon watanni shida.

Wasu sanatoci sun nuna damuwa kan yadda kwamitin ladabtarwa da ɗabi’a ƙarƙashin jagorancin Sanata Neda Imaseun (LP, Edo ta Kudu), ya gaggauta yanke hukunci kan lamarin.

Majalisar Dattawa.
An fara samun rabuwar kai a Majalisar Dattawa kan dakatar da Natasha Hoto: Nigeria Senate
Asali: Facebook

Rahotan Vanguard ya bayyana cewa sanatoci da dama musamman manyan da suka jima a majalisa, ba su halarci zaman da aka yi na dakatar da Natasha ba.

Kara karanta wannan

Daga ƙarshe, Sanatocin PDP sun ziyarci Natasha, sun yi mata babban alkawari

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matsala ta kunno kai a Majalisar dattawa

Da yawan sanatocin da ba su halarta ba suna wurin taron gyaran haraji da kwamitin kuɗi na majalisa ya shirya. Duk da haka, sai ga shi an hanzarta ɗaukar mataki.

Wani babban sanata da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa an tsara zaman kan batun Natasha a ranar Talata, 11 ga Maris, amma ba zato ba tsammani sai aka canza lokaci.

"An yi wannan abu cikin gaggawa. Me ya sa? Me yasa ba su jira ba? Rashin halartar manyan sanatoci a zaman ya nuna mana inda aka dosa,” in ji shi.

Natasha: Sanatoci 13 ba su sa hannu ba

Sanatan ya kuma ƙalubalanci shugabannnin Majalisa kan dalilin da ya sa aka ci gaba da binciken duk da umarnin kotu na dakatar da lamarin.

"Mu ‘yan majalisa ne, dole ne mu bi tsarin doka. Wannan dalili ne ya sa sanatoci 13 suka ƙi halarta ko sanya hannu a rahoton."

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta tsoma baki kan zargin shugaban Majalisa da neman matar aure

Majalisar Dattawa ta dakatar da Akpoti-Uduaghan a ranar Alhamis, tana mai zargin ta da karya dokokin majalisa na 2023.

Abin da ya jawo dakatar da Natasha

Dakatarwar ta biyo bayan rigimar da ta yi da Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, a ranar 20 ga Fabrairu kan tsarin wurin zsma.

Majalisar ta zargi Sanata Natasha da batawa Shugaban majalisa da zauren majalisar suna a bainar jama’a.

Matsayar wasu Sanatoci a majalisa

Rahoton kwamitin ladabtarwa ya kuma bayar da shawarar a dakatar da albashin dukkan ma’aikatan ofishinta.

Amma Sanata Orji Uzor Kalu (APC, Abia ta Arewa), da Sanata Ned Nwoko (APC, Delta ta Arewa) sun nemi a ci gaba da biyan hadiman Sanata Natasha haƙƙoƙinsu.

Duk da haka, Majalisar ta bayyana cewa za a iya sake duba hukuncin idan har ta rubuta wasiƙar neman afuwa.

Sai dai bayanai sun nuna wannan dakatarwa ta raba kawunan sanatoci, musamnan waɗanda ba su halarci zaman da aka yi kan lamarin ba balle su sa hannu.

Kara karanta wannan

Sanatan Katsina ya fusata, ya soki sharadin yi wa Natasha afuwa

Sanatocin PDP sun ziyarci Natasha

A wani rahoton, kun ji cewa wasu daga cikin sanatocin PDP sun ziyarci dakatacciyar sanatar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti.

Yayin ziyarar, ƴan Majalisar sun jaddada cewa za su yi duk mai yiwuwa wajen ganin an ɗage dakatarwar da aka yi wa abokiyar aikinsu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng