Malamin Izala Ya Hango Fitina a Kashe Sheikh Yahaya Masussuka da Aka Yi
- Yahaya Muhammad Assalafy bai goyi bayan kashe Yahaya Ibrahim Masussuka da aka yi a garin Dutsinma ba
- Malamin da yake karatu a Kaduna, ya gargadi wadanda suke farin ciki da mutuwar malamin na Kur'ani zallah
- Assalafy ya ce bai yi na’am da da’awar takwaran na shi ba, amma kashe shi zai bude kofar fitina ne a ban kasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Kaduna - Malamin addinin Musulunci a Kaduna, Yahaya Muhammad Assalafy ya yi tsokaci kan rasuwar Yahaya Ibrahim Masussuka.
Yahaya Muhammad Assalafy ya yi magana washegarin da abin ya faru, inda ‘yan ta’addan Ansaru suka harbe malamin a jihar Katsina.

Source: Facebook
Kisan Masussuka: Tsokacin Sheikh Yahaya Assalafy
Legit Hausa ta samu nasihar da malamin ya yi ne a shafin Muhammad Kabir Yahaya a kafar Facebook ranar 28 ga watan Oktoba 2026.
Sheikh Yahaya Muhammad Assalafy ya fara da yin tir da cewa wasu daidaikun mutane ne kurum suka ga bayan malamin, ba hukuma ba.
Malamin addinin ya ce idan ana zargin wani da laifi, ba hakkin wasu tsirarrun mutane ba ne su dauki doko a hannu da sunan hukunci.
Haramcin mutum ya dauki doka a hannu
Malamin ya ce bai halatta wasu mutane su ce za su tsaida hukunci a kan wadanda suka aikata laifi.
“Haramun ne mai girman gaske idan ka ga mutum yana da wata akida sabanin naka, kai kana ganin ya yi ridda, sai ka ce tunda ya yi ridda, ai Allah ya ce ‘duk wanda ya canza addini, ku kashe shi!’, to bari in kashe shi
"Shi ma yana ganin kai ka ma ka canza addini. Yadda ka ke ganin shi kafiri, haka yake ganinka kafiri. Wanda za ta raba gardama ita ce hukuma."
- Yahaya Muhammad Assalafy
Malamin ya yi kashedi kan bude kofar kashe-kashe
Muddin aka bar kofar a bude, Yahaya Muhammad Assalafy ya yi gargadi cewa masu mabambantan ra’ayi za su yi ta kashe junansu.
Ya bada misali da Sheikh Lawal Shua’ibu Abubakar (Triumph), yake cewa a wurin ‘yan darika, malamin na Izala ya yi ridda tuni.
Yanzu da ake shari’a a kotu, ya ce alkalin ‘dan darika ne amma babu ta yadda zai kama malamin da laifi sai dai ya bi tsarin alkalanci.
Kisan Yahaya Masussuka ba abin murna ba ne
Game da lamarin kisan Yahaya Ibrahim Masussuka, shehin ya ce ba abin da jama’a za su rika murna ba ne, abin tada hankali ne.
"Abin da ya faru jiyan nan, ba abu ne da ya kamata Ahlul Sunnah su rika murna, suna farin ciki ba
"Abu ne wanda ya kamata hankalin mu ya tashi. Saboda duk abin da zai bude kofa ta barna, ya kamata mu yi addu’a ka da Allah ya kawo shi."
- Yahaya Muhammad Assalafy
Yahaya Assalafy yake cewa a tarihin Musulunci, daga kashe Sayyidina Umar da Usman aka daga takobin da ba zai taba komawa ba.
Malamin ya yi wannan bayani ne ganin wasu cikin almajiransu sun kira shi a waya, suna nuna murnarsu da kashe Masussuka.
Yadda ya kamata a bullowa irinsu Masussuka
Idan ana zargin wani malami ya kauce hanya, malamin ya ce abin da za su yi shi ne su kai kara wajen gwamnati ta hada mukabala.
Bayan an yi zama an iya kai wani bango, sai gwamnati ta shigar da kara a kotu, yake cewa haka aka yi wa Sheikh Abduljabbar Kabara.
Ya yi gargadi cewa bin hanyar makami a kashe malami saboda ana ganin ya saba wa tafarki, bai cikin koyarwar magaba a Musulunci.
Sheikh Assalafy ya ce duk da sukar kisan, ba su goyon bayan akidar Yahaya Masussuka amma bai ga maslaha a daukar makami ba.
Abin da ya bada shawarar a maida hankali a kai shi ne yi wa juna raddi na ilmi domin babu wanda ya san karshen fitina idan ta tashi.
Za a yi wa Yahaya Masussuka jana'iza
Sabanin yadda wasu suka yi tunani, an ji labari cewa masoya da almajirai za su yi wa Yahaya Ibrahim Masussuka sallar jana'iza.
Bayan an yi masa sallah a fadar Sarkin Katsina kuma an birne shi a makwancinsa, almajiran malamin sun shaida cewa za a yi masa addu'a.
Wasu sun yi tunanin cewa ba za a yi wadannan abubuwa ba ne kasancewar malamin ya mutu ne a tafarkin bin littafin Al-Kur'ani zallah.
Asali: Legit.ng



