EFCC: Yahaya Bello Ya Fusata kan Ce Masa Barawo, Ya Yi Raddi Mai Zafi
- Tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello, ya bayyana mutanen da ke zarginsa da satar kudaden gwamnati a matsayin jahilai
- Bello ya ce dukkan kasafin kudin gwamnatinsa na tsawon shekara takwas da bayanan yadda aka kashe kudin suna nan a intanet
- Yahaya Bello ya kuma bukaci ’yan jarida da masu suka su je Kogi domin tantance ayyukan da gwamnatinsa ta gudanar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya bayyana wadanda ke kiransa barawo kan zargin karkatar da kudin gwamnati a lokacin mulkinsa a matsayin mutanen da blaa su da cikakken sani.
Ya fadi haka ne yayin mayar da martani kan tambayoyi game da zargin da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ke yi masa na karkatar da kudin jihar Kogi.

Source: Facebook
Yahaya Bello, wanda ya mulki jihar daga shekarar 2016 zuwa 2024, ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na Channels a ranar Juma’a.
Yahaya Bello ya ki tsokaci kan EFCC
Da aka tambaye shi yadda yake kallon mutanen da ke zarginsa da satar kudin gwamnati, tsohon gwamnan ya ce ba zai yi magana kai tsaye kan binciken EFCC ba saboda ana shari’a a kotu.
Ya ce:
“Zan fi son in ki yin tsokaci kan EFCC a gidan talabijin na kasa saboda muna gaban kotu.”
Sai dai Bello ya kalubalanci ’yan jarida da sauran masu sukarsa da su duba bayanan kudin gwamnatinsa, tare da ziyartar jihar domin tantance ayyukan da aka gudanar da kuma yadda aka kashe kudaden.
Karin bayani daga Yahaya Bello
Tsohon gwamnan ya bayyana cewa kasafin kudin gwamnatinsa na tsawon shekara takwas, bayanan kudin shiga da kashewa da kuma rahotannin ayyukan da aka gudanar duk suna samuwa a intanet.
Ya ce babu wani dan jarida ko mai suka da ya kamata ya yi hukunci ba tare da ya je jihar Kogi ya yi bincike da kansa ba.
Bello ya bukaci masu son sanin gaskiya da su sauke kasafin kudin da bayanan kudi, su je Kogi, sannan su yi amfani da dokar ‘yancin samun bayanai wajen neman karin bayani.

Source: Twitter
Da aka sake tambayarsa yadda yake ji idan aka kira shi barawo bayan ya shafe shekaru takwas yana mulkin jihar, Bello ya ce yana tausaya wa masu zargin nasa.
Punch ta rahoto ya kara da cewa:
“Zan fi son in tausaya musu saboda jahilai ne.”
A halin yanzu, tsohon gwamnan na fuskantar shari’o’i biyu daban-daban da EFCC ta shigar a kansa kan zargin halasta kudin haram da karkatar da kudin gwamnatin jihar Kogi da kananan hukumominta a lokacin mulkinsa.
Maganar Yahaya Bello kan El-Rufa'i
A wani labarin, mun rahoto cewa tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello, ya ce yana da tabbacin kayar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan a zaben Majalisar Dattawa na 2027.
Bello ya bayyana cewa mutanen yankinsa na bukatar ya wakilce su a Majalisar Dattawa, yana mai cewa farin jininsa ya karu tun bayan barin kujerar gwamnan jihar.
Haka kuma, ya ce da ya samu damar tattaunawa da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, kafin fara shari’o’insa, da ya shawarce shi ya rage magana, ya ci gaba da zama a APC tare da jiran matakin da Shugaba Bola Tinubu zai dauka.
Asali: Legit.ng

