Ana Zargin Gwamna na Shirin Tsige Babban Sarki a Najeriya kafin 2027

Ana Zargin Gwamna na Shirin Tsige Babban Sarki a Najeriya kafin 2027

  • Tsohon gwamnan Ekiti, Ayodele Fayose ya sake fito da zargin cewa gwamna Seyi Makinde na shirin tsige Sarkin Ibadan daga kujerarsa
  • Hakan na zuwa ne bayan wani zargi da ya yi a baya game da lamarin amma aka fitar da wata sanarwa da ke karyata maganar da ya yi
  • Ikirarin Ayodele Fayose na zuwa ne a daidai lokacin da ake wata takaddama ta siyasa kan zargin tsige gwamna Seyi Makinde daga mulki

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Oyo - Tsohon gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose ya sake nanata zargin cewa gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, na shirin tsige Olubadan, Oba Rashidi Ladoja.

Rahotanni sun nuna cewa ya maimaita zargin ne duk da cewa gwamnatin jihar Oyo da masauratar Ibadan sun karyata abin da ya fada a baya.

Kara karanta wannan

"Ba mu yarda ba," Malaman Musulunci sun tunkari gwamna kan 'tsarin' da ya kawo a Najeriya

Sarkin Ibadan lokacin da aka nada shi
Lokacin da aka nada Sarkin Ibadan, Oba Rashidi Ladoja a 2025. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Zargin shirin tsige Sarkin Ibadan

A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, Fayose ya jaddada cewa akwai alamun an tsara yadda za a tsige Sarkin Ibadan.

Ya ce:

“Duk wanda har yanzu suke da shakku game da shirin Gwamna Seyi Makinde na tsige Sarkin Ibadan, Oba Rahidi Adewolu Ladoja, su jira kawai su ga yadda abubuwa za su wakana,”

Inji Fayose yana mai zargin cewa sababbin zarge-zargen da ake yi wa sarkin wani bangare ne shirya dabaru domin a samu hujjar daukar mataki a kansa.

Ya kara da cewa:

“Sun karyata cewa babu sabani tsakanin Olubadan da Makinde bayan na bayyana hakan. Amma yanzu suna zargin Olubadan da shirin tsige gwamnan,”

Zargin tsige gwamna Makinde

Sabon zargin ya zo ne a daidai lokacin da ake fuskantar sabuwar takaddama ta siyasa a jihar, inda dan majalisar dokokin Jihar Oyo, Gbenga Oyekola, ya nesanta kansa daga zargin cewa wasu ‘yan majalisa na shirin tsige gwamnan.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya fara shari'a da hadiman Abba Kabir 4, ya nemi a bi masa kadunsa

Punch ta wallafa cewa Oyekola da ke wakiltar mazabar Atiba ya bayyana a wata sanarwa cewa ba ya cikin irin wannan shiri, yana mai jaddada cewa ba zai shiga duk wani abu da zai iya kawo tashin hankali a jihar ba.

Sanarwar ta nuna cewa ya ce:

“Na nesanta kaina gaba daya daga duk wani tsari ko aiki da zai iya kawo cikas ga zaman lafiya a Jihar Oyo. Ba a gayyace ni ba, ba a tuntube ni ba, kuma ban shiga irin wadannan taruka ko shirye-shirye ba.”
Tsohon gwamna Ekiti, Ayo Fayose
Tsohon gwamnan jihar ekiti, Ayo Fayose a wajen taro. Hoto: @GovAyoFayose
Source: Facebook

Ya kuma sake jaddada biyayyarsa ga gwamnan, yana cewa:

“Ba zan iya ba, kuma ba zan yi rashin biyayya ga shugabana ba… Ina nan daram wajen goyon bayan zaman lafiya, hadin kai da ci gaban Jihar Oyo.”

Gwamnan Oyo ya gana da Kwankwaso

A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Seyi Makinde ya gana da jagoram Kwankwasiyya a Najeriya, Sanata Rabiu Kwankwaso a jihar Oyo.

Hakan na zuwa ne yayain da yanayin siyasar Najeriya ke kara daukar sabon salo, inda 'yan adawa ke kara haduwa domin tunkarar APC.

Seyi Makinde na cikin gwamnoni kadan da suka saura a jam'iyyar adawa ta PDP yayin da Kwankwaso ya sauya sheka daga NNPP zuwa ADC.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng