Duk da Bakin Talauci a Bauchi, Gwamna Ya Fadi Dalilin Raba Motoci 156 ga Sarakuna
- Gwamnan Bauchi, Bala Mohammaed ya raba motoci ga sarakunan gargajiya a lokacin da alkaluman NBS ke cewa akwai bakin talauci a jihar
- Rahoton hukumar kididdiga ta kasa ta NBS ya nuna cewa sama da 70% na jama’a na rayuwa cikin talauci ta fuskoki da dama, da suka hada da samun abin kashewa
- Yara da mata sun fi fuskantar matsaloli, musamman a bangaren ilimi da lafiya, wanda hakan ya sa kyautar motocin ta sake daukar hankulan jama'a
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Bauchi – A ranar Litinin, 13 ga watan Afrilu, 2026 ne gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya raba daruruwan motoci na aiki ga sarakunan gargajiya.
Wannan na zuwa ne a lokacin da alkaluma na hukuma suka nuna cewa sama da 70% na al’ummar jihar na rayuwa cikin talauci mai fuska da dama.

Source: Facebook
Premium Times ta wallafa cewa motocin da aka raba sun hada da sababbin motocin saloon na GMC 14, bas-bas na Toyota, motocin daukar kaya na Hilux, da kuma fiye da motoci 100 kirar Toyota Camry.
Gwamnan jihar Bauchi ya raba motoci
The Cable ta wallafa cewa gwamnan ya bayyana cewa rabon motocin wani bangare ne na kokarin gwamnatinsa na karfafa shugabanci a matakin kasa da kuma bunkasa hulda da al’umma.
Ya ce zai ci gaba da tallafawa masarautu da sababbin tsarin gargajiya domin tabbatar da cewa gwamnati ta kai ga kowa musamman na kasa.
Sai dai kuma, wannan mataki ya janyo suka, musamman idan aka kwatanta shi da halin talauci da yawancin al’ummar jihar ke ciki.

Source: Twitter
Rahoton hukumar kididdiga ta (NBS) ya nuna cewa kusan mutane miliyan 5.7 a Bauchi na fama da talauci mai tsanani.
Sannan kusan 69.2% na jama’a ba su da damar amfani da tsaftataccen makamashin girki, yayin da sama da rabin gidaje ba su da tsaftataccen ruwan sha.
An gano 'kamarin' talauci a Bauchi
Rahotanni sun nuna cewa yara ne suka fi shan wahala a wannan hali. Kimanin 74% na yara ‘yan kasa da shekaru 10 ba sa samun ilimi yadda ya kamata.
Haka kuma, 54% na yara masu zuwa makaranta ba zuwa aji, yayin da fiye da rabinsu gaba daya ba su cikin makaranta.
A bangaren lafiya kuwa, wani bincike ya nuna cewa a cikin watanni shida kacal tsakanin Yuli zuwa Disamba 2022, an samu mutuwar mata masu juna biyu da jarirai 872 a cibiyoyin lafiya 123 a jihar.
Haka kuma, haihuwa bakwai cikin 1a na faruwa ne a gida ba tare da kulawar kwararru ba, lamarin da ke kara hadarin mace-mace.
Gwamnatin Bauchi ta rufe kasuwanni
A baya, mun wallafa cewa Gwamnatin Bala Mohammed a Bauchi ta dauki matakin rufe wasu kasuwanni domin yaki da matsalar rashin tsaron da ake fama da ita a wasu daga cikin sassann jihar.

Kara karanta wannan
"Ba mu yarda ba," Malaman Musulunci sun tunkari gwamna kan 'tsarin' da ya kawo a Najeriya
Wannan na kunshe a cikin wata sanarwar da aka fitar, inda bayyana cewa an rufe kasuwannin shanu guda 25 a kananan hukumomi hudu saboda kamari da rashin tsaro ke kara yi a yankunan.
Gwamnatin Bauchin ta kuma umarci shugabannin hukumomin da abin ya shafa da su tabbatar da an sanya ido don ganin an aiwatar da umarnin domin a samu nasarar kare rayukan jama'a.
Asali: Legit.ng

