Bayyanar Sheikh Alkali Salihu Zaria a Shirin Gabon 'Talk Show' Ya Bar Baya da Ƙura

Bayyanar Sheikh Alkali Salihu Zaria a Shirin Gabon 'Talk Show' Ya Bar Baya da Ƙura

  • Amsa gayyatar Sheikh Alƙali Abubakar Salihu Zariya a shirin Hadiza Gabon ya haifar da muhawara a kafafen sada zumunta
  • Wasu sun soki halartarsa, suna cewa bai dace malami ya shiga irin wannan dandali ba saboda yana rage daraja da mutuncinsa
  • Sai dai wasu sun kare shi, suna cewa irin wannan dandali yana ba mutane dama su fahimci wasu ɓangarorin rayuwar shahararrun mutane

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Sheikh Alkali Abubakar Salihu Zaria ya sake jawo ka-ce-na-ce da suka a kafofin sadarwa bayan fitowa a wani shiri.

A cikin makon nan, an ga hotunan Sheikh Alƙali Abubakar Zariya ya halarci shirin Hadiza Aliyu Gabon mai suna Gabon 'Talkshow', wanda ya tayar da kura sosai.

An soki Alkali Salihu Zaria bayan bayyana a shirin Gabon
Bayyanar Sheikh Alkali Zaria a shirin Gabon ya jawo magana. Hoto: Sheikh Alƙali Abubakar Salihu Zaria.
Asali: Facebook

Gabon 'Talkshow': An soki Alkali Salihu Zaria

Wani masoyinsa, Ibrahim G. Lamara, ya nuna damuwa kan yadda malamin ke jawo musu magana a cikin rubutunsa a Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu daga cikin masoyan Sheikh Alƙali sun nuna rashin jin daɗi da wannan bayyanar tasa da kuma ce-ce-ku-ce da ta biyo baya.

Sun bayyana damuwa kan yadda wasu ke zaginsa, suna masu cewa hakan na sa malaminsu ya shiga abin da bai kamata ba.

Matashin ya rubuta kamar haka:

“Mu ‘yan Izala tsagin Jos… ba ma jin daɗin zagin da Malam Alƙali Zariya yake janyo mana."

Shirin Gabon 'Talkshow' dandali ne da jarumar ke gayyatar fitattun mutane daga masana’antar Kannywood da wasu mawaƙa da makamantansu domin tattaunawa da su kan rayuwa da aikinsu.

Bayyanar Sheikh Alƙali a cikin wannan zaure ya jawo ce-ce-ku-ce da suka daga wasu mutane a dandalin sada zumunta.

Wasu sun bayyana cewa ba daidai ba ne malami ya je irin wannan shiri, saboda ba wuri ne na koyarwa ko ilmantarwa ba.

A ra’ayinsu, hakan yana iya sa mutane su riƙa kallon malamai da wani salo daban da ba daidai ba, cewar rahoton Aminiya.

An taso Alkali Salihu Zaria a gaba
An caccaki Alkali Salihu Zaria bayan fitowa a shirin Hadiza Gabon. Hoto: Alkali Abubakar Salihu Zaria, Hadiza Aliyu.
Asali: Facebook

Wasu sun goyi bayan Alkali Salihu Zaria

Amma akwai wasu da ke ganin babu laifi cikin hakan, domin ana gayyatar mashahuran mutane ne domin bayyana sirrin rayuwarsu.

Wasu na ganin irin wannan shiri yana taimaka wa mutane su fi kusantar malamai da fahimtar su fiye da da.

Haka kuma, wasu sun tuna cewa ba Sheikh Alƙali ne na farko da ya shiga wannan zaure ba tun da Sheikh Ibrahim Khalil ma ya taɓa zuwa.

A ƙarshe, wannan lamari ya ƙara nuna yadda mutane da malamai ke fuskantar kalubale daga ra’ayoyin jama’a a kafafen sada zumunta.

Wanene Abubakar Salihu Zaria?

Sheikh Alƙali Abubakar Salihu Zaria malamin addinin Musulunci ne daga jihar Kaduna. Yana ɗaya daga cikin fitattun malamai a arewacin Najeriya, musamman a fannin ilimin addini da shari’a.

An san shi da faɗakarwa da kuma tsayawa tsayin daka wajen bayyana koyarwar Musulunci ga al’umma.

Sheikh Alƙali Zaria ya yi fice wajen bayyana ra’ayoyi masu ban dariya kan al’amuran addini da zamantakewa, kuma yana da mabiya da dama.

Shi dai Sheikh Alƙali Zaria ya fito ne daga gidan malamai - mahaifinsa shi ne Marigayi Alaranma Salihu Zariya kuma yanzu jagora ne a kungiyar Izala ta reshen Jos.

Wannan ya sa fitowarsa a kafafen watsa labarai ke jawo ce-ce-ku-ce a cikin al’umma tare da ganin hakan bai dace ba.

Wacece Hadiza Gabon?

Hadiza Gabon wata shahararriyar jarumar fim ce ta masana’antar Kannywood, wato fina-finan Hausa a arewacin Najeriya.

Ta yi suna ne wajen taka rawa a fina-finai da dama da suka shahara a Arewacin Najeriya.

Bayan harkar fim, Hadiza ta kafa shirin gabatar da tattaunawa mai suna “Gabon Talkshow,” inda take gayyatar fitattun mutane daga fannoni daban-daban don hira da su kan rayuwarsu da aikinsu.

Shirin nata ya samu karbuwa sosai saboda yadda take bayyana sirrin rayuwar mashahurai cikin sauki da nishadi. Hadiza Gabon ta zama daya daga cikin mashahuran ‘yan Kannywood masu tasiri.

Sheikh Alkali Salihu Zaria ya gargaɗi Dan Bello

Kun ji cewa Malam Alkali Abubakar Salihu Zaria ya gargadi Ɗan Bello kan zargin da ya yi wa Sheikh Bala Lau.

Malamin ya bayyana haka a cikin bidiyo cewa lokaci ya yi da za a dakatar da masu cin mutuncin malamai a Najeriya, darika ko Izalah.

Ya ce suna ci gaba da bincike kan Ɗan Bello, bayan kammalawa, za su dauki mataki kan cin mutuncin da aka yi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.