Dalilin Kotun Kaduna na Sake 'Dage Shari'ar Neman Belin Nasir El Rufa'i
- A yau, 14 ga watan Afrilu, 2026 kotu ta ci gaba da zama a kan shari'ar tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i a jihar Kaduna
- A zaman da aka yi a yau Talata, kotun ta Kaduna ta sake dage yanke hukunci kan bukatar beli da Nasir El-Rufai ya gabatar a gabanta
- An dage zaman ne saboda alkalin kotu yana cikin jimami, sannan an sanar da ranar da za a ci gaba da shari'ar da ya ke da ICPC
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kaduna – Babbar kotun Kaduna ta sake dage yanke hukunci kan bukatar beli da tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai, ya gabatar a shari’ar da ICPC ta shigar a kansa.
Tun da farko an shirya yanke hukuncin ne a ranar 14 ga Afrilu, 2026, amma kotun ta sanar da dage zaman zuwa ranar Talata, 21 ga Afrilu, 2026.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa ana tuhumar El-Rufai da laifuffuka guda tara da aka gyara, wadanda suka shafi zargin damfara, amfani da mukami ba daidai ba, da kuma cin hanci da rashawa.
Nasir El-Rufa'i ya je zaman kotu
Daily post ta wallafa cewa rahotanni sun ce tsohon gwamnan ya isa kotu da misalin karfe 9.00 na dare, inda jami’an ICPC suka kawo shi cikin wata mota kirar Hilux mai launin fari.
Lauyan wanda ake kara, Ubong Akpan, ya bayyana wa manema labarai bayan zaman kotun, wanda bai wuce mintuna 30 ba, cewa an dage shari’ar ne saboda alkalin kotun, Dariyus Khobo, yana cikin jimami.

Source: Facebook
Ya ce:
“Mai shari’a yana cikin jimami, don haka bai samu damar kammala rubuta hukuncin ba. Mun fahimci cewa irin wannan abu kan faru. An dage zaman zuwa ranar Talata mai zuwa, 21 ga Afrilu, 2026, domin yanke hukunci kan bukatar beli.”
Martanin lauya kan shari'ar El-Rufa'i
Lauyan ya kuma yi karin bayani cikin yanayi na barkwanci da cewa ana iya ganin karin tuhume-tuhume daga wasu bangarori daban-daban, yana mai cewa ICPC na kokarin gabatar da karar a matakai daban-daban.
A cewarsa:
“Yanzu za mu tafi kotun tarayya, wanda shi ne mataki na biyu na wannan shari’a, domin ICPC ta yanke shawarar gurfanar da mu a matakai.”
Ya kara da cewa:
“Wata kila ma Hukumar Kula da Shuke-shuke za ta shigar da kara kan shigo da tsirrai daga Masar, tun da kowa na kokarin samun suna ta hanyar El-Rufai.”
A halin yanzu, tsohon gwamnan yana gaban Kotun Tarayya domin ci gaba da sauraron bukatarsa ta beli, yayin da ake jiran sabon ranar da kotun jihar za ta yanke hukunci.
Korafin El-Rufa'i kan shari'arsa
A baya, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya rubuta takarda ga Alkaliyar Najeriya inda ya bayyana rashin gamsuwa da yadda ake shari'arsa da hukumar ICPC a kasar nan.
Gwamnatin Najeriya na shari'a da Nasir El-Rufa'i bisa zarge-zargen almundahana, karkatar da kudin jama'a da halasta kudin haram a wata kotun Kaduna, inda har yanzu ake ci gaba da duba tuhume-tuhumen.
Tsohon gwamnan ya bayyana cewa yana da babban korafi a kan alkalin da ke sauraron shari'ar tare da rokon Kudirat Kekere-Ekun ta kawo masa agaji domin yana da yakinin ba za a yi masa adalci ba.
Asali: Legit.ng

