Akwai Gagarumar Matsala, Iran Ta Sanar da Asarar da Ta Tafka a Yakin Amurka da Isra'ila
- Kasar Iran ta tafka asarar biliyoyin Dalolin a yakin da ta yi da Amurka da Isra'ila, wanda ya shafe sama da ranaku 40
- A rahoton binciken farko da gwamnatin Iran ta fitar, ta ce kasar ta yi asarar Dala biliyan 270 daga farkon yakin zuwa ranar da aka tsagaita wuta
- Jamhuriyar ta Musulunci ta jaddada cewa za ta nemi diyya yayin da ake kokarin sulhun da zai kawo karshen yakin gaba daya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Iran - Gwamnatin Iran ta bayyana cewa asarar da ta yi a yakin da Amurka da Isra’ila suka kaddamar a kanta ta kai kimanin Dala biliyan 270.
Ta kuma jaddada cewa wannan kididdiga ta wucin gadi ce kuma ana sa ran za ta karu nan gaba idan rahoton kammalallen binciken barnar da aka yi mata ya fito.

Kara karanta wannan
Kasar Iran ta jero sunayen kasashe 5 da take bukatar su biya ta diyya kan yakin Amurka

Source: Getty Images
Wata mai magana da yawun gwamnati, Fatimah Mohajerani, ce ta bayyana hakan yayin wata hira da ita bayan tsagaita wuta tsakanin kasar da Amurka/Isra'ila, kamar yadda Tasnim News ta Iran ruwaito.
Iran ta tafka a asara a yakin Amurka
Ta ce daya daga cikin muhimman batutuwan da tawagar Iran ke mayar da hankali a kai a tattaunawar diflomasiyya, ciki har da wadda aka yi a Islamabad, shi ne batun diyya kan barnar da aka yi wa kasar.
“Muna bukatar a duba asarar da aka yi ta fannoni da dama. A halin yanzu, an kiyasta asarar Iran daga hare-haren Amurka da Isra’ila zuwa kusan Dala biliyan 270,” in ji ta
Fatimah Mohajerani ta kara da cewa ana ci gaba da tantance girman barnar da aka yi, wanda hakan ke nufin cewa ainihin adadin zai iya wuce wannan da aka bayyana a yanzu.
Kasar Iran ta dage sai an biya diyya

Kara karanta wannan
Muhimman abubuwa 5 da Amurka da Iran suka gaza warwarewa a zaman sulhu a Islamabad
Wannan mataki na Iran na neman diyya na zuwa ne a daidai lokacin da ake kokarin samun mafita ta hanyar tattaunawa tsakanin bangarorin da ke rikici, inda ake sa ran warware batutuwan da suka shafi shirin nukiliyar kasar.
Legit Hausa ta kawo muku rahoton da ke cewa biyan diyya da shirin nukiliya na cikin sharuddan da suka haddasa sabani tsakanin Iran da Amurka a tattaunawar Islamabad.
Masu sharhi na ganin cewa batun diyya zai iya zama daya daga cikin manyan kalubalen da za su iya jinkirta cimma yarjejeniya karshe, musamman idan bangarorin ba su cimma matsaya guda ba.
Shin Amurka ta amince da biyan diyya?
Har yanzu dai babu wata sanarwa daga Amurka ko Isra’ila kan wannan kididdiga asara da aka fitar ko kuma bukatar diyya da Iran ke gabatarwa
Rahoton Al-Jazeera ya nuna cewa rikicin ya haifar da babbar illa ga tattalin arzikin Iran da kuma kayayyakin more rayuwa, lamarin da ke kara jaddada bukatar samun sulhu mai dorewa a yankin Gabas ta Tsakiya.

Source: Getty Images
Amurka da Iran za su koma teburin sulhu
A wani rahoton, kun ji cewa akwai yiwuwar tawagogin tattaunawa daga Amurka da Iran su koma ƙasar Pakistan a ƙarshen wannan mako domin ci gaba tattaunawar sulhu.

Kara karanta wannan
Bayan gama zagayen farko, an bayyana bukata 1 da Amurka ta amince za ta yi wa Iran
Hakan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan tattaunawar farko ta ƙare ba tare da an cimma wata matsaya ba, lamarin da ya sake jefa shakku kan yiwuwar komawa fagen daga.
Wata majiya da ke da masaniya kan tattaunawar ta ce an riga an aika wa Washington da Tehran wata shawara na cewa tawagogin su koma Islamabad.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng