Masussuka: Shehu Sani Ya Faɗi 'Dalilai' da Ke Jawo Kisan Malamai a Arewa

Masussuka: Shehu Sani Ya Faɗi 'Dalilai' da Ke Jawo Kisan Malamai a Arewa

  • Tsohon Sanata Shehu Sani ya bayyana dalilai uku da yake ganin suka jawo kashe fitattun malaman addini a Arewacin Najeriya cikin shekaru 15
  • Shehu Sani ya ce malaman sun yi fice wajen yin Allah-wadai da tsattsauran ra’ayi, inganta zaman lafiya da kuma jure wa bambancin addinai
  • Tsohon sanatan ya bayyana cewa ‘yan ta’adda suna son a yi shiru, yana mai cewa duk wanda ya yi magana kan ta’addanci na iya fuskantar barazana

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kaduna - Tsohon ɗan majalisar dattawa, wanda ya wakilci mazabar Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani ya yi magana kan kisan malamai a Arewa.

Shehu Sani ya bayyana dalilan da suka sa ake kashe fitattun malaman addini a Arewacin Najeriya.

Shehu Sani ya magantu kan kisan malamai a Arewa
Tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani. Hoto: Shehu Sani.
Source: Facebook

Hakan na cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X da aka tantance a ranar Talata 27 ga watan Oktobar 2026.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun kama ɗan agajin Izala kan zargin barazana ga Kiristoci a bidiyo

Ansaru ta dauki alhakin kisan Masussuka

Ƙungiyar Ansaru mai alaƙa da Al-Qaeda ta ɗauki alhakin kashe Malam Yahaya Masussuka, wanda aka harbe har lahira a Dutsin-Ma ta jihar Katsina a ranar Litinin.

A cikin wani saƙon murya, ƙungiyar ta zargi malamin da kafirci da adawa da Musulunci, amma ba ta bayyana wani takamaiman laifi da ya aikata ba.

Malam Yahaya Masussuka ya dauki hankalin jama'a sosai a Najeriya, yayin da hukumomin tsaro ke fuskantar kira na gano waɗanda suka aikata kisan.

Shehu Sani ya magantu kan kisan malaman Arewa

Sanata Sani ya ce duk fitattun malaman addinin da aka kashe a Arewa cikin shekaru 15 da suka gabata suna da abubuwa uku da suka yi tarayya a kai, waɗanda babu shakka suka jawo kashe su.

Ya lissafa abubuwan uku da suka haɗa da yin magana kan illolin tsattsauran ra’ayi, kira ga jituwa da zaman lafiya tsakanin mabiya addinai daban-daban, da kuma ambaton sunayen shugabannin ‘yan ta’adda ko ƙungiyoyin ta’addanci a wa’azozinsu.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya yi magana kan kisan gilla da aka yi wa Sheikh Masussuka a Katsina

A cewarsa, a shekarar 2011, tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo tare da shi sun je Maiduguri a ɓoye domin fara tattaunawar samar da zaman lafiya.

Ya ce bayan kammala taron, sun dawo Abuja, amma washegari aka kashe mutumin da ya taimaka wajen shirya tattaunawar, sannan suka fara samun barazanar rayuwarsu.

Shehu Sani ya ce:

“Duk fitattun malaman addinin da aka kashe a Arewacin Najeriya cikin shekaru 15 da suka gabata, an kashe su ne saboda yin magana kan ta’addanci, kiran a zauna lafiya da kuma ambaton shugabannin yan ta'adda

“‘Yan ta’addan suna son mutane su yi shiru, idan ba haka ba, za su tilasta musu yin shiru.”

Sheikh Gumi ya magantu kan kisan Masussuka

Mun ba ku labarin cewa Sheikh Ahmad Abubakar Gumi ya bayyana kisan Sheikh Yahaya Ibrahim Masussuka a matsayin babban kuskure da ka iya jawo fitina a cikin al’umma.

Malamin ya yi gargaɗin cewa akwai yiwuwar maƙiyan Musulunci su yi amfani da lamarin wajen haifar da ruɗani.

Gumi ya yi kira ga jama’a da su kwantar da hankalinsu, su bar hukuma ta ɗauki matakin da ya dace domin tabbatar da adalci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.