
Nade-naden gwamnati







Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta nada sababbin mukamai, inda aka zabo da yawa daga cikinsu matasan 'yan siyasa, daga ciki har da Auwal Lawan Aramposu.

Dakataccen gwamnan jihar Ribas, Sir Siminalayi Fubara ya tattara kayansa ya bar gidan gwamnati yayin da ake shirye-shiryen miƙa mulki ga sabon 'gwamnan riko'.

Gwamnan jihar Ebonyi, Francis Nwifuru ya kori hadimai biyu daga aiki bayan gani s] da aikata laifukan da suka shafi rashin ladabi, ya buƙaci su bar ofis nan take.

Gwamna Francis Nwifuru ya bayyana takaicinsa bisa rashin ganin kwamishinoni 3 a wurin taron Majalisar zartarwa, ta dakatar da su na tsawon wata guda.

El-Rufai ya ce Uba Sani ya kori shugaban KADIRS ne saboda ya bukaci shugaban majalisa, Yusuf Liman, da ya biya haraji kan Naira biliyan 10 da ya ajiye.

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya naɗa shahararren malamin cocin katolika na Sakkwato, Bishof Mathewa Kuka a matsayin shugaban majalir gudanar na Jami'ar Kachia.

Gwamna Abba Yusuf ya naɗa Ibrahim Adamu Kwamishinan Raya Gidaje na Kano, yana mai buƙatar ya tunkari matsalar gidaje, musamman ga ma’aikatan gwamnati.

Rahotanni sun karyata labarin da ke cewa masarautar Zazzau, karkashin Mai Martaba Ahmad Nuhu Bamalli ta kwace rawanin Magajin Rafin Zazzau, Ango Abdullahi.

Tsohon shugaban kasa Obasanjo ya koka kan yadda 'yan ta'adda da masu shaye-shaye ke zama sarakuna a Najeriya duba da irin miyagun ayyuka da suke aikatawa.
Nade-naden gwamnati
Samu kari