APC Ta Bayyana Gaskiyar da Ta Yarda da Ita Kan Matsalar Rashin Tsaro a Gwamnatin Tinubu
- Sakataren yaɗa labaran APC, Felix Morka, ya ce an samu raguwar hare-haren rashin tsaro da asarar rayuka a Najeriya cikin shekarar da ta gabata
- Morka ya danganta ci gaban da ƙarin albashin sojoji, inganta walwalarsu da ƙara yawan rundunonin sojojin ƙasar
- Ya amince cewa har yanzu Najeriya na fuskantar matsalolin tsaro, amma ya ce matakan gwamnati sun sa wasu ’yan ta’adda da ’yan bindiga miƙa wuya ga sojoji
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Jam’iyyar APC ta yi magana kan ci gaba da aka samu ta fannin tsaro a karkashin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Jam'iyyar APC ta bayyana cewa an samu ci gaba a fannin tsaro a Najeriya tun bayan hawan Shugaba Tinubu mulki a shekarar 2023.

Source: Facebook
Sakataren yaɗa labaran jam’iyyar na ƙasa, Felix Morka, ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a shirin The Morning Brief na gidan talabijin na Channels a ranar Laraba, 18 ga watan Nuwamban 2026.
Ya ce daga cikin abubuwan da suka taimaka wajen inganta tsaro akwai ƙarin albashin sojoji da kuma inganta walwalar jami’an da ke gudanar da ayyukan yaƙi da rashin tsaro.
APC ta ce an samu raguwar hare-hare
Morka ya yi iƙirarin cewa cikin shekarar da ta gabata, an samu raguwar hare-haren rashin tsaro da kuma yawan mutanen da ke rasa rayukansu sakamakon matsalolin tsaro.
A kalamansa:
“A cikin shekarar da ta gabata, mun ga ana samun raguwar matsalolin rashin tsaro a kai a kai, ta fuskar yawan hare-hare da kuma asarar rayuka.”
Yayin da yake bayyana nasarorin da ya ce gwamnatin Tinubu ta samu, Morka ya ce sojojin Najeriya sun samu ci gaba a fannoni daban-daban.
Ya lissafa ƙarin albashi, faɗaɗa rundunar sojoji da kuma inganta yanayin aikin jami’an tsaro a matsayin wasu daga cikin matakan da aka ɗauka.
Sakatren yada labaran na APC ya kuma yi nuni da ƙirƙirar ƙarin sassan rundunar sojoji, inganta walwalar sojojin da ke fuskantar haɗari a bakin daga, da kuma samar musu da ingantattun wuraren kwana.
Morka ya yi magana kan garkuwa da ’yan NYSC
Da yake magana kan matsalolin tsaro da suka haɗa da sace wasu ’yan bautar ƙasa (NYSC) da ayyukan ’yan bindiga a Arewacin Najeriya, Morka ya ce matsalar rashin tsaro ba Najeriya kaɗai ta shafa ba.
Ya bayyana cewa babu wata ƙasa a duniya da ba ta fuskantar ƙalubalen tsaro, kuma babu wata gwamnati da ke fatan ganin al’ummarta na cikin rashin tsaro.
Ya ce wasu ’yan ta’adda sun miƙa wuya
Morka ya kuma yi iƙirarin cewa matakan tsaron da gwamnatin Tinubu ta ɗauka sun sa ƙarin ’yan ta’adda da ’yan bindiga miƙa wuya ga jami’an soji.
Ya dage cewa an samu gagarumin ci gaba wajen tabbatar da tsaron ƙasa, duk da cewa har yanzu akwai ƙalubalen da ke buƙatar kulawa.
Sakataren yaɗa labaran APC ya kuma bukaci kafafen yaɗa labarai su riƙa gabatar da rahotannin tsaro cikin daidaito, ba tare da nuna ɓangare ɗaya ba.
Ya ce ya kamata a riƙa bayyana sakamakon ƙoƙarin da Shugaba Tinubu ke yi wajen magance matsalar tsaro a ƙasar.

Kara karanta wannan
Sabon tsarin da Kwankwaso yake so a yi amfani da shi a zaben shugaban kasa a Najeriya

Source: Facebook
Batun lafiyar Shugaba Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa Babatunde Fashola, ya yi watsi da damuwar da ake nunawa kan lafiyar jikin Shugaba Bola Tinubu da kuma ƙarfinsa na tunani.
Fashola ya ce bai ga wani abu da ke nuna cewa shugaban kasar ba zai iya gudanar da ayyukansa yadda ya kamata ba.
Asali: Legit.ng

