'Yan Bindiga Sun Kai Wa Tinubu Hari Yana cikin Jawabi a Wurin Taro? An Samu Bayani
A ranar 5 ga Nuwamba, 2026, wani mai amfani da kafr sada zumunta ya wallafa wani bidiyo na Shugaba Bola Tinubu, yana zargin cewa bidiyon ya nuna wani yunƙurin kai wa shugaban ƙasar hari da ’yan bindiga suka yi.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
A cikin bidiyon, wani mutum ya bayyana a gefe guna, tare da yin bayanin abin da yake zargin shi ne ya faru da Shugaba Tinubu.

Source: Facebook
An wallafa bidiyon a shafin Bro Smiling Comedy na Facebook, lamarin da ya ja hankalin mutane da dama, inda suka nuna ba su yarda ba.
Wanda ya yi bayani a jikin bidiyon ya ce:
“Da sun cire kan shugaban ƙasarku. Waɗannan ’yan bindiga sun so kai masa hari. Da ba don kasancewarsa shugaban ƙasa ba, da an kai masa hari. Ku kalli bidiyon kawai.”
Faifan bidiyon da aka ɗora a saman ya nuna shugaban ƙasar a tsaye a gaban makirufo. Ya firgita kaɗan lokacin da wani mutum da ke gefensa ya ruga da gudu, sannan wasu mutane biyu sanye da kayan soji suka matsa kusa da shi domin kare shi.
An rubuta a jikin bidiyon cewa, “’Yan bindiga sun kai wa shugaban ƙasa hari a yau.”
Martanin mutane kan bidiyon
A martaninsa kan wallafar, @Jude Ebere ya rubuta cewa: “Shugaban ƙasarmu ba shi da laifi, amma mutanen da ke tare da shi su ne miyagun mutane. Ina masa fatan tsawon rai.”
@Ayo Sunday ya yi sharhi da cewa:
“Ba za su iya ba. Saboda barazanar da suka yi wa shugaban ƙasa, ya kamata a rusa wannan yanki gaba ɗaya. Ba ku kai wa Gumi hari ba; ba ku kai wa Sarkin Musulmi hari ba. Ku gwada yanzu ku gani…”
Tabbatar da gaskiyar bidiyon
Jaridar DUBAWA ta lura cewa bidiyon shugaban ƙasar yana ɗauke da tambarin TVC News, abin da ke nuna cewa hotunan sun fito ne daga shirin gidan talabijin.
Daga nan, ta gano asalin bidiyon a wani shirin kai tsaye na TVC News da aka wallafa a YouTube mai taken “Pres. Tinubu Inaugurates CNG Mass Transit Buses at Murtala Square.”

Kara karanta wannan
An ba 'yar Amurka Dala miliyan 4.5 bayan ta yi hira da Shugaba Tinubu? Gaskiya ta bayyana
An wallafa bidiyon ne a ranar 19 ga Yuni, 2025, kuma ya nuna irin wannan yanayin da ke cikin bidiyon da ya yaɗu, inda shugaban ƙasar ya dakata yayin da jami’an tsaro suka matsa kusa da shi.
Binciken ya kai ga wani rahoto da jaridar The Cable ta wallafa, wanda ya ƙunshi bidiyon wannan lamari.
Rahoton da aka wallafa a ranar 19 ga Yuni, 2025, ya bayyana cewa Tinubu yana Kaduna ne domin ƙaddamar da wasu ayyukan da gwamnatin Gwamna Uba Sani ta gudanar, lokacin da wani mutumi ya matso kusa da shi, hakan ya sa ya dakata da jawabinsa.
Rahoton ya ce jami’an tsaronsa sun hana mutumin ci gaba da matsowa, sannan shugaban ƙasar ya umarce su da su “kyale shi”. Rahoton bai ambaci ’yan bindiga ko wani yunƙurin kai hari ba.
A cikin wata sanarwa da rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna ta fitar a ranar Juma’a, 20 ga Yuni, 2025, ta bayyana cewa sunan mutumin Umar Mohammed ne, mazaunin Anguwan Muazu da ke Ƙaramar Hukumar Kaduna ta Kudu.
A cewar rahoton, Umar, swanda aka ce yana da ɗan tabin jankali, na cikin magoya bayan da aka ba su damar shiga wurin taron Murtala Square.

Kara karanta wannan
Fashola ya fito da bayanin da ya kamata mutane su sani kan yanayin lafiyar Tinubu
’Yan sandan sun ce mutumin ya ketare shingen tsaro ne domin ya kusanci shugaban ƙasa saboda tsananin sha’awa da farin ciki. Jami’an tsaro sun tare shi tare da kama shi nan take.
Binciken da aka yi masa bai gano wani makami ko wani abu mai haɗari a tare da shi ba. Rundunar ’yan sandan ta bayyana matakin nasa a matsayin sakamakon tsananin farin ciki, ba wai wata muguwar manufa ba.
Hukuncin karshe kan bidiyon
Bidiyon ya haura shekara ɗaya, kuma ba shi da alaƙa da ’yan bindiga. An ɗauke shi ne a wani taro da aka gudanar a Kaduna a ranar 19 ga Yuni, 2025.
Saboda haka, ikirarin cewa bidiyon ya nuna yunƙurin kai wa Shugaba Bola Tinubu hari da ’yan bindiga suka yi ƙarya ne.
Kun ji cewa
Asali: Legit.ng
