Tsugunne ba Ta Kare ba: Sabuwar Matsala Ta Tunkaro Akpabio kan dakatar da Natasha
- Ƙungiyar SERAP ta nuna rashin amincewarta da dakatarwar da majalisar dattawa ta yi wa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan
- SERAP ta buƙaci shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio da ya gaggauta janye dakatarwar da aka yi wa Natasha
- Ƙungiyar ta bayyana cewa dakatarwar a matsayin wacce ba ta dace ba kuma take haƙƙin ƴancin faɗin albarkacin baki ce
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Ƙungiyar SERAP ta buƙaci shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, da ya gaggauta janye dakatarwar da aka yi wa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan.
Ƙungiyar SERAP ta bayyana dakatarwar a matsayin wacce ba bisa ƙa’ida ba kuma take haƙƙin ta ne na ƴancin faɗar albarkacin baki.

Asali: Facebook
Hakan na ƙunshe ne a cikin sanarwa da ƙungiyar ta fitar a shafinta na yanar gizo serapnigeria.org.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majalisa ta dakatar da Sanata Natasha
An dakatar da Natasha na tsawon watanni shida a makon da ya gabata bayan an zarge ta da cewa ta yi magana ba tare da izini ba, kuma ta ƙi komawa sabon wurin zamanta a zauren majalisar.
Har ila yau, an dakatar da albashinta da sauran haƙƙoƙinta na kuɗaɗe har tsawon lokacin dakatarwar, kuma an hana ta gabatar da kanta a matsayin sanata.
SERAP ta gargaɗi Akpabio
A cikin sanarwar da SERAP ta fitar, wacce Kolawole Oluwadare, ya sanyawa hannu, ƙungiyar ta yi gargaɗin cewa za ta ɗauki matakin shari’a idan shugaban majalisar dattawa ya gaza janye dakatarwar cikin sa’o’i 48.
Sanarwar ta jaddada cewa babu wanda ya kamata a hukunta shi saboda yin magana ba tare da izini ba.
SERAP ta yi iƙirarin cewa dakatarwar ta take haƙƙin Natasha Akpoti-Uduaghan na ƴancin faɗin albarkacin baki, wanda doka ta amince da shi a kundin tsarin mulkin Najeriya da kuma yarjejeniyoyin ƙasa da ƙasa.
Ƙungiyar ta yi nuni da sashe na 39 na kundin tsarin mulkin Najeriya da kuma sashe na 9 na kundin kare haƙƙoƙin ɗan Adam na Afirka, inda ta ce matakin da majalisar dattawa ta ɗauka ba bisa ƙa’ida ba ne kuma ya saɓa doka.
"Ya kamata majalisar dattawa ta zama abin koyi wajen kiyaye doka da kare haƙƙin ɗan Adam, ba wai take shi ba."
- Kolawole Oluwadare
SERAP ta soki majalisar dattawa
Haka kuma, ƙungiyar ta soki majalisar dattawa saboda tauye haƙƙin al’ummar mazaɓar Sanatan Kogi ta Tsakiya wajen samun ingantaccen wakilci.
SERAP ta buƙaci majalisar dattawa da ta mayar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan kan mukaminta sannan ta sake duba dokokinta don hana tauye ƴancin faɗin albarkacin baki.
Kungiyar ta gargadi cewa rashin daukar matakin da ya dace cikin lokacin da ta ba da, zai sa ta ɗauki matakin shari’a don kare haƙƙin sanatar.
Majalisa ta faɗi dalilin dakatar da Natasha
A wani labarin kuma, kun ji cewa majalisar dattawa ta kare kanta kan dakatarwar da ta yi wa Sanata Nataha Akpoti-Uduaghan.
Shugaban masu rinjaye na majalisar, Sanata Opeyemi Bamidele ya bayyana cewa ba saboda zargin cin zarafi ba ne aka dakatar da Natasha.
Ya nuna cewa an dakatar da Sanata Natasha ne saboda saɓa wasu daga cikin dokokin majalisar da ta yi.
Asali: Legit.ng