Ana Hasashen Zai Zama Mataimakin Abba, Gwamnatin Kano Ta Sake Shiga Kotu da Garo
- Gwamnatin jihar Kano ta sake shigar da ƙara a Kotun Ɗaukaka Ƙara game da tsohon kwamishina Murtala Sule Garo da wasu mutane
- Matakin shigar da ƙarar ya zo ne watanni tara bayan kotun ta yanke hukunci, a daidai lokacin da ake matsin lamba kan gwamna ya naɗa Garo mataimaki
- Takardun shari’a sun nuna gwamnati na ƙalubalantar hukuncin gaba ɗaya, inda ake zargin karkatar da biliyoyin kuɗaɗen kananan hukumomi
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Kano - Gwamnatin Kano ta sake shigar da ƙara kan tsohon kwamishina, Murtala Sule Garo, da wasu da ake zargi.
An shigar da karar a Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Kano bayan kotun jiha ta yi watsi da shari’ar da ta shafi tsohon kwamishinan.

Source: Facebook
Rahotanni daga Daily Nigerian sun nuna cewa an miƙa takardun ƙarar tun ranar 12 ga Maris, 2026, watanni tara bayan Babbar Kotun Kano ta soke shari’ar da aka shigar.
Dalilin maka Murtala Garo a kotu a Kano
Hakan ya biyo bayan takaddama tsakanin gwamnatin Kano da kuma tsohon kwamishina, Sule Garo a jihar.
A shekarar 2024, Gwamnatin jihar Kano ta kai tsohon kwamishinan kananan hukumomi, Sule Garo a gaban babbar kotun jihar.
An yi zargin kwamishinan Gandujen ne da yin rub da ciki tare da waddaka da N24bn na kananan hukumomi.
An shigar da kararsa ne tare da wasu kamfanoni biyu da kuma, Mustapha Sule Garo da Isah Musa Kera.
Sule Garo ya rike mukamin kwamishina har sau biyu a ma'aikatar kananan hukumomi karkashin mulkin Abdullahi Umar Ganduje.

Source: Facebook
Yadda ake matsa wa Abba kan nadin Garo
Wannan mataki ya zo ne a lokacin da ake matsin lamba ga gwamna Abba Kabir Yusuf domin ya naɗa Murtala Sule Garo a matsayin mataimakin gwamna, lamarin da ya janyo muhawara.
Takardun kotu sun nuna cewa gwamnatin jihar na ƙalubalantar hukuncin gaba ɗaya, inda ake zargin Garo da ‘yan uwansa da karkatar da kuɗaɗen kananan hukumomi, cewar Sahara Reporters.

Kara karanta wannan
Siyasa ta ɗau zafi: Kwankwaso ya sa DSS ta tsare wasu manyan hadiman gwamnan Kano
A cewar tuhume-tuhumen, ana zargin sun karkatar da biliyoyin naira daga asusun gwamnati, tare da amfani da wasu daga ciki wajen sayen kadarori ciki har da gidaje a ƙasashen waje.
Kotun ta baya ta duba batutuwa biyu da suka haɗa da sahihancin shigar da ƙarar ba tare da cikakken bincike ba, da kuma tasirin wasu hukuncin kotunan tarayya da suka gabata.
Yanzu dai gwamnatin Kano na neman a sake nazarin hukuncin domin tabbatar da adalci, yayin da shari’ar ke ɗaukar sabon salo a matakin Kotun Ɗaukaka Ƙara.
An roki Tinubu game da 'nadin' Sule Garo
A farko, mun ba ku labarin cewa wasu masu ruwa da tsaki a Kano sun bayyana damuwa game da shirin kakaba sabon mataimakin gwamna a jihar.
Kungiyar ta rubuta wa Bola Tinubu wasiƙa mai zafi, tana zargin akwai matsin lamba domin tilasta nada mataimakin gwamna.
Ta ce matakin na iya lalata martabar gwamnati da APC, tare da jawo matsalar siyasa yayin da ake shirin zaben 2027.
Asali: Legit.ng
