Mukabala tsakanin Sheikh Abduljabbar da malaman Kano: Babu hannunmu a hana zaman, gwamnatin Kano

Mukabala tsakanin Sheikh Abduljabbar da malaman Kano: Babu hannunmu a hana zaman, gwamnatin Kano

- Gwamnatin Kano ta yi na’am da hukuncin kotu na hana mukabala tsakanin malaman jihar da Sheikh Nasiru Kabara

- Kotu ta yanke wannan hukunci ne a ranar Juma’a, 5 ga watan Maris

- Sai dai lauyan Kabara ya ce su a nasu bangaren zama na nan don babu inda kotu ta fadi hana mukabalar kai tsaye

Gwamnatin Kano ta yi amanna da hukuncin kotun majistare ta jihar wacce ta hana yin mukabala tsakanin malaman jihar da Sheikh Nasiru Kabara.

A ranar Juma’a, 5 ga watan Maris ne kotun ta zartar da wannan hukunci, ana saura kwana biyu kafin gudanar da mukabalar da mutane ke ta zuba ido.

Hukuncin kotun ya nemi a tsaya kan hukuncin da kotu ta zartar tun a ranar 8 ga watan Fabrairu, wanda ya hada da haramtawa Sheikh Kabara yin wa’azi a jihar.

Mukabala tsakanin Sheikh Abduljabbar da malaman Kano: Babu hannunmu a hana zaman, gwamnatin Kano
Mukabala tsakanin Sheikh Abduljabbar da malaman Kano: Babu hannunmu a hana zaman, gwamnatin Kano Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: A karon farko, Fafaroma Francis ya ziyarci Iraki ya rokawa Iraki zaman lafiya

Kwamishinan labarai na jihar Kano, Muhammadu Garba, ya shaida wa sashin Hausa na BBC cewa bayan zantawa da gwamnati ta yi da bangaren shari’a, sun gamsu da wannan hukunci.

Ya ce saboda haka, an fasa yin mukabalar da aka shirya gudanarwa a ranar Lahadi, 7 ga watan Maris.

Da aka tambaye shi kan zargin da ake yi na cewa da hannun gwamnatin Kano a shigar da karar da aka yi domin hana zaman mukabalar, saboda sarkin Musulmi ya nuna rashin amincewarsa da hakan, ya ce wannan zargi kanzon kurege ne.

Ya kara da cewa ko da an daukaka kara daga baya wata kotun ta ce a gudanar da zaman, sai Gwamnatin Kano ta sake yin nazari kafin duba yiwuwar yin hakan.

A nashi bangaren, daya daga cikin lauyoyin Sheikh Kabara, Barista Tabiu Shu’aibu Abdullahi, ya ce su a iya saninsu wannan zama na nan, cewa babu wani waje da kotu ta fito karara ta hana yin mukabalar.

“Abun da muka fahimta a wannan hukunci shine kotu ta ce a ci gaba da aiki da hukuncin da aka zartar a ranar 8 ga Fabrairu. Cewa ta haramtawa Abduljabbar yin wa’azi da kuma yin kalaman tunzurawa, da rufe masallaci da ciniyarsa, amma babu wani waje da tace kada a yi mukabalar da aka shirya.”

Ya jaddada cewa ko kadan hukuncin da kotu ta zartar bai da nasaba da yin mukabalar, balle ma har a ce za a fasa ta.

Barista Rabiu ya kuma ce ko da dai wasu na son fakewa da haba Kabara yin wa’azi da kotu ta yi, “to a kwana da sanin cewa ba wa’azi za a yi da shi ba, ita Gwamnatin Kano cewa ta yi tattaunawa za a yi.”

A baya mun ji cewa, wata kotun Majistsare da ke zamanta Gidan Murtala a jihar Kano ta bada umurnin dakatar da mukabalar gwamnatin jihar ta shirya yi tsakanin Sheikh Abdul-Jabbar da malaman Kano a ranar Lahadi 7 ga watan Maris, BBC ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Jerin sunaye: BUK ta fara karatun digiri a sabbin kwasa-kwasai 8

Alkalin kotun, mai shari'a Muhammadu Jibrin ya yanke hukuncin dakatar da mukabalar sakamakon bukatar da wani lauya mai zaman kasan, Barrister Ma'aruf Yakasai ya shigar wa kotun.

Yakasai ya bukaci a dakatar da yin mukabalar ne saboda hakan ya saba umurnin da kotu ta bayar a baya na hana Sheikh Abdul-Jabbar yin karatu da saka karatunsa a kafofin watsa labarai na jihar Kano.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Online view pixel