Yadda Sheikh Yahaya Masussuka Ya Yi Maganar Mutuwa ana daf da Harbe Shi

Yadda Sheikh Yahaya Masussuka Ya Yi Maganar Mutuwa ana daf da Harbe Shi

  • Malam Yahaya Masussuka ya yi magana kan mutuwa 'yan sa’o’i kaɗan kafin wasu ’yan bindiga su kashe shi da abokinsa a Katsina
  • Wani mazaunin Dutsin-Ma ya ce malamin ya tunatar da jama’a game da hakuri da bambancin addini, ƙabila da sauransu
  • Mataimakinsa da sauran makusantansa sun buƙaci mabiyansa su kwantar da hankalinsu, su guji kalaman da za su iya haddasa tashin hankali

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Katsina – Sa’o’i kaɗan kafin wasu ’yan bindiga su kashe Sheikh Yahaya Ibrahim Masussuka da abokinsa, Adamu Abubakar, a Dutsin-Ma ta jihar Katsina, malamin ya yi magana kan mutuwa.

Rahotanni sun nuna cewa an kashe malamin da abokinsa ne a harin da aka kai masu a gaban gidansa a yammacin ranar Litinin. Kisan ya jefa iyalansa, mabiyansa da sauran makusantansa cikin alhini.

Kara karanta wannan

An sanar da shirye shiryen jana'izar Sheikh Yahaya Masussuka a Fadar Sarkin Katsina

Malam Yahaya Ibrahim Masussuka
Yahaya Masussuka da aka kashe a Katsina. Hoto: Sheikh Yahaya Ibrahim Masussuka
Source: Facebook

Abin da Masussuka ya faɗa

Daily Trust ta wallafa cewa sa’o’i kaɗan kafin kashe shi, Masussuka ya halarci wani taro a gidan surukinsa, inda ’yan uwa da sauran jama’a suka taru domin jimamin rasuwar wani.

A wajen taron, an ce malamin ya yi wa mahalarta nasiha kan cewa mutuwa wajibi ce ga kowane mutum, kuma ya kamata mutane su yi amfani da rayuwarsu wajen aikata alheri da yi wa bil’adama hidima.

Wani mazaunin yankin mai suna Murtala Narega, wanda ya san abubuwan da suka faru a sa’o’in ƙarshe na rayuwar malamin, ya ce ya tunatar da jama’a su nisanci bambancin launin fata, ƙabila da sauransu.

Narega ya ce malamin ya bayyana cewa Allah ne Ya halicci mutane da bambance-bambance, amma hakan bai kamata ya zama sanadin gaba ko ƙiyayya a tsakaninsu ba.

Ya ƙara da cewa malamin ya tunatar da mahalarta taron cewa duniya ba wurin zama na dindindin ba ce, kuma kowa zai koma ga Allah.

Kara karanta wannan

Masussuka: Shehu Sani ya faɗi 'dalilai' da ke jawo kisan malamai a Arewa

Maganganunsa sun ɗauki hankali

Narega ya ce kalaman malamin sun ƙara ɗaukar ma’ana mai zurfi bayan rasuwarsa, domin ba wanda ya yi tsammanin za su yi jimamin mutuwarsa sa’o’i kaɗan bayan ya yi musu nasiha kan mutuwa.

Ya bayyana cewa kalaman Masussuka sun ci gaba da kasancewa a zukatansu, musamman saboda yadda ya jaddada cewa rayuwa ta wucin gadi ce, kuma ya kamata mutane su yi amfani da lokacinsu wajen aikata alheri.

Bayan kammala taron, rahotanni sun ce malamin ya koma ɗakin da yake amfani da shi wajen gabatar da karatu a gidansa, inda ya saba gabatar da karatuttuka ga mabiyansa ta intanet.

Sai dai daga baya aka kai masa harin da ya yi sanadin mutuwarsa tare da abokinsa, Adamu Abubakar.

Masussuka da gwamnan Katsina
Gwamna Dikko Radda da Yahaya Masussuka. Hoto: Ibrahim Kaulaha Muhammad
Source: Facebook

Makusantansa sun yi bayani

Bello Danwaire, wani makusancin marigayin, ya ce shi ne ya taimaka wajen ƙarfafa wa Masussuka gwiwar ƙaura daga Bauchi zuwa Dutsin-Ma a shekarar 1988.

Danwaire ya bayyana malamin a matsayin mutum mai mutunci da girmama jama’a ba tare da la’akari da addininsu ba.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya yi magana kan kisan gilla da aka yi wa Sheikh Masussuka a Katsina

Maganar Tinubu kan Masussuka

A wani labarin, mun ruwaito cewa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya yi Allah-wadai da kisan Sheikh Yahaya Ibrahim Masussuka da abokinsa, Adamu Abubakar, a Dutsin-Ma ta jihar Katsina.

A cikin wata sanarwa da Bayo Onanuga ya fitar ranar Talata, Tinubu ya bayyana kisan a matsayin mummunan aiki da ya saɓa wa ƙa’idojin zaman lafiya da darajar rayuwar ɗan Adam.

Shugaban ƙasar ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan, mabiyansu da al’ummar Katsina, tare da umartar rundunar ’yan sanda da sauran hukumomin tsaro su yi bincike.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng