Trump Ya Yi Magana Mai Jan Hankali, da Alamu Amurka da Iran Za Su Koma Islamabad
- Donald Trump ya bayyana alamun da ke nuna cewa nan da kwanki biyu, tawagar Amurka da ta Iran za su sake haduwa a birnin Islamabad
- Shugaban na Amurka ya ce za a koma teburin tattaunawa a zagaye na biyu da nufin cimma yarjejeniyar da za ta tabbatar da zaman lafiya
- Rahotanni sun nuna cewa Trump ya yaba da kokarin shugaban rundunar sojin Pakistan, Asim Munir, inda ya ce yana yin aiki mai kyau
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Washington D.C - Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya nuna alamun yiwuwar kasar ta koma teburin tattaunawa da Jamhuriyar Musulunci ta Iran a karo na biyu.
Shugaban Donald Trump, ya bayyana cewa za a iya gudanar da zagaye na biyu na tattaunawa da Iran a birnin Islamabad na Pakistan cikin kwanaki biyu masu zuwa.

Source: Getty Images
Amurka za ta sake zama da Iran
A wata hira ta waya da New York Post, Trump ya ce akwai yiwuwar samun sabon ci gaba cikin gaggawa, yana mai cewa ya fi dacewa a ci gaba da tattaunawar a Pakistan.
“Ya kamata ku ci gaba da zama a can, domin akwai yiwuwar wani abu ya faru cikin kwanaki biyu masu zuwa, kuma mun fi karkata zuwa komawa can,” in ji shi
Wannan na zuwa ne bayan zagaye na farko na tattaunawar da aka gudanar a karshen mako bai kai ga cimma wata yarjejeniya ba.
A baya, Trump ya nuna cewa ana iya gudanar da zagaye na gaba na tattaunawar kai tsaye a wata kasa ta Turai, amma daga bisani ya sauya matsaya.
Shugaban na Amurka ya tabbatar da cewa akwai yiwuwar komawa birnin Islamabad domin ci gaba da tattaunawar, maimakon tafiya wani wuri daban, in ji tashar Al-Jazeera.
Trump ya jinjina wa hafsan sojin Pakistan
Rahotanni sun nuna cewa Trump ya yaba da kokarin shugaban rundunar sojin Pakistan, Asim Munir, inda ya ce yana yin aiki mai kyau wajen taimakawa wajen shirya zaman tattaunawar.
Masu sharhi na ganin cewa ci gaba da tattaunawar a Pakistan na iya nuna irin rawar da kasar ke takawa a matsayin mai shiga tsakani son sulhunta bangarorin da ke rikici.

Source: Getty Images
Sai dai har yanzu ba a tabbatar da ko wannan sabon zagaye na tattaunawa zai kai ga warware sabanin da ke tsakanin Amurka da Iran ba, musamman kan batutuwan da suka shafi shirin nukiliyar Iran da kuma iko a mashigar ruwa ta Hormuz.
Ana sa ran cewa kwanaki masu zuwa za su zama masu muhimmanci wajen tantance ko bangarorin za su iya matsawa gaba zuwa ga cimma yarjejeniya mai dorewa ko kuma rza su ci gaba da yaki.
Amurka ta koka kan rufe maahigar Hormuz
A wani rahoton, kun ji cewa Mataimakin shugaban Amurka, JD Vance ya tuna matakin da Iran ta dauka wanda ya girgiza kasar da sauran kasashen duniya.

Kara karanta wannan
Wata sabuwa: Matsalar da aka samu a sulhun Amurka da Iran ya rusa burin 'yan Najeriya
Vance ya zargi Iran da aikata abin da ya kira “ta’addancin tattalin arziki” bayan katse zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar Hormuz.
Shugaban ya kuma bayyana cewa an samu “kyakkyawar tattaunawa” tsakanin Amurka da Iran a Pakistan a karshen mako, duk da cewa ba a cimma wata yarjejeniya ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

