Kolmani: Gwamnatin Tinubu za Ta Cigaba da Hako Man Fetur a Arewa
- Sabon shugaban NNPCL, Bayo Ojulari, ya tabbatar da cewa za su koma aikin haƙar mai a Kolmani da ke iyakar Bauchi da Gombe
- Bayo Ojulari ya ce aikin zai haifar da ci gaba a yankin Arewa, inda zai jawo bude sababbin kamfanoni da farfaɗo da tsofaffi
- An fara aikin hako man fetur din ne a zamanin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, amma ya tsaya bayan ya sauka
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Sabon shugaban kamfanin mai na ƙasa wato NNPCL, Bayo Ojulari, ya bayyana cewa kamfanin na shirin komawa bakin aikin haƙar ɗanyen man fetur a yankin Kolmani.
Bayo Ojulari ya yi magana ne bayan kusan shekara biyu da tsayawar aikin da gwamnatin Muhammadu Buhari ta fara a yankin Kolmani da ke tsakanin Gombe da Bauchi.

Asali: Twitter
A yayin wata tattaunawa da gidan rediyon BBC Hausa, Ojulari ya ce aikin zai ci gaba, tare da kammala wasu muhimman ayyuka na bututun man gas daga Ajaokuta zuwa Kano.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayo Ojulari ya ce hakan zai taimaka wajen farfaɗo da masana’antu da samar da ci gaba a Arewacin ƙasar.
Wannan na zuwa ne a lokacin da ‘yan Najeriya ke fama da tsadar rayuwa, musamman sakamakon cire tallafin mai da shugaba Bola Tinubu ya yi a ranar rantsar da shi.
NNPCL: 'Za a cigaba da haƙo mai a Kolmani'
Bayo Ojulari ya tabbatar da cewa kamfanin NNPCL ya shirya tsaf don komawa kan aikin haƙo ɗanyen man da ya tsaya tun bayan ƙaddamar da shi.
A wancan lokaci, tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya jagoranci fara aikin a Kolmani, a shirin haƙo mai a Arewacin Najeriya.
A cewar shugaban NNPCL, hakan zai buɗe kofar bude sababbin masana’antu da farfaɗo da waɗanda aka rufe a baya.

Asali: Facebook
Ojulari ya jaddada cewa hakan zai haifar da ci gaba da bunƙasar tattalin arziki a Arewa, tare da taimaka wa jama’a wajen samun ayyukan yi da rage talauci.
NNPCL ya ce za a bunƙasa tattalin Arewa
Shugaban NNPCL ya ce aikin ba kamfanin kawai zai amfana ba, har da sauran al’umma baki ɗaya, musamman ma a Arewa.
Ojulari ya ce ‘yan Najeriya musamman ma 'yan Arewa sun nuna farin ciki lokacin da aka sanar da aikin, saboda sun fahimci irin rawar da haƙar mai zai taka wajen sauƙaƙa farashin sufuri.
A ƙarshe, Ojulari ya bayyana cewa shi ma ɗan Arewa ne, kuma ya ji daɗin irin martanin da wasu ‘yan yankin suka yi bayan naɗinsa.
Dangote ya yabi shugabannin NNPCL
A wani rahoton, kun ji cewa Alhaji Aliko Dangote ya wanke sababbin shugabannin kamfanin NNPCL daga zargin masa makarkashiya.
Aliko Dangote ya ce sababbin shugabannin suna goyon bayan ayyukan matatar man shi da ke jihar Legas.
Dangote ya bayyana cewa wasu 'yan kasuwar man fetur ne ke cin dunduniyar matatar shi domin ganin bai ci nasara ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng