Ana Son ba Shugaban Kasa, Gwamnoni Damar Yin Wa'adin Shekara 6
- Gwamnan Bayelsa, Sanata Douye Diri ya sake taso da maganar sauya tsari mulkin Najeriya domin gyara kan wa'adin shugaban kasa da gwamnoni
- Sanata Douye Diri ya bayyana cewa akwai bukatar su dawo yin wa'adi daya tilo mai tsawon shekara shida maimakon ba da damar tazarce
- Diri ya fadi haka ne yayin da ya karbi wata kungiyar magoya bayan shugaba Bola Tinubu, inda ya kawo dalilai kan bukatar neman sauya wa'adin
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Bayelsa - Gwamnan Jihar Bayelsa, Sanata Douye Diri, ya sake jaddada ra’ayinsa na cewa a mayar da wa’adin mulki guda daya mai shekaru shida ga shugaban kasa da gwamnoni na da muhimmanci.
Rahotanni sun bayyana cewa gwamnan Diri ya bayyana haka ne yana mai cewa shekaru hudu ba su isa a auna aikin shugaba yadda ya kamata ba.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa gwamna Douye Diri ya yi maganar ne yayin karbar magoya bayan Bola Tinubu karkashin kungiyar City Boy Movement (CBM)
Ganawar Diri da kungiyar Tinubu
Yana magana yayin karbar bakuncin kungiyar goyon bayan Tinubu mai suna City Boy Movement (CBM) karkashin jagorancin shugabanta, Oluwatosin Shoga, a wata ziyara ta girmamawa a ranar Talata, 14 ga Afrilun 2026.
Bayan tattaunawa da suka yi a Bayelsa, gwamna Diri ya bayyana goyon bayansa ga sake zaben Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027.
Maganar sauya wa'adin shugabanni
Gwamnan ya bayyana cewa tun yana Majalisar Dokoki ta Kasa ya yi kokarin ganin an amince da tsarin wa’adi guda daya na shekaru shida ga shugaban kasa da gwamnoni.
Yayin da ya ke kawo dalilai kan kiran da yake yi, gwamna Diri ya ce manufarsa ita ce kada gwamnati ta bata lokaci da dukiya wajen neman tazarce.
Ya ce:
“Idan shugaba yana da wa’adi guda daya na shekaru shida, zai mayar da hankali gaba daya kan shugabanci, ci gaba da bunkasa kasa ba tare da wata katsewa ba.”
Ya kara da cewa:
“Muna son dimokuradiyya inda mutane za su rika fadin ra’ayinsu ba tare da hakan ya zama cin mutunci ga manya ko gwamnati ba. Kasancewa a bangaren adawa na nufin kawo mafita, amma abin takaici a wasu lokuta ‘yan adawa na yada karya da sunan siyasa.”

Source: Facebook
A shekarar da ta wuce ma dai gwamna Diri ya yi kira a sauya kundin tsarin mulki domin dawo da wa'adin da za su yi zuwa daya tilo mai shekara shida kamar yadda News Central ta wallafa bidiyonsa a YouTube.
An nemi Tinubu ya sauya Shettma
A wani labarin, mun kawo muku cewa wata kungiyar siyasa a jihar Bauchi ta fito ta nuna goyon baya ga gwamna Bala Mohamed kan shirin shiga jam'iyyar APC.

Kara karanta wannan
Dalilin gwamnan Borno na goyon bayan harin sojin sama duk da rasa rayuka akalla 200
Kungiyar ta yi kira ga shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi takara da gwamna Bala Mohammed bayan sauke Sanata Kashim Shettima.
Shugaban kungiyar ya sanar da cewa za su hada matasa da masu zabe akalla miliyan 10 domin goyon bayan Bola Tinubu da Bala Mohammed.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

