Buba Galadima: "Ko Gawa aka Tsayar, Za Ta Buga Tinubu da Kasa a Zaɓen 2027"

Buba Galadima: "Ko Gawa aka Tsayar, Za Ta Buga Tinubu da Kasa a Zaɓen 2027"

  • Fitaccen dan siyasa, kuma daya daga cikin wadanda suka kafa APC, Inijiniya Buba Galadima ya hango karshen mulkin Bola Tinubu a 2027
  • A wani jawabi da ya yi a wajen taron jam'iyyarsa ta ADC a Abuja, Buba Galadima ya bayyana cewa doke Bola Tinubu a zabe mai zuwa ba zai yi wahala ba
  • Ya zargi gwamnati da yunƙurin hana taron jam’iyyar ADC, tare da bayar da tabbacin cewa 'yan adawa za su ci gaba da tsayawa tsayin daka wajen tunkarar APC

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Fitaccen ɗan siyasa a bangaren adawa, Buba Galadima, ya bayyana cewa ko da gawa aka tsayar takara a kan Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, za ta iya yin nasara a zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Jigon ADC ya 'gano' halin da APC ke ciki, ya fadi hadin da zai kai Tinubu ƙasa a 2027

Injiniya Buba Galadima ya yi wannan furuci ne yayin da yake magana a wani taron jam’iyyar ADC, inda ya nuna rashin gamsuwa da yadda yake ganin tafiyar siyasar ƙasar ke gudana.

Buba Galadima ya ce Tinubu zai sha kasa a 2027
Shugaban kasa Bola Tinubu da Buba Galadima Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu/Buba Galadima
Source: Facebook

Arise News ta wallafa cewa jigon na APC ya ce shugaba mai ci a yanzu ba zai yi wahalar kifar wa ba a filin zabe saboda 'yan Najeriya sun gaji.

Buba Galadima ya magantu kan zaben 2027

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa Injiniya Buba Galadima yana da yakinin cewa ko gawa aka tsayar ta kara da Tinubu, APC ce za ta sha kasa a babban zaben.

A cewarsa:

“Ko da babu wani mutum mai rai a Najeriya, muka ɗauko gawa a cikin akwatin gawa muka tsayar da ita takara da Shugaba Tinubu, ina tabbatar maku wannan gawar ce za ta yi nasara a 2027.”

Tsohon abokin tafiyar Muhammadu Buhari ya yabawa jam’iyyar ADC kan gudanar da taronta duk da barazanar da ya ce sun fuskanta daga wasu masu iko.

Buba Galadima ya ce an matsa masu

Buba Galadima ya bayyana cewa an yi yunƙurin hana gudanar da taron ta hanyar matsa wa mai wurin da aka shirya gudanar da shi, amma haka bai cimma ruwa ba.

Kara karanta wannan

Naja'atu: Yadda ƴan Najeriya za su yi amfani da ADC a kifar da APC a 2027

A cewarsa:

“Mun samu saƙo cewa an soke wannan wajen da muka tanada domin taron, saboda an yi wa mai wurin barazana cewa idan ya bari mu yi amfani da wurin, za a ƙwace takardar mallakarsa.”

Buba Galadima ya ce wannan barazana ta kusan kawo cikas ga taron, amma duk da haka masu shirya taron suka yanke shawarar ci gaba da gudanar da shi.

Buba Galadima ya ce APC ta shirya tunkarar APC a 2027
Injiniya Buba Galadima wani taro da ka yi a Kano a shekarun baya Hoto: Kwankwasiyya reporters
Source: Facebook

Ya kara da cewa wannan mataki wata hanya ce ta nuna cewa ba za su bari tsoro ko matsin lamba su dakile su ba.

Buba Galadima ya ce duk da irin ƙalubalen da suka fuskanta, sun kuduri aniyar ci gaba da fafutukar siyasa ba tare da tsoro ba.

Ya ce an tambaye shi ra’ayinsa kan halin da ake ciki, sai ya amsa da cewa ko da Abuja za ta ƙone gaba ɗaya, za su gudanar da taron a wurin.

'Yar ADC ta zaburar da 'yan Najeriya

Kara karanta wannan

"Tinubu na yi wa dimokuradiyya shakar mutuwa": Obi ya ce da matsala gabanin 2027

A baya, mun ruwaito cewa fitacciyar ƴar siyasa a Najeriya, Hajiya Najaatu Muhammad ta ce ADC ce injin ceto Najeriya daga bakin da ta ke ciki a babban zaben 2027 da ke kara tunkarowa.

A yayin da ta ke jawabi a wajen babban taron jam'iyya da ya gudana a Abuja a ranar Talata 14 ga watan Afrilu, 2026, ta ce zaɓe mai zuwa ba wai tsakanin ADC da APC ba ne kawai.

Ta bukaci ‘yan Najeriya su hada kai domin kawo karshen mulkin rashin adalci da ta ce ana yi masu a ƙarƙashin mulkin Bola Tinubu da APC, ta hanyar zaben ADC idan lokaci ya yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng