"Mutuwa Mai Yankar Ƙauna": Fitacciyar Jarumar Fim da ke Tashe a Najeriya Ta Rasu
- Jaruma a masana'antar Nollywood kuma ƴar gwagwarmayar kare haƙƙin mata masu ƙiba a Najeriya, Monalisa Stephen ta mutu
- Rahotanni sun nuna cewa jarumar wacce ta shahara a kafafen sada zumunta ta mutu ne tun jiya Talata, 12 ga watan Mayu bayan fama da jinya
- Duk da har yanzu babu sanarwa a hukumance daga iyalanta amma tuni abokan aikinta suka fara alhini da miƙa sakon ta'aziyya
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Lagos - Fitacciyar jaruma a masana'antar shirya fina-finan turanci ta Najeriya watau Nollywood kuma mai rajin kare masu ƙiba da ƙarfafa gwiwa, Monalisa Ayobami Stephen, ta rasu.
Jarumar wacce ta shahara a ɓangaraen harkar fim da harkokin soshiyal midiya ta mutu ne sakamakon rashin lafiya da suka shafi karancin sukari da zubar jini a ciki.

Asali: Twitter
Babban mai shirya fina-finai kuma shugaban ƙungiyar taurarin fim watau Best of Nollywood, Seun Oloketuyi, ya tabbatar da mutuwarta a wani rubutu da ya wallafa a shafin Instagram a ranar Laraba,
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bugu da ƙari, wasu daga cikin ƴan uwanta sun tabbatar da rasuwarta tun a ranar Talata, 13 ga Mayu, 2025, a jihar Legas amma labarin ya fara yaɗuwa a yau Laraba.
An tabbatar da mutuwar jarumar Nollywood
Seun Oloketuyi ya bayyana marigayiya jarumar a matsayin mace mai sadaukarwa kuma mai ƙwazo da kyaun aiki.
"Monalisa Ayobami Stephen ta rasu. Ta mutu jiya a Legas bayan fama da karancin sukari da zubar jini a cikin jiki.
"Yar uwarta ta kusa ce ta tabbatar da wannan mummunan labari.”
- In ji Seun Oloketuyi.
Jarumar ta shahara a soshiyal midiya
Monalisa, mai shekara 33 a duniya, ta shahara wajen kare hakkokin mata masu jiki watau mata masu ƙiba da kuma wayar da kai kan lafiyar kwakwalwa.
Jarumar ta yi kaurin suna sosai a kafafen sada zumunta inda ta rika wayar da kan jama’a kan muhimmancin kaunar kai da motsa jiki, musamman ga mata masu ƙiba kamarta.
Ta yi fice wajen fitowa fili ta bayyana ra’ayoyinta da ke cikin zuciyarta ba tare da jin wata kunya ba, lamarin da ke yawan haddasa muhawara da ce-ce-ku-ce a lokuta da dama.
Yadda ta haddasa surutu kan soyayya
A watan Afrilu 2023, ta janyo ce-ce-ku-ce bayan ta bayyana cewa tsohon saurayinta ya na jima'in baki da ita idan tana yin al'adar mata.
Wannan kalamai nata sun tayar da ƙura a kafafen sada zumunta amma hakan bai sa ta ja da baya daga fafutukar da take ba, inda ta ci gaba da karfafa wa mata gwiwa su zauna da gaskiyarsu.
Duk da cewa iyalinta ba su fitar da sanarwar mutuwarta a hukumance ba, amma tuni abokan aikinta suka fara jimami da miƙa sakon ta'aziyya.
Rashin jarumai a masana'antar fim
A ‘yan shekarun nan, masana’antar fina-finai ta yi ta fuskantar rashin jarumai da yawa, wanda hakan ya jawo damuwa a tsakanin masoya da ‘yan wasa.
Daga cikin jaruman da suka rasu kwanan nan akwai Sadiq Daba, fitaccen jarumin da ya shahara da rawar da ya taka a fina-finai da talabijin.
Haka kuma, Maryam Babangida, wata jaruma mai tasiri a masana’antar, ta rasu cikin yanayi na rashin lafiya. Wasu ‘yan wasan sun rasa rayukansu ne sakamakon cututtuka, yayin da wasu suka yi rasuwa ta hanyar haɗari ko rashin kulawa da lafiyarsu.
Wannan jerin mutuwa ya sa masu ruwa da tsaki a Nollywood da ma Kannywood suna kira ga gwamnatin Najeriya da ta dauki matakai na musamman wajen inganta kiwon lafiya da walwalar ‘yan wasa.
Haka kuma, an nemi ƙungiyoyin da ke kula da harkar fina-finai su samar da tsarin tallafi da kulawa ga ‘yan wasan domin kaucewa irin wannan asara a nan gaba.
Masana’antar na bukatar tsare-tsare masu dorewa don tabbatar da lafiyar ‘yan wasa da kare su daga matsalolin da ka iya jawo matsanancin rashi ga masana’antar.
Wannan yanayi na nuna muhimmancin kulawa da lafiyar jarumai domin ci gaban Nollywood.
Jaruma Nkechi Nweje ta bar duniya
A wani labarin, kun ji cewa jarumar fim da ke aiki a masana'antar Nollywood, Nkechi Nweje ta riga mu gidan gaskiya.
Wannan labari ya girgiza masana’antar shirya fina-finai ta Kudancin Najeriya, tuni abokan aikinta da masoya suka nuna alhininsu.
An tattaro cewa marigayiya jarumar ta rasu ne bayan fama da jinya ta ɗan lokaci sakamakon tiyatar da aka yi mata a watan Nuwamba, 2024.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng