Ziyarar Hannatu Musawa Ofishin Uban ‘Ya ‘yanta, Abdussamad Ya Dawo da Batun Aure

Ziyarar Hannatu Musawa Ofishin Uban ‘Ya ‘yanta, Abdussamad Ya Dawo da Batun Aure

  • Haduwar Abdul Samad Rabiu CFR, CON da Hannatu Musawa ta sa jama’a sun samu abin tattaunawa
  • Ministar ta ziyarci tsohon mijinta a ofishinsa na Abuja, shi ma ya nuna ya ji dadin ganinta kwatsam
  • ‘Yan Facebook da Instagram suna ta rokon Allah SWT cewa ‘dan kasuwan ya maido da mai dakinsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Lagos - Abdussamad Rabiu ya yi zama da Hannatu Musa Musawa, amma a matsayinta na minista a Gwamnatin tarayya.

Sai dai wannan ziyara da aka kai babu tsammani ta jawo mutane suna ta tofa albarkacin bakinsu a dandalin sada zumunta na zamani.

Abdul Samad Rabiu da Hannatu Musawa
Hannatu Musawa a ofishin Abdul Samad Rabiu Hoto: Abdul Samad Rabiu CFR CON/Hannatu Musawa
Source: Facebook

Hannatu Musawa ta ziyarci Abdul Samad Rabiu

Abin da ya faru kuwa shi ne Abdussamad Rabiu ya yi amfani da kafar Facebook ya ce ya gana da ministar, ya kuma ji dadin ziyarar.

Kara karanta wannan

Bincike ya tono matsala a N37bn da aka ce gwamnatin Tinubu da Buhari sun raba wa talakawa

Hajiya Hannatu Musawa ita ce Ministar fasaha, kirkire-kirkire, al’adu da yawon bude ido a gwamnatin Bola Ahmed Tinubu tun 2023.

A makon nan ta je ofishin daya daga cikin manyan attajiran Afrika wanda kuma ya kasance mijinta a can baya.

Kamar yadda aka san su biyun, suna da kyakkayawar dangataka mai ban sha’awa duk da cewa babu aure a halin yanzu tsakaninsu.

Wannan karo ma Abdussamad Rabiu ya yi rubutu a shafin nasa, ya bayyana Hannatu da wanda a baya yake kiranta da matarsa.

‘Dan kasuwan ya kuma yi mata fatan alheri, Legit Hausa ta lura hakan ya burge masu bibiyarsa ainun.

Ya rubuta:

"Na samu ziyarar bazata mai kayatarwa a ofishina da ke Abuja yau, daga hannun wadda na taɓa kira da matata, Mai girma Ministar Hannatu Musawa.
"Lokuta suna canzawa, amma abokantaka da mutunta juna suna nan daram. Na ji daɗin ganinta da kuma ganin yadda take ci gaba da nuna himma da ƙwazo wajen bunƙasa al’adu da tattalin arzikin fasaha da kere-kere a Najeriya.

Kara karanta wannan

Masussuka: Shehu Sani ya faɗi 'dalilai' da ke jawo kisan malamai a Arewa

"Ina mata fatan ci gaba da samun nasarori!"

An yi fatan Abdussamad, Musawa su kara aure

Daga jin wannan sai aka ga irinsu Adnan Mukhtar Tudun wada suna bada shawarar cewa ya kamata aurensu ya dawo.

Malam Adnan ya yi sha’awar su yu aure tun dama dai wani abin ya taba shiga tsakaninsu, kuma ya ce sun dace da junansu.

Wasu kuma suka ce ai idan dai aka ga ana haka, wata rana za a ji sun koma gidan jiya.

Baba Bello Nafaty ya yi addu’a cewa Allah SWT ya sa dawowarta kenan.

“Fatan alheri”

- Bello Ahmad Adamu

Abubakar Bin Abdullahi ya rubuta:

"A dawo a gyara lalurarga, tunda dai har yanzu akwai soyayya."

Fatan da ake yi wa Hannatu Musawa a Instagram

A shafinsa na Instagram ma dai hotunan suna ta cigaba da jan hankalin matasa da yawa.

Wani Kakdams99 ya ce:

“Toh a maida ta dakinta mana.”

Mahmoud Shaba ya rubuta:

Kara karanta wannan

Gwamnan Katsina ya fadi matakin da za a dauka kan kashe Masussuka

“Wannan shi ne mafi kyawun mutuwar aure da na taba gani a rayuwa ta.”

Chefdeejerh_idisule:

"Baba a a mai da mama in da hali. Shi ne mafi alheri."

Wata ‘yar kasuwa mai saida kayan barci ta ce babu mamaki aminan juna ne tun kafin aure ya shiga tsakaninsu.

Havilahdivas101 ta ce:

"Haka ya kamata idan akwai ‘ya ‘ya a tsakani. Abin ya burge ni."

Kamar yadda ta saba fada, ita ma FMK Clothing ta rubuta: “Ya Allah!”

Ita ma da ta tashi a Facebook, Hannatu Musawa ta yabi tsohon mai gidan nata da irin gudumuwar da yake bada wa a nahiyar nan.

"Abdulsamad mutum ne wanda matsayinsa a tarihin Najeriya ya yi daidai da girman gudummawar da ya bayar ga bil’adama.
"Shi ginshiƙi ne mai ƙarfi ga Afirka kuma gwarzo a cikin al’ummarsa, kuma alheri ne ga duk waɗanda ya taɓa rayuwarsu.
"A nan ne wasu suka rika nuni da cewa da tsohuwar zuma ake magani."

- Hannatu Musawa

Bashir Shuaibu Abdullahi ya ce don Allah idan ba saki uku aka yi ba, a koma a cigaba da zaman auren.

Kara karanta wannan

Lauya ya ga hannun Tinubu wajen neman hana Pantami da Aminu Gwarzo shiga takara

Soyayyar da ke tsakanin Hannatu da Abdussamad

An ji labari Hannatu Musawa, ta bayyana cewa tsohon mijinta, Abdul Samad Rabiu (BUA), zai ci gaba da kasancewa a zuciyarta har abada.

Ministar harkokin fasaha ta jaddada cewa ba ta da wata nadama kan auren nasu, kuma dangantakarsu ta koma ta 'yan uwa duk da rabuwarsu.

Hannatu Musawa ta bayyana hakan ne yayin wata hira a shirin MIC on Podcast, inda ta yabi attajirin, tare da nuna girmamawa a tsakaninsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng