Duk da Ɓatan Dabo da Turji Ya Yi, Hadiminsa Ya Sauya Salon Hare Hare a Sokoto

Duk da Ɓatan Dabo da Turji Ya Yi, Hadiminsa Ya Sauya Salon Hare Hare a Sokoto

  • Ƴan bindiga sun sake kai hari a Rambahdawa, Tudun Wada, Dan Kware, Baushe, Nasarawa da Idi a karamar hukumar Isa a jihar Sokoto da ke Arewacin Najeriya
  • Duk da an biya ₦22m a matsayin kuɗin fansa makonni da suka wuce, sun fara kwace kaya, fyade mata da sace kayan gona marar misaltawa wanda ya kawo asara
  • Mazauna yankin da abin ya shafa sun dora alhakin hare-haren kan Kallamu Buzu wanda ake zargi da kasancewa cikin tawagar rikakken ɗan bindiga, Bello Turji

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Sokoto - Har yanzu dai al'umma da dama musamman yankunan karkara na ci gaba da fuskantar hare-haren daga yan bindiga.

Duk da neman riƙaƙƙen ɗan ta'adda, Bello Turji da sojoji ke yi, ana zargin babban hadiminsa ya kai wasu muggan hare-hare a ƙauyukan jihar Sokoto.

Yaran Bello Turji sun yi ta'asa a Sokoto
Ana zargin yaran Bello Turji da kai hari a Sokoto. Hoto: Legit.
Asali: Original

Rahoton Bakatsine mai sharhi kan lamuran tsaro shi ya tabbatar da haka a shafin X a yau Lahadi 11 ga watan Mayun 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rashin tsaro: Gwamnonin Arewa sun gana a Kaduna

Hakan ya biyo bayan taron gwamnonin Arewa 19 da kuma sarakunan gargajiya a jihar Kaduna domin kawo karshen ta'addanci da ya addabi yankin.

Gwamnonin sun nuna damuwa kan matsalolin yankin kama daga rashin tsaro, talauci da kuma yawan yaran da ba su zuwa makaranta.

Daga cikin bukatar da suka gabatar da suke neman a gaggauta aiwatarwa shi ne kafa yan sandan jihohi saboda magance matsalolin tsaro a yankin.

Sokoto: Ana zargin yaron Turji da kai hari

Wasu mazauna ƙauyuka da dama a jihar Sokoto sun fuskanci munanan hare-hare da aka zargin yaran Bello Turji ne.

Majiyar ta ce al'ummar yankunan sun daura alhakin kai harin kan yaron Bello Turji mai suna Kallamu Buzu.

Ƴan bindigar sun kai harin ne a Rambahdawa, Tudun Wada, Dan Kware, Baushe, Nasarawa da Idi, duka a ƙaramar hukumar Isa ta jihar Sokoto.

Yaran Turji sun kai hari Sokoto
Ana zargin yaran Turji da kai hari Sokoto. Hoto: HQ Nigerian Army.
Asali: Twitter

Yaran Turji sun sauya salon hare-hare

Rahotanni suka ce duk da an biya ₦22m a matsayin fansa makwanni da suka wuce, yanzu suna kwace gidaje, fyade ga mata da sace kayan gona da tufafi.

Mazauna yankin suna zargin hadimin Turji mai suna Kallamu Buzu wanda yana daga cikin wadanda suka addabi yankin.

Hakan ya biyo bayan tsanantar hare-haren da ake yawan kai wa a kwanan nan wanda ya jefa al'umma cikin matsala a ƙauyukan da ke fama da matsalolin tsaro.

Yaran Bello Turji sun yi ta'asa a Sokoto

Mun ba ku labarin cewa ƴan bindiga da ake zargin yaran Bello Turji ne sun kai farmaki garuruwan Satiru, Makwaruwa da Gidan Gyara a Isa dake jihar Sokoto.

Al’ummomin da aka kai harin sun shiga tsoro da rudani, yayin da mutane suka fara tserewa daga gidajensu domin neman mafaka saboda tsira daga miyagun.

Wannan farmakin na cikin jerin hare-haren da ake kaiwa a yankin, inda ake fama da matsanancin rashin tsaro da yawaitar sace-sace wanda ya ke cutar da al'umma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.