Ana Zargin Su Dan Bello da Tallata Tinubu a Boye, an Fitar da Bidiyo a kansu

Ana Zargin Su Dan Bello da Tallata Tinubu a Boye, an Fitar da Bidiyo a kansu

  • Tsohon ministan wasanni, Solomon Dalung, ya yi tsokaci kan zargin cewa Dan Bello da Sharafadeen Bature sun taka rawa wajen tallata Bola Tinubu
  • Dalung ya nuna damuwa kan yadda wasu masu sukar gwamnatin Shugaba Bola Tinubu a kafafen sada zumunta ke da alaka da mutanen da suke goyon bayan gwamnatin
  • Tsohon ministan ya bukaci Dan Bello da Sharafadeen Bature su yi wa mabiyansu karin bayani kan irin alakar siyasar da suke da ita da APC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Tsohon ministan wasanni, Solomon Dalung, ya yi tsokaci kan zargin da Abdul Turaki ya yi cewa Dan Bello da Sharafadeen Bature ne suka gabatar da shi ga Seyi Tinubu tare da shawo kansa ya koma jam’iyyar APC.

Kara karanta wannan

EFCC: Yahaya Bello ya fusata kan ce masa barawo, ya yi raddi mai zafi

Dalung ya bayyana ra’ayinsa ne a wani rubutu da ya wallafa, inda ya yi tambayoyi kan yadda wasu mutane ke bayyana kansu a matsayin masu fafutukar adawa da gwamnatin Tinubu, amma a lokaci guda suke da alaka da masu goyon bayan gwamnatin.

Dan Bello
Dan Bello da ake zargi da tallata APC a boye. Hoto: Dan Bello
Source: Facebook

A sakon da ya wallafa a Facebook, ya ce lamarin ya kamata ya sa ’yan Najeriya su yi nazari kan irin mutanen da suke amincewa da su a kafafen sada zumunta.

Dalung ya yi tambayoyi ga Dan Bello

A cewar Dalung, Abdul Turaki ya bayyana a cikin wani bidiyo cewa Dan Bello da Sharafadeen ne suka kai shi wajen Sheyi Tinubu tare da shawo kansa ya koma APC.

Dalung ya ce abin mamaki shi ne yadda mutanen da ake zargin sun taka wannan rawa suka shahara wajen sukar gwamnatin Tinubu da kuma nuna kansu a matsayin masu kare muradun talakawa.

Ya kuma ambaci cewa Turaki ya dage cewa har yanzu yana cikin masu fafutukar ganin an kawo karshen gwamnatin Tinubu, duk da ikirarin da ya yi kan alakar sa da wasu masu goyon bayan APC.

Dalung ya ce Turaki ya kuma yi wata magana kan mutanen da suka karbi wasu kyaututtuka, inda ya nuna cewa mai yiwuwa sun riga sun kashe abin da suka samu.

Kara karanta wannan

Yahaya Bello ya fadi matakin da ya kamata El Rufa'i ya dauka kafin tsare shi

Karin bayanin da Dalung ya yi

Tsohon ministan ya yi tambaya kan yadda mutum zai gina suna a matsayin mai tsananin sukar gwamnati, amma a lokaci guda ake zargin yana taimakawa wajen jawo mutane cikin jam’iyyar da ke mulki.

Ya kuma tambayi ko akwai yiwuwar wasu daga cikin masu bayyana kansu a matsayin masu fafutuka masu zaman kansu suna da wasu alakar siyasa da muradun kansu da mabiyansu ba su sani ba.

Dalung ya ce wasu masu fafutuka a kafafen sada zumunta sun samu karfin tasiri sosai wajen tsara ra’ayin jama’a, musamman a kan matsalolin tsadar rayuwa, rashin tsaro da rashin aikin yi.

Ya bayyana cewa mutane da dama suna sauraron masu fafutukar ne saboda sun yi imanin cewa suna magana ne bisa akida, ba don neman wata alaka ta siyasa ko wata moriya ta kashin kai ba.

An bukaci su dan Bello su yi bayani

Dalung ya ce idan bayanin Abdul Turaki gaskiya ne, ya kamata Dan Bello da Sharafadeen su yi wa mabiyansu bayani kan alakar siyasar da ake zargin suna da ita.

Kara karanta wannan

Dalung ya ja hankalin Rarara bayan lakada masa duka a Abuja

Ya jaddada cewa ba wai laifin su ne sun gana da Seyi Tinubu ba, sai dai abin da ya kamata jama’a su fahimta shi ne irin alakar siyasar da ke tsakanin masu fafutukar da masu fada a ji a gwamnati.

Solomon Dalung
Tsohon ministan wasanni, Solomon Dalung. Hoto: Solomon Dalung
Source: Getty Images

Ya kuma gargadi ’yan Najeriya da kada su mika tunaninsu da hukuncinsu na siyasa ga wasu fitattun mutane a kafafen sada zumunta kawai saboda sun kware wajen bayyana kansu a matsayin masu magana da yawun talakawa.

Ga bidiyon da Abdul Turaki ya yi bayani a kasa:

Maganar Dalung kan dukan Rarara

A wani labarin, mun rahoto cewa tsohon ministan wasanni, Solomon Dalung, ya yi Allah-wadai da rahoton dukan mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara, a wani masallaci da ke Abuja.

Dalung ya ce babu wanda ya cancanci a kai masa hari saboda ra’ayinsa na siyasa ko goyon bayan gwamnatin da yake so, yana mai cewa bai kamata a yi amfani da tashin hankali wajen warware sabanin ra’ayi ba.

Sai dai ya bukaci Rarara ya yi tunani kan halin da talakawan Najeriya ke ciki, musamman matsin tattalin arziki da suke dangantawa da manufofin gwamnatin da yake yabawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng