An Sanar da Shirye Shiryen Jana'izar Sheikh Yahaya Masussuka a Fadar Sarkin Katsina
- A ranar Juma’a 30 ga watan Oktoba 2026 za a yi wa marigayi Yahaya Ibrahim Masussuka sallar jana’iza
- Za a gudanar da sallar gawar ne a fadar Sarkin Katsina, daga nan kuma sai a birne shahararren malamin
- Na kusa da shi sun yi bayanin cewa taron da aka yi niyyar yi a ranar Asabar yana nan babu wani fashi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Katsina - An fitar da sanarwa ta musamman game da jana’izar marigayi Yahaya Ibrahim Masussuka da aka kashe a makon nan.
‘Yan ta’adda sun hallaka fitaccen malamin addinin tare da wani amininsa a gidansa da ke garin Dutsinma a jihar Katsina.

Source: Facebook
A shafin marigayin na Facebook aka fitar da bidiyo da ya tabbatar da mutuwarsa dauke kuma da bayanin birne shi.
Maja-bakin Yahaya Masussuka, Gwani Salihu ya fara da jawo ayoyin Kur’ani da suke maganar mutuwar Annabi Muhammad SAW.
Yaushe za a birne Yahaya Ibrahim Masussuka?
Bayan nan sai Abdulrashid Abdulkarim ya yi sallama da daukacin al’ummar duniya yana fara wa da yin sallalamin rashin.
"Muna sanar da ‘yanuwa ganin yadda al’amarin ya kasance na jana’iza da za mu gudanar da rashin wannan babban malami namu, Sheikh Yahaya Ibrahim Masussuka.
"Wannan jana’iza za ta gudana ne a ranar wannan Juma’a, 30 ga wata (Oktoba) a wannan gari namu na Katsina mai tarin albarka
"Za a gudanar da sallah ta wannan gawa bayan sallar Juma’a a fadar Mai martaba Sarkin Katsina."
- Imam Rashid
Za a yi taro bayan birne Yahaya Masussuka
Duk da malamin ya cika, Abdulrashid Abdulkarim ya tabbatar da cewa ba za a fasa shirya taron da aka yi niyya a karshen mako ba.
Ya nuna za su cika wa marigayin burinsa na wannan gagarumin taro na neman zaman lafiya a kasa, kokarin da yake yi da yake raye.
Imam Rashid ya ce bayan an birne malamin addinin a kabari, za a yi masa addu’o’i na musamman.
Daga nan kuma malamin ya ce za su cigaba da shirye-shiryen gudanar da taron da aka shirya za a yi a ranar Asabar dinnan.
Sanarwar ta yi wa masu shirin zuwa sallar jana’iza, ta’aziyya wannan taro daga ko ina a fadin duniya maraba zuwa Katsina.
Hikimar barin jana'iza sai bayan sallar Juma'a
A hirar shi da Freedom Radio, Naziru Salihu ya ce sun bar jana’izar sai Juma’a ne saboda shawarar da jami’an tsaro suka bada.
Hukuma tana bincike ganin cewa harbin malamin aka yi ya mutu, sannan kuma za a ba mutanen nesa damar zuwa jana’izar.
Naziru Salihu ‘da ne a wajen ma-ja-bakin marigayi Sheikh Masussuka wanda ya tabbatar da za a cire harsashi daga jikin gawar.
Shugaban kasa ya yi magana kan mutuwar Masussuka
An samu labari cewa Bola Tinubu ya yi Allah-wadai da kisan Sheikh Yahaya Masussuka da abokinsa, Adamu Abubakar, a Katsina.
A wata sanarwa da ya fitar, ya umarci jami’an tsaro su gudanar da cikakken bincike tare da cafke waɗanda suka yi wannan kisa.
Shugaban ƙasar ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan da al’ummar Katsina kan babban rashin malamin addinin da aka yi.
Asali: Legit.ng


