'Idan na Zama Shugaban Ƙasa," Obi Ya Faɗi Matakin da Zai Ɗauka kan Ƴan Bindiga
- Tsohon ɗan takarar shugaban kasa, Peter Obi, ya yi magana kan yin sulhu da ƴan ta'adda ba idan ya zama shugaban ƙasa
- Obi ya kafa hujja da nasarorin da ya samu a jihar Anambra, inda ya ce zai yi amfani da dabarunsa na da don dawo da tsaro a Najeriya
- Ya bayyana aniyar yin aiki kafada-da-kafada da manyan ƴan siyasar Arewa kamar Nasir El-Rufai da Rabiu Musa Kwankwaso
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Ɗan takarar shugaban kasa a zaɓen 2023, Peter Obi, ya bayyana babban matakin da zai ɗauka kan ƴan ta'adda idan ya zama shugaban ƙasa.
Peter Obi ya ce zai magance rashin tsaro shi ne ta hanyar ayyana yaƙi kai-tsaye kan ƴan ta’adda maimakon zama dasu domin tattaunawar sulhu.

Source: Twitter
Peter Obi ya magantu kan rashin tsaro
A yayin wata hira da ya yi da tashar Arise TV a ranar Litinin 13 ga Afrilu, 2026, Obi ya nuna ɓacin ransa game da kisan mummuke da aka yi wa Janar Oseni Braimah da wasu sojoji a harin Boko Haram/ISWAP.
"Babu wata ƙasa da za ta rasa manyan jami'an tsaro har guda 10 ba tare da mayar da martani ba. Zan ayyanar da yaƙi ne kawai, babu maganar sulhu,"
- In ji Obi
Peter Obi ya ce zai yi amfani da dabarun da ya yi aiki da su ya samu nasara a lokacin da yake matsayin gwamna don magance matsalolin ƙasa.
Ya tuna yadda ya tuntuɓi tsohon Shugaban kasa, Olusegun Obasanjo domin neman izinin ɗaukar matakan da suka kawo ƙarshen fashi da makami da garkuwa da mutane a Anambra na tsawon shekaru biyar.
Abin da ya jawo rashin tsaro a Najeriya
Obi ya kafa hujja da kalaman tsohon sufeton ƴan sanda, MD Abubakar, wanda ya tabbatar da cewa dabarunsa sun yi aiki yadda ya kamata, cewar Punch.
Sai dai kuma, Obi ya yi gargaɗin cewa ƙarfin soja kaɗai ba zai magance matsalar rashin tsaro a kasar ba kamar yadda wasu suke tunani game da lamarin, cewar Punch.

Kara karanta wannan
Alkawuran da Tinubu, Atiku da wasu da ke neman takarar shugaban kasa suka fara yi wa talakawa
Ya ce abin da Najeriya ke fuskanta yanzu shi ne sakamakon gazawar shugabanni na tsawon shekaru, rashin ilmantar da matasa, da kuma rugujewar amana tsakanin al’umma.
Obi ya lissafa ƙusoshin siyasar Arewa
A wani mataki na nuna shirye-shiryensa na gaba, Peter Obi ya bayyana sunayen wasu jiga-jigan siyasar Arewa da yake shirin yin aiki da su domin ceto ƙasar nan.
Ya ambaci Malam Nasir El-Rufai da tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, yana mai jaddada cewa babban burinsa shi ne ya kasance a yankin Arewa domin tunkarar ƙalubalen da ke akwai.
Wani Nura Haruna Maikarfe da Legit Hausa ta zanta da shi, ya ce 'yan siyasa da dama sun yi alkawuran kawo karshen 'yan ta'adda a lokacin yakin neman zabe, amma da suka ci zaben, ba su iya tabuka abin kirki ba.
"Ya kamata Peter Obi ya gane cewa, ba a yin yakin neman zabe da matsalar tsaro. Kowa ya ga yadda shugabannin kasa da suka gabata suka dauki alkawuran kawo karshen matsalar tsaro kafin su ci zabe, amma har suka sauka, abin jiya-i-yau.
"In zai yi yakin neman zabe ya yi a wasu muhimman abubuwan, amma daukar alkawari na kawo karshen matsalar ba abin wasa ba ne. Sai dai, tabbas, gwamnati tana da karfin kawo karshen 'yan ta'adda.
"Idan har Peter Obi da gaske ya ke yi, to dole ne ya kewaye kansa da wadanda su ma suna son kawo karshen matsalar, dole ne ya kawo hafsoshin tsaro masu son kawo karshen matsalar, domin rashin gaskiya ne ke hana ruwa gudu a harkar yaki da ta'addanci."
- Nura Haruna Mai Karfe.
Fasto ya yi hasashen zaben shugaban kasa
A wani labarin, an ji cewa wani malamin addinin Kirista a Najeriya, Solomon Emeka Eliyah ya yi hasashe game da zaben shugaban kasa na shekarar 2027.
Faston ya yi hasashen da ya ba mutane mamaki saboda ya nuna shugaba Bola Tinubu bai da nasara a zaben.
Malamin ya gargadi cewa duk wani yunkurin magudin zabe zai iya haifar da abubuwan da ba a taba gani ba a Najeriya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

