Sojojin Najeriya Sun Bi 'Yan Ta'adda cikin Daji Sun Masu Barin Wuta

Sojojin Najeriya Sun Bi 'Yan Ta'adda cikin Daji Sun Masu Barin Wuta

  • Dakarun sojojin Najeriya sun kai wani gagarumin farmaki maboyar 'yan ta'adda da suka fitini al'umma a wasu yankunan jihar Bauchi
  • Rahotanni sun bayyana cewa an kai farmakin ne kakashin Operation Wutar Daji, inda sojoji suka kona wasu wuraren 'yan ta'addan
  • A baya-bayan nan 'yan bindiga sun kai hare-hare wasu yankunan karamar hukumar Alkaleri a jihar Bauchi, inda suka sanya jama'a gudun hijira

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Bauchi - Dakarun rundunar sojin Najeriya karkashin Operation Wutar Daji sun samu gagarumar nasara bayan gudanar da wani samame a dajin Kumbodoro da kauyen Kumbodoro a Jihar Bauchi.

Rahotanni sun nuna cewa farmaki ya jawo wa 'yan bindigan da ke fakewa a cikin dazukan koma baya kan shirin kai hare-hare da suke yi.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai kazamin hari wata fitacciyar jami'a a Arewa? Gaskiya ta bayyana

Maboyar 'yan bindiga da sojoji suka kona a Bauchi
Yadda sojoji suka bankawa maboyar 'yan bindiga wuta a Bauchi. Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Facebook

Legit Hausa ta tattaro bayanai kan nasarar da sojojin suka samu ne a wani sako da rundunar ta wallafa a shafinta na Facebook.

An ragargaza 'yan ta'adda a Bauchi

Rahoto ya nuna cewa dakarun sun yi nasarar wargaza maboyar ‘yan bindiga da dama, ciki har da sansanonin Azuge da suka yi kaurin suna a yankin dajin Kumbodoro.

Tare da goyon bayan rundunar sojin sama, dakarun Najeriya sun kashe wasu daga cikin ‘yan bindigar tare da rusa muhimman cibiyoyin ayyukansu, lamarin da ya rage karfinsu na barazana ga rayuka da dukiyoyin jama’a.

Haka kuma, dakarun Najeriya sun yi nasarar kubutar da mutane takwas da 'yan ta'addan suka yi garkuwa da su suna neman kudin fansa.

Abubuwan da sojoji suka kwato

Bayan bincike a maboyar 'yan ta'addan, sojojin Najeriya sun kwato makamai da kayayyaki da dama, ciki har da bindigogi masu yawa.

An gano bindigogi, harsashin bindigar FN guda daya, harsashin AK-47 guda daya, da kuma na’urorin sadarwa da sauran kayayyaki.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan bindiga sun kutsa cikin otal, sun sace shugaban karamar hukuma a Najeriya

Sauran kayayyakin da aka kwato sun hada da takalma guda biyu, hulunan kwano guda uku, na’urar StarTimes guda daya, wuka guda daya, wayoyin hannu guda shida da sauransu.

Wasu abubuwan da sojoji suka kwato a Bauchi
Wasu makamai da abubuwan da sojoji suka kwato a Bauchi. Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Facebook

Haka zalika, dakarun Najeriya sun yi nasarar gano katunan ATM na OPAY, hotuna, katin shaidar aiki, kayan sojoji da dama da kuma sarƙoƙin daure mutane a kafa.

Sojoji sun kwato shanu a Duguri

Haka kuma, dakarun da ke karamar hukumar Duguri sun kwato shanu guda 36 a kauyen Mushen Kura tare da hadin gwiwar ‘yan banga.

An yi zaton ‘yan bindigar sun tsere sun bar shanun saboda matsin lambar da sojoji ke musu. Ana ci gaba da kokarin gano masu shanun domin mayar masu da su.

Punch ta wallafa cewa rundunar Sojin Najeriya ta tabbatar da kudurinta na dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a dukkan wuraren da take aiki a kasar nan.

An kashe fararen hula a Borno

A wani labarin, kun ji cewa wani jirgin yaki mallakar rundunar sojin saman Najeriya ya saki bama-bamai a wata kasuwa a jihar Borno.

Wasu rahotanni sun nuna cewa harin ya yi sanadin mutuwar fararen hula da dama, lamarin da ya jawo hankalin al'ummar Najeriya.

Gwamnatin jihar Borno ta sanar da cewa ta rufe kasuwar shekara 5 da suka wuce saboda 'yan ta'adda na hada-hadar kasuwanci a wajen.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng