Dan Uwan Sheikh Yahaya Masussuka Ya Fadi yadda Yan Bindiga Suka Kashe Shi

Dan Uwan Sheikh Yahaya Masussuka Ya Fadi yadda Yan Bindiga Suka Kashe Shi

  • Wani da ya ce shi dan uwan Sheikh Yahaya Ibrahim Masussuka ne, ya bayyana yadda wasu ’yan bindiga suka kashe malamin a Katsina
  • Zaradden Surajo ya ce maharan sun bude wa malamin da wani da yake tare da shi wuta ne yayin da suke shirye-shiryen babban taro
  • Ya bayyana cewa maharan sun tsere a kan babura bayan harin, yayin da masoyan malamin suka taru a gidansa cikin jimami da fargaba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Dutsinma, Katsina - Wani da ya ce shi dan uwan Sheikh Yahaya Ibrahim Masussuka ne ya fadi yadda aka kashe shi.

Zaradden Surajo Abbas ya ce yana da kusanci da shi malam saboda shirin wani babban taro na kasa da suke shiryawa.

Yadda aka kashe Sheikh Masussuka
Marigayi Sheikh Yahaya Ibrahim Masussuka da aka hallaka a Katsina. Hoto: Sheikh Yahaya Ibrahim Masussuka.
Source: Facebook

Wakilin Legit Hausa ya bibiyo wani sakon murya da aka ji ana hira da Zaradden wanda aka wallafa a shafin Labarai 24 a Facebook.

Kara karanta wannan

Atiku ko Tinubu: Malamai 1100 sun tsaida ‘dan takaran shugaban kasarsu a Katsina

An kashe Malam Yahaya Masussuka

Mutumin ya nuna damuwa kan yadda mutanen dauke da bindiga suka bude wa Masussuka wuta tare da wani da suke tare da shi.

Ya bayyana cewa lamarin ya faru ne yayin da suke shirye-shiryen gudanar da wani babban taro na kasa da malamin zai jagoranta.

Ya ce:

"Muna shirye-shiryen babban taro, kawai ba a wuce minti 30 zuwa 40 wasu da ba a san ko su waye ba suka bude masa wuta, aka garzaya da su asibiti ko kuma kafin aje ma Allah ya masu rasuwa su duka.
"Lamarin ya faru a Dutsinma inda can ne inda gidansa ya ke, yanzu halin da ake ciki, muna ta kokarin waya da dalibai da ke can mu ci halin da ake ciki.
"Na kira Dakta Muhammad Haruna wani da ke kusa da malam, ya tabbatar da rasuwar malam inda ya ce suna kokarin daukar gawar malam zuwa gida."

Kara karanta wannan

Sheikh Pakistan ya faɗi aikin Tinubu a Kano da ya cancanci a zaɓe shi a 2027

An kashe Malam Masussuka a Katsina
Taswirar jihar Katsina da aka hallaka Sheikh Yahaya Ibrahim Masussuka. Hoto: Legit.
Source: Original

Yadda maharan suka tsere bayan kashe Masussuka

Zaradden ya ce mutane sun taru a gidan malam cikin jimami wanda ke nuna cewa akwai damuwa sosai da fargaba a tsakanin masoyan marigayin.

Ya tabbatar da cewa wadanda suka yi ajalin malam sun lallabe ne kafin yin harbin wanda ya yi sanadiyyar malamin kafin su hau babura su tsere.

"Amma mutane sun taru akwai hayaniya sosai a wurin, amma zuwa lokacin da muke magana babu wani abu daga jami'an tsaro.
"Lallai an ce wadanda suka yi harbin sun yi harbin ne a lallabe yayin suka hau babura suka tsere bayan sun harbin."

- Cewar Zaradden

Kisan Masussuka: Gwamnatin Katsina ta magantu

Mun ba ku labarin cewa gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya yi jimamin kisan malamin addinin Musulunci, Sheikh Yahaya Masussuka, wanda wasu ’yan bindiga suka kashe a Dutsin-Ma.

Radda ya bayyana marigayin a matsayin malamin da ya yi fice wajen wa’azin zaman lafiya, zaman tare tsakanin mabiya addinai musamman a Arewacin Najeriya.

Gwamnan ya yi alƙawarin gudanar da cikakken bincike kan kisan, tare da kira ga mazauna jihar da su kwantar da hankalinsu su kuma bai wa jami’an tsaro haɗin kai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.