Mutumin da Ya Maido Sheikh Masussuka Katsina Ya Fito da Maganganu Bayan Rasuwa
- Bello Danwaire yana cikin bakin ciki maras misaltuwa a dalilin rasuwar Sheikh Yahaya Ibrahim Masussuka
- Abokin karatun malamin ya yaba da kokarinsa na neman ilmi da hada kan jama’a daga kowane addini
- Taron da aka shirya kuwa babu fashi domin Danwaire ya ce Masussuka ya gama shiri kafin ya bar duniya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Katsina - Malam Bello Danwaire yana cikin abokan karatu kuma wanda yake da kusanci da Yahaya Ibrahim Masussuka.
Bello Danwaire ya bayyana cewa shi ne ya yi sanadin dawowar Yahaya Ibrahim Masussuka gida bayan sun yi karatu.

Source: Facebook
Alakar Bello Daniware da Yahaya Ibrahim Masussuka
Da JBC Hausa ta yi hira da Bello Danwaire, ya bayyana marigayin a matsayin abokinsa kuma malaminsa na addinin Islama.
Danwaire ya ce tun kafin marigayi Yahaya Ibrahim Masussuka ya dawo Katsina, shi ya zauna a gidansu na tsawon shekaru biyu.
Sun yi karatu tare da shi kuma daga baya ya yi sanadiyyar dawowar malamin garin Dutsinma ya zauna ya cigaba da karantarwa.
Me ya kawo Yahaya Ibrahim Masussuka jihar Katsina?
Yake cewa malamin ya zabi Dutsinma ne ganin yadda garin yake da wadanda suka yarda da Kur’ani wato ‘yan Kur’ani zallah.
Kamar yadda Malam Danwaire ya shaida, Yahaya Ibrahim Masussuka ya bi tafarkoki dabam-dabam kafin ya yi riko da Kur’ani.
Malam Danwaire ya ce bayan tarayyarsu a garin Masussuka a karamar hukumar Ningi a Bauchi, sai suka dawo Katsina.
Abokin malamin ya fada wa ‘yan jarida cewa a shekarar 1988 suka zo garin Dutsinma. Dama can nan ne asalin iyayensa.
Aminin Sheikh Masussuka yana cikin takaici
Da aka tambaye shi halin da yake ciki, sai ya ce bai taba samun kan shi a yanayi na bakin ciki a rayuwa irin na yanzu ba.
“Kai, wannan abin…ban iya misalta shi saboda ban taba shiga wani bala’i irin wannan ba.
Saboda shi malam uba ne kuma ga kowa domin idan kana tare da shi za ka koyi darasi na rayuwa.

Kara karanta wannan
An sanar da shirye shiryen jana'izar Sheikh Yahaya Masussuka a Fadar Sarkin Katsina
- Bello Danwaire
Danwaire ya kuma jero wasu abubuwan da ya koya a zamansa da Masussuka wanda ‘yan ta’adda suka bindige shi a gidansa.
Bello Danwaire ya ce:
"Za ka koyi ta-ka-tsan-tsan, za ka koyi mutunta al’umma, sannan za ka koyi mike wa bangaren jihadi na addini"
Abubuwan karshe da marigayin ya yi a rayuwarsa
Ana gobe za a harbe malamin, Danwaire suna tare da shi wajen ganin yadda za a hada-kan al’umma ba tare da lura da addini ba.
Game da taro kuwa, almajirin malamin na Kur’ani zallah ya bayyana cewa tuni an riga an kammala duk abin da ya dace a tanada.
Abubuwan karshe da ya yi kafin ya cika sun hada da jana’izar surukinsa da ziyartar wani Malam Abdulhadi da bai da lafiya.
Ya ce maras lafiyan ya rungume marigayin, ganawar da ba za su kara yi ba kenan a gidan duniya.
Yake cewa mutuwarsa ta ba su kwarin guiwa domin Masussuka ua mutu a wajen daga addini da rike tafarkin Kur’ani mai girma.
Ya ce irin mutuwar da suke so kenan, yana mai takaicin rasa amininsa wanda ya rayuwa da kowane mutum a matsayin na shi.
Jana'izar Yahaya Masussuka sai ranar Juma'a
Sai ranar Juma'ar nan 30 ga watan Oktoba 2026 aka ji cewa za a birne Yahaya Ibrahim Masussuka a fadar sarkin Katsina.
Wani malami da yake tare da shi, Imam Rashid ya ce za a yi jana'izar shehin bayan an kammala sallar Juma'a a ranar.
An ji dalilai biyu da suka jawo daga sallar sai ‘yan kwanaki bayan an bindige malamin addinin da ya shahara a duniya.
Asali: Legit.ng

